Daga Abubakar Abba
A bisa binciken da aka gudanar ya nuna cewar, babbar matsalar dake addabar maza itace ta rashin ƙarfin mazaƙuta.Wata alamace dake hana mazaƙutar namiji tashi har ya kaiga ya iya yin jima’i.
Fiye ɗan rage ƙarfin ɗa namiji ta wajen yin jima’i, hakan yana kuma janyo namiji ya kasa yiwa mace ciki, sai dai, labari mai kyau shi ne, ana iya warkewa daga wannan matsalar.
Sai dai kuma yana da muhimmanci a zayyana wasu ɗabi’u waɗanda sune suke haddasa hakan kamar haka;
Abinci mai gina jiki: Tunda farko ya kamata a san cewar karfin mazaƙutar ɗa namiji ta danganta ne akan yadda jini ke gudana ta hanayar mazaƙutarsa, kuma hakan yana taimakawa ne sakamakon cin abinci mai gina jiki da mutane keyi.
Manajin Darakta na kafar yanar Gizo, ya bada bayanai akan yadda za a kare lafiya, inda ya ce, cin abinci mai gina jiki da kuma wasu hanyoyi na cin abinci mnasu gina jiki da zasu iya haifar da ciwon zuciya saboda ƙarancin tafiyar jini, zai iya kuma janyo rashin tafiyar jini a cikin mazaƙuta, musamman kuma zai iya hana jini ya wuce a cikin mazaƙutar ɗa namiji da zai sanya mazaƙutar ta tashi.
A saboda haka, don kaucewa rashin ƙarfin mazaƙuta, ana baiwa maza shawara dasu dinga shan kayan marmari da kayan Lambu da Kifi da sauransu.
Wani ƙwararre mai suna Andrew McCullough, ya bayyana cewar, “ uk wani abu da baida kyau a cikin zuciyar namji, haka ma baida kyau a mazaƙutarsa. “
Ƙiba: Kiba tana ɗaya daga cikin abinda ke haifar rashin ƙarfin mzakuntar ɗa namiji yake. Acewar kafar yanar Gizo ta WebMD ta ce, kiba mai yawa tana haifar da ciwon Suga, wadda zai iya haifar da gameji a wasu sassa na jikin namji.
Idan ɗaya daga cikin jijiyoyon da ke haɗe da mazaƙuta ta samu dameji, zai iya shafar ƙarfin mazaƙutar namiji har ta kaiga bata iya tashi kamar yadda ya kamata. Bugu da ƙari, ciwon Suga yana ɗaya daga cikin abinda ke janyo hana jini yawo a a cikin mazaƙuta.
Rashin motsa jiki: Bincike ya nuna cewar wasa jini yana taimakawa jikin mutum, kuma yana ƙara taimakwa wajen zagayawar jini a jiki. Bugu da ƙari, wasa jini yana ƙara ƙarfin mazaƙutar namiji saboda yadda jini ke wucewa a mazaƙuta.
A waje ɗaya kuma, kasa wani kuzari ko wata jin daɗi ta rayuwa na haifar da rashin ƙarfin mazaƙuta. A saboda haka, ana baiwa
Haka, ana shawartar mutane dasu dinga kiyayewa da irin wasa jinin da zasu dinga yi domin kuwa duk wani wasa jini kamar irin na hajijiya da zai sanyawa mutum wani nauyi tsakanin tuburarsa da matsematsinsa zai iya shafar jijiyoyin jininsa da suke haɗe da mazaƙutarsa hakan kuma ya janyo mazaƙutar tasa, taƙi yin ƙarfi.
Zuƙar Taba Sigari: a bisa wasu bincike da aka gudanar a baya, sun nuna cewar, akwai rashin muhimmanci tattare da zuƙar taba cigari dominkuwa tana shafar huhun mutum hakan kuma zai iya rage ƙarfin mazaƙutar namiji.
Kafar yanar Gizo ta WebMD ta bayyana cewar, zuƙar taba cigari, zai iya yiwa jijiyoyin jini lahani da kuma rage hana jini tafiya zuwa ga mazaƙuta.
Bugu da ƙari, an gano cewar, sanadarin dake cikin cigari zai iya sanya jijiyoyin jini su takura,inda daga ƙarshe, jini ya kasa wucewa zuwa cikin mazaƙuta.
An ruwaito wani ƙaramin farfesa a sashen magani na jima’I dake jami’ar Charles Walker, yana cewa zuƙar taba cigari, tana shafar jijiyoyin jini, inda hakan zai iya janyo ƙarfin jijiyar mazaƙuta da kuma
tafiyar jini zuwa ga mazaƙuta. Kowa ya san cewar, ɗabi’ar zuƙar taba sigari bata da kyau ga lafiyar jikin ɗan adam, amma mafi yawancin mutane basu san dangantaka kai tsaye da zuƙar sigari keda ita da hana aikin mazaƙuta ba.
Jin ciwo a jikin mazaƙuta: Mafi yawancin mutane suka mamaki cewar ya za a yi ace wani ciwo ya shafi mazaƙutar namiji, musamman ganin inda Allah ya ajiye ta, Amma akwai abubuwa da ke haifar da hakan kamar mugun wasa da yin jima’I barkarai ko kuma sanadiyyar haɗari.
Gajiya: wannan itama aba ce data zamo ruwan dare, kuma mafi yawancin mutane sun san abinda ke haddasata ta da kuma illolinta. Wannan ilar, an gano cewar, tana janyo jijiyoyin jini, inda kuma hakan kan janyo rashin tashin mazaƙuta. Amma rage damuwa da yanayi na ƙunci yana taimakwa wajen Yawon jini zuwa mazaƙuta.
Shaye-Shaye: Shan kayan maye abunne da ya zama ruwan dare ga wasu mutanen, amma ba kowa ya san hakan ba, domin kuwa yana iya shafar ƙarfin yin jima’i ko kuma ya kashe masu sha’awa kwata-kwata. A saboda haka, ana shawartar mutane masu shan magungunan ƙara ƙarfin jima’i, dasu tuntuɓi likita ko masu saida magungunan asibiti kafin su sha wani magani.