Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Rayuwar Sayyadina Abubakar Da Ayyukansa Na Yada Addinin Musulunci (II)

by
3 years ago
in TARIHI
5 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Cigaba daga inda muka tsaya a makon jiya.

Haka shi ma Bilal Dan Abu Rabah Radiyallahu Anhu (Ladanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama), Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu ya same shi ana azabtar da shi, sai ya saye shi daga mai gidansa Umayyatu Dan Khalaf, ya diyauta shi (Yantawa). Shi ma kuma ya halarci yake – yaken Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.

Sai kuma Zinnirah, wata baiwar Allah da Umar Dan Khaddabi Radiyallahu Anhu ya mallake ta kafin musuluntarsa, ya kuma rinka azabtar da ita har sai da ta rasa idanunta, sannan sai Mushrikai suka ce, Lata da Uzza sun la’ance ta shi ya sa ta ma kance. Amma imaninta da Allah ya sa Allah Madaukakin Sarki ya mai da mata da ganinta, sai suka ce, wannan yana cikin sihirin Manzon Allah. A kan wannan baiwar Allah da izgilin da mushrikai ke yiwa Musulunci a kanta aya ta sha daya daga suratul Ahkaf ta sauka. Sayyadina Abubakar ya fitar da ita daga kangin bauta don ta samu ‘yancin ba da gudunmawa ga addinin Allah.

Labarai Masu Nasaba

Tarihin Kafuwar Masarautar Nupe Da Jerin Sarakunanta

Tsarin Shugabancin Hausa/Fulani Gabanin Zuwan Bature

Ba wadannan kadai Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu ya saya ya ‘yanta su saboda Allah ba, akwai wasu bayi daga kabilun Banu Adiyyin da Banu Abdul Shamsin su ma sun more ma karamcin Sayyadina Abubakar da kishinsa ga addini wajen samun wannan babbar garabasar da yake neman yardar Allah da Manzonsa a kanta.

Kadan Daga Cikin Darajojinsa:

Babu wani daga cikin Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama wanda ya tara darajoji musamman wadanda ya kebanta da su idan kacire Ahlul Baiti (iyalan gidan Annabi) kamar Sayyadina Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu.

Daga cikin darajojinsa akwai tsananin kusancinsa ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da kasancewarsa abokin sirrinsa. Misali, shi kadai ne wanda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya sanar da shi yana son Uwar Muminai Nana Hafsah Radiyallahu Anhuma kafin ya yi maganar aurenta.

Ga kuma ayoyin Alkur’ani da suka sauka suna yaba ma halayensa na jarunta da karamci da tsoron Allah. (Suratut Taubah aya ta 40 da Suratuz Zumar aya ta 33 zuwa 35 da kuma Suratul Lai aya 17 zuwa 21).

Ga shi kuma ya tara dukkan ayyukan alheri da suka sa za a kira shi ta dukkan kofofin aljanna. (Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim).

Ga kuma fifikonsa na ilimi a kan sauran Sahabbai (in ka cire Sayyadina Ali saboda shine kofar ilimin Annabi), domin dukkansu sun aminta cewa, bayan dai ya kebanta da sanin ilimin nasaba (Dangatakar mutane da sanin tarihin kakanninsu) kuma shi ne ya fi su ilimi daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. (Sharhin Imam Nawawi a kan Sahihu Muslim (15/150)).

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi mafarkin an kawo masa madara a cikin wata kwarya sai ya sha har ta gudana a tsakanin fatarsa da tsokarsa, sannan sai ya bai wa Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu. Sahabbai suka fassara wannan da cewa, ilimin da Allah ya ba shi ne ya rage wa Sayyadina Abubakar. Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce, kun yi dai-dai! Kun yi dai-dai!!

Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu kuma shi ne mafi tsentseni da tsoron Allah a cikinsu. Saboda tsentseninsa ne ya taba amaye madarar da ya sha domin ya yi shakkar halalcinta. Haka kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ba shi shedar tawali’u da rashin girman kai a lokacin da ya ce masa, kai ba ka jan tufafin ka saboda girman kai.

ADVERTISEMENT

Jarumtarsa Da Tsayuwar Ra’ayinsa:

Da yawa daga marubuta tarihi suna kallon Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu a matsayin mutum mai rauni, maras kuzari, wanda sanyin halinsa ya rinjayi karfin jikinsa. Sukan dauki Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu a matsayin kakkarfa, matsananci, mai kazar kazar. Wannan sai ya sa mafi yawan makaranta suka kuskuri fahimtar wane irin mutum ne shi Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu.

Ga wasu ‘yan misalai a gurguje da za su wargaza wannan gurguwar fahimta nan take:

An tambayi sayyidina Ali Alaihi Salatu Wasallamu wane ne duk ya fi ku jarunta? Sai ya ce, ba shakka ni ban taba fito na fito da namiji ba sai na kada shi. Amma a cikinmu babban jarumi shi ne Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu. Sai Sayyadina Ali Alaihi Salatu Wasallamu ya ba da labarin irin bajintar Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu yayi a ranar da aka yi yakin Badar wanda shi ne karo na farko da Musulmai suka fara sanin yaki.

Babu wani yakin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya fita ba tare da Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu yana tare da shi ba. Ya kuma shugabantar da shi a kan rundunar yaki ba sau daya ba, kuma ba in da ya je ba tare da Allah ya ba shi nasara ba. Misali a shekara ta bakwai bayan hijira, shi ya jagoranci rundunar da ta yaki Banu Fizarah ya ganimanto dukiyarsu.

Sannan shi ya ke rike da tuta a yakin da ya fi ko wane tsananta a kan Musulmai, shi ne yakin Tabuka. A ranar yakin Hunaini kuwa Musulmai sun sha wahalar da ta sa akasarinsu suka ja da baya kamar yadda Allah ya fada a aya ta 25 a Suratu Ali Imran. Amma duk da haka Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu ya tsaya wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yana ba shi kariya tare da ‘yan kadan daga cikin Sahabbai wadanda suka hada da Sayyadina Umar da Ali da Fadlu Dan Abbas da babansa Abbas da Usamatu da Abu Sufyan Dan Harisu Radiyallahu Anhuma. To, wane irin kuzari mu ke nema ga wanda yake a duk yake – yake shi ne yake tare da jagoran tafiya Sallallahu Alaihi Wasallama? Wannan shi ne raggo? A dai sake nazari ya yan uwa!

Wani muhimmin abu game da Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu shi ne kasancewar sa mai tsayayyen ra’ayi wanda ba a saurin girgiza shi. Wannan dabi’a ce da ta ke taimakon shugaba. Mu tuna yadda Sayyadina Umar Radiyallahu Anhu ya ringa jayayya da shi a kan yakar wadanda suka soke rukunin Zakka da hujjar cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne kawai Allah ya ce ya karbe ta, tun da kuwa ya yi wafati babu sauran ba da Zakka.

A daidai lokacin da Sayyadina Umar ke ganin a dakatar da yakarsu har komai ya koma dai-dai, Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu ya nace ya wajabta a ya kesu kuma daga karshe Sayyadina Umar ya gamsu, sannan Allah ya ba su nasara. Sayyadina Abubakar ya kuma yi jayayya da Usamatu Dan Zaidu Radiyallahu Anhu da mafi yawancin Sahabbai a kan tafiyar rundunar Usamatu bayan ainihin wafatin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Duk a wadannan wurare Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu shi kadai yake a ra’ayinsa, kuma bai ja da baya ba har sai da Allah ya nuna wa mutane cewa ra’ayin nasa shi ne dai-dai.

Wane irin kuzari muke nema ga Sayyadina Abubakar Radiyallahu Anhu? Mutumin da kowa ya rude a lokacin wafatin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama har ba mai iya ba da sanarwar haka sai shi. Wanda ya yanke hanzarin duk mai wata shakka ko mai nufin ya sauya tafiya bayan wafatin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin wannan hadaddiyar hudubar tasa. Irin wannan hudubar ce kuma ya yi wadda ta raba gardama a Sakifa lokacin zaben khalifa na farko.

Za mu dakata a nan, sai wani makon mai zuwa idan Allah ya kai mu da rai da lafiya za mu cigaba. Kar ku manta ku na tare da dan ‘yar uwarku, Mohammed Bala Garba, Maiduguri. 08098331260.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

KSSSMB Za Ta Tabbatar Da Nasarar Ilimi Kyauta A Kano

Next Post

Matsalar Tsaro Ba Za Ta Hana Yin Zabe A Rafi Ba – Shugaban Riko

Labarai Masu Nasaba

Masarautar Nupe

Tarihin Kafuwar Masarautar Nupe Da Jerin Sarakunanta

by
8 months ago
0

...

Hausa/Fulani

Tsarin Shugabancin Hausa/Fulani Gabanin Zuwan Bature

by
9 months ago
0

...

Coomassie

Tarihin Tsohon Sifeta Janar Na ‘Yan Sanda Ibrahim Coomassie

by
10 months ago
0

...

Mai Martaba Aminu Ado Bayero: Sarkin Kano Na 15 A Daular Fulani

Mai Martaba Aminu Ado Bayero: Sarkin Kano Na 15 A Daular Fulani

by
11 months ago
0

...

Next Post

Matsalar Tsaro Ba Za Ta Hana Yin Zabe A Rafi Ba – Shugaban Riko

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: