Ƴan Ta'adda 284 Sun Miƙa Wuya Ga Sojojin Haɗaka
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƴan Ta’adda 284 Sun Miƙa Wuya Ga Sojojin Haɗaka

byAbubakar Sulaiman
1 year ago
Ƴan Ta'adda

Nasarar yaki da ta’addanci na ci gagaba da samuwa, domin a tsakanin 10 zuwa 17 ga Yuli, 2024, mayakan Boko Haram 284 tare da iyalansu sun mika wuya ga rundunar hadin Gwuiwa ta kasa da kasa (MNJTF) a Kamaru. Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi, Shugaban sashen Hulda da Jama’a, ya bayyana cewa dakarun sashi na 1 sun karbi mayaka biyar a Wulgo a ranar 11 ga Yuli, 2024. Bayanai na farko sun nuna cewa wadannan mayakan sun fito ne daga Tumbuma da Kutumgulla a karamar kukumar Marte ta Jihar Borno, Nijeriya.

A wannan ranar, Malum Kori Bukar, mai shekaru 50 da ya tsere daga maboyar Jibilaram, ya mika wuya ga dakarun. Haka zalika, mayaka 19 sun mika wuya a Madaya, Arewa Maso Gabashin Kamaru, da wasu 11 a Wulgo. A ranar 12 ga Yuli, mayaka 64, ciki har da manya shida, mata 20, da yara 38, sun mika wuya a Bonderi, Kamaru.

  • An Tafka Gumurzu, Sojoji Sun Kashe Ƴan Boko Haram Da Yawa, Wasu Sun Miƙa Wuya
  • Boko Haram Sun Sace Wani Alkali Da Matarsa Tare Da Awon-Gaba Da Wasu Mutane A Borno

A ranakun da suka biyo baya, 27 mayaka sun mika wuya a ranar 13 ga Yuli, 102 a ranar 15 ga Yuli, da wasu biyar a ranar 16 ga Yuli. A ranar 17 ga Yuli, mayaka 48, ciki har da maza 10 manya, mata 15, da yara 23, sun mika wuya.

Ƴan Ta'adda

Bincike na farko ya nuna cewa wadannan mutane 48 da suka mika wuya a ranar 17 ga Yuli sun fito ne daga al’ummomin Nijeriya. An mika su ga dakarun Operation Hadin Kai domin daukar matakan da suka dace.

Ƴan Ta'adda

Mika wuyan da ake cigaba da samu yana nuna kokarin da ake yi na tarwatsa cibiyoyin ‘yan ta’adda a yankin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sojoji Sun Ƙaryata Rahoton Cewa Ƴan Bindiga Sun Mamaye Sansaninsu A Kwara
Tsaro

Sojoji Sun Ƙaryata Rahoton Cewa Ƴan Bindiga Sun Mamaye Sansaninsu A Kwara

October 5, 2025
Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 450, Sun Ceto Mutane 180 A Satumba — DHQ
Tsaro

Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 450, Sun Ceto Mutane 180 A Satumba — DHQ

October 4, 2025
Bayan Sulhu  Da Ƴan Bindiga, An Saki Mutane 70 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina
Tsaro

Bayan Sulhu  Da Ƴan Bindiga, An Saki Mutane 70 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina

September 22, 2025
Next Post
Dalilin Raguwar Rikicin Manoma Da Makiyaya A Jihar Gombe

Dalilin Raguwar Rikicin Manoma Da Makiyaya A Jihar Gombe

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version