Kungiyar ‘yan Majalisar dokokin kasa t Jam’iyyar APC ta amince da shugaba Bola Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2027 mai zuwa.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis.
Ayayin da yake jawabi a wajen taron kolin jam’iyyar APC na kasa da aka gudanar a fadar shugaban kasa a Abuja. Akpabio ya bayyana irin hikimar siyasa da jajircewar shugaba Tinubu a matsayin dalilan da yasa suka amince shugaban ya ci gaba da mulki don amfanar al’umma.
Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas ya amince da wannan batun na takwaransa cikin gaggawa.
“Na tsaya a madadin Sanatoci 109 da ‘yan Majalisar Wakilai 360 don amincewa da wannan matakin na Akpabio,” in ji Abbas.