Ƴan Matanci A Zamanin Nan
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƴan Matanci A Zamanin Nan

byRabi'at Sidi Bala
1 year ago
Zamani

Rayuwar ‘yan matanci da mata ke yi abu ne da ya dace a lura da shi tamkar yadda ake lura da sauran al’amuran da suka shafi rayuwa. Don a irin wadannan lokutan mata da yawa suke lalacewa, wasu kuma su koyi munanan dabi’u ko ta sanadin samarinsu ko ta sanadin kawayensu, abin da ke haifar da haka shi ne gurbacewar al’adunmu da kuma samun shigowar sababbin bakin al’adu. Sannan sababbin nau’o’in na’urorin fasaha, wanda suka hada da wayar salula da kuma intanet kamar shafukan ‘Facebook’ ‘Whatapp’ TikTok da dai sauransu.

Sai ka ga yarinya mace wacce ba ta wuce shekaru 13 ba ta mallaki wayar kanta, wani bi ma iyayenne suke siya mata su bata don gata, ba tare da sun lura ko sun sa ido a kan su waye da waye za su bugo mata ba, ko kuma za ta bugawa ba. Ko da kuwa mace ta mallaki wasu shekaru ni ban ga ribar hirar waya ga wandanda ba ma’aurata ba ko muharramai ba, saboda hakika irin wannan hirarrakin na samari da ‘yan mata a yawancin lokuta ba sa haifar da alheri. Musamman in aka yi la’akari da lokutan da ake yin hirar lokacin kwanciyar bacci ne, su kan yi amfani da kalmomi ne na sha’awa zalla don kwantarwa juna zuciya, da wuya ka ji suna tattaunawa kan batun aure da azamaninsu.

  • Shekara 10 Da Sace ‘Yan Matan Chibok: Gidauniya Ta Bayyana Abubuwan Alhini
  • ‘Yan Mata Mu Yi Karatu Sannan Mu Kama Sana’a – Khadija Sambo

Yarinya karama sai ka ga ta san komi, kuma in har zuciyarta ta yi zurfi a kan sha’awar abokin hirarta ko wani daban sai a ga ba wuya ta lalace, kafin iyaye su farga labarin ya munanta.

Ni dai a nazarin da na yi na fahimci in har ba a lura an yi gyara ga rayuwar ‘yan matanci ba, to wallahi kar mu taba saka ran al’umma za ta gyaru, ko kuma shugabanni za su gyaru su dinga gudanar da mulki a cikin adalci, saboda tarbiya tana samuwa ne tun daga gida. In muka waiwaya baya muka dubi rayuwar ‘yan matan da sai mu ga akwai bambanci da yanzu, tun daga kan ‘yan matan da iyayensu, dan galibin iyayen da suna kokari suna bayar da gudummawa wajen kame kansu daga kwadayin irin mazajen da suke zuwa wurin ‘ya’yansu, kuma suna tsawatarwa ‘ya’yan tare da sa musu idanu a kan al’amuransu na yau da kullum.

Kuma al’adun mutanen da suka shude wajibi ne makwabci da ‘yan’uwa su taimaka wajen tarbiyar ‘ya’ya, kuma ko wanne irin laifi ya ga dan makwabcinsa ya yi kai tsaye zai tsawatar masa ko ya tari uban ya sanar da shi don a gaggauta daukar mataki, amma yanzu iyaye ba sa son laifukan ‘ya’yansu, Sun fi so ai ta yabon ‘ya’yan, ko da kuwa ba su yi abin yabon ba, ko a yi shiru a zuba musu ido su ci karensu ba babbaka, ba dama makwabci ya fadi wani gyara ga dan makwabcinsa sai abin ya zama jidali, in an yi sa’a uban ya yadda to uwa mace sai ta ce atabau ba ta yadda ba, an yi wa ‘yarta sharri.

Wasu iyayen dai fatansu su ga saurayi dan mutunci na zuwa wurin ‘ya’yansu. Yayin da mafi yawancin iyayen yanzu idanunsu suka fi karkata kan mai dukiya, ko ‘ya’yan manya ba wai dole mai kyakykyawan hali ba ko mai mutunci. Sannan al’adun ma na ‘yan matanci ya sauya, irin su kunya da kawaici yanzu galibin ‘yan matan ba sa yi, su kan bude baki su fadi duk wata kalma da suka san za ta ja hankalin namijin da ba mujinsu ba, don kawai cimma wasu bukatu na kyale-kyalen rayuwa. Wasu ma kan fita wuraren shakatawa tare, su hole son ransu iyaye na gida.

Har kullum wajibi ne mace ta-gari ta san cewa babu soyayyar da ta kai ta aure dadi da armashi.

Masana da yawa sun bayar da bayanai kan dadin soyayya a gidan aure saboda halaccin aure a tsarin ko wacce al’ada ya ba da damammaki na kusantar juna tare da debe kewa.

Don haka in har namiji na son mace da gaske to ya aureta ya kaita gidansa ya gwada mata duk launin son da ya dace. Ba maganar doguwar soyayya a waje, a yi shekara da shekaru ana abu daya, wani bi ma har sai an kai ga yin abin da ba a so, sannan kuma daga baya a yi aure, to wajibi ne mace ta sani tsawaita rayuwar ‘yan matanci na kashe sha’awarta a gidan aure a na yinsa ne don kunya da mutunci, in suka gushe kuma da wuya zaman aure ya yi dadi.

Ai da ba a fiye yawan sake-saken aure ba kamar yanzu, saboda ‘yan matan da yawancinsu suna matukar kame kansu daga duk wani abu da zai zubar musu da mutunci, kuma da wuya ka samu soyayyar son zuciya, wato mace ta rinka nunawa namiji soyayya a fili bayan a zuciyarta ba ta son shi abin hannunsa take so.

Su sukan yi soyayya ne dan suna son mutum har zuciya, dan Allah ba wai dan wani abin duniya ba, ko kwadayin wani mukami ko matsayi da yake da shi ba, sannan ba su da wata cikakkakiyar sakewa da namiji in ba mujinsu ba ne, kuma ko wayewar tara samari barkatai ma ba su da ita, irin na ‘yan matan yanzu wanda sai ka samu mace da samari goma kuma duk iyayenta na sane, a cewarsu wai ba sa son su yi mata auren dole.

Sabanin mutanen da, in dai mutum na farko ya turo ta ce ba ta son shi, to da wuya ta ki na biyun, wanda da wuya a hada shekara ana zance ba a yi auren ba. Haka ne ya sa auren mutanen da yake karko saboda an gina shi da tubala masu kwarin gaske.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Za A Magance Amosanin Baki
Ado Da Kwalliya

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

October 4, 2025
Hadin Tsumin Baure
Ado Da Kwalliya

Hadin Tsumin Baure

September 27, 2025
Gyaran fuska
Ado Da Kwalliya

Gyaran Fuska Da Laushin Fata

August 30, 2025
Next Post
Kasar Sin Na Kokarin Inganta Muhallin Teku

Kasar Sin Na Kokarin Inganta Muhallin Teku

LABARAI MASU NASABA

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version