Rundunar ‘yansandan Jihar Benue ta tabbatar da sakin ɗalibai mata uku da aka sace daga Jami’ar Noma ta Joseph Sarwuan Tarka da ke Makurdi.
An sace daliban ne a ranar 25 ga Fabrairu, 2025, yayin da suke dawowa daga karatu da daddare, lamarin da ya tayar da hankula kan matsalar tsaro a jami’ar.
- Majalisa Za Ta Binciki INEC Kan Jinkirin Gudanar Da Zaben Cike Gurbi
- An Fara Haska Fim Din Sin A Sinimomin Najeriya Da Ghana Da Laberiya
Labarin fitowarsu ya bayyana ne a yau Alhamis, a wata sanarwa da Gidan Talabijin na Najeriya (NTA) ya wallafa a shafinsa na X.
Tun bayan sace su, hukumar jami’ar ta ayyana hutun tsakiyar zangon karatu na mako guda don ɗaukar matakin tsaro.
Duk da ba a bayyana cikakkun bayanai kan yadda aka sako su ba, sakin ɗaliban ya faru ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan taɓarɓarewar tsaro a manyan makarantu a Nijeriya.