Connect with us

TATTAUNAWA

12 Ga Yuni: An Maida Mu Shekara 25 Baya – Sanata Hanga

Published

on

A cigaba da bayyana ra’ayoyi tun Ranar Dimukradiyya a Nijeriya bisa nasara ko akasin haka da a ka samu a mulkin farar hula daga 1999 zuwa 2020, mutane da dama su na cigaba da bayyana mabambantan ra’ayoyi kan wannan ranar. Wannan ya sa wakilin LEADERSHIP A YAU, HARUNA AKARADA, ya samu ganawa da mai fashin baki a duk wani sha’ani idan ya taso. Wannan mutum kuwa shi ne SANATA RUFAI SANI HANGA, tsohon sanatan Kano ta Tsakiya kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa a matsayinsa na wanda a ka kafa shi da ita. Sanata Hanga ya tabo abubuwa da dama na rayuwar al’umma, musamman ma wannan lokacin na annobar Korona da sauransu. Ga dai yadda hirar ta kasance:

 

A wannan tunawa da Ranar Dimukuradiyya ta 2020, yaya sanata ya kalli wannan ranar?

To, abinda zan ce a kan cigaba ko rashin cigaba jama’a da dama sun fada, amma ni a ganina an ja mu baya. Shekara 25 baya a ka maida mu. Kawai dai abinda zan ce a kan Ranar Dimukradiyya ta 12 ga Yuni ba ta dace da Ranar Dimukradiyya ba; 29 ga Mayu ce ta dace da Ranar Dimukradiyya, amma ba wannan ranar ba, domin wannan ranar ta ranar ta 29 ga Mayu ita ce ranar da soja ya ba wa farar hula mulki. Wannan ta 12 ga Yuni rana ce da a ka ce Marigayi Abiola ya ci zabe. A wannan lokacin ma ai mu ne Abiolan, domin ni ma ai na ci zabe. Duk mun shiga zabe a wannan locacin a ko’ina tare da shi, mu ma ’yan jam’iyyar ne. To, a wannan lokacin an ce ya ci zabe, ba a ba shi ba. To, ko ya ci ko bai ci ba, zato ne, tunda ba a yi sanarwa ba, to amma dai a na cewa, ya ci an soke, sai wani bangare na kasar nan su ka tayar da bore, saboda tsaro da kwalama ta ’yan Arewa, shi ne yanzu wai a ka ce 12 ga Yuni wani abu ne, kuma ai an biya su. Abinda ya sa na ce an biya shi ne, da zabe ya zo a ka hana kowa tsaya wa takara sai Yarabawa, wato mutum biyu; Falaye da Obasanjo. Duk Yarabawa ne. Duk wani dan Arewa a ka hana shi. Obasanjo ya hau ya yi shekara takwas ya na mulki. Yanzu wannan ba a biya su ba? Me a ke nema? Kuma kafin Obasanjo ma ya yau, Shonikan a ka bawa. Ko iya Shonikan an biya su. Da su ka hau su ka rusa mu, su ka gina kansu. Wannan ya sa har yanzu Arewa ba ta farfado daga halin da ta ke ciki ba. Sa wannan ranar da a ka yi a matsayin Ranar Dimukradiyya kawai fadanci ne! Wannan tsoro ne, bukata ce, rashin shawara ne kuma ba inda za ta kai mu! Duk wani fadanci da za a yi mu su, ba za mu birge su ba, duk abinda a ka yi mu su korafi su ke yi a kanmu a na ta gina su, su na kin godiya, kuma shuwagabanninmu su na yin haka ne, saboda bukatar kansu da iyalansu. Arewa an gama ruguza ta, yanzu Arewa talauci, rashin ilimi a Arewa ga rashin zaman lafiya, amma har yanzu lallaba su a ke yi; wai 12 ga Yuni. Sai a yi kasafi 85 a je a kashe mu su, mu kuwa a na kashe mu a nan, kuma abubuwa da ke zagawa cewa mulkin ma su za a baiwa. To wannan kashe-kashen da a ke yi yanzu a na dan tura jami’an tsaro, to nan gaba sai dai Allah ya kare, domin da ma wannan rashin tsaron a nan ka ga sai dai su ce ‘ku ci kanku’. Da ma mu na da rashin ilimi, ga talauci, domin idan wannan masifa ta ki karewa, idan su ka samu mulki, ba abin kunya ba ne su ce a bar kasar.

 

Duniya ta shiga annobar Korona, inda a ka umarci daukar mataki, domin guje wa wannan cuta, ga shi wasu gwamnoni sun bada umarnin bude gidan kallo da ma wasu guraren. Ya ya ka ji umarnin?

Eh to, wannan magana ce ta Kano. A Kano ne a ka bude gidan wasanni, amma ba a bude makarantun islamiyya ba, ba a bude kasuwanni yadda ya kamata ba, ba a bude sauran gurare na amfanin al’umma ba. To, a ganina cewa, wai sai abinda Gwamnatin Taraiyya ta ce, karya ne, domin kowanne gwamna ya na da ikon gudanar da mulkinsa yadda ya ga dama. Wannan maganar ba haka ta ke ba, kuma yanzu ni ba na goyan bayan a kulle ko’ina, domin wannan ciwon dole a koyi zama da shi. Kawai mu saba zama da shi, kamar yadda mu ka saba zama da maleriya. Mu dauki matakai kamar yadda mu ke sayen gidan sauro, don kada ya sa ma na maleriya. To, shi ma ya kamata mu koyi zama da shi, a kyale kowa ya fita ya yi mu’amularsa, amma don an bude gidan kallo, ba ya damu na, kawai dai sauran guraren ma a bude su mana. Wannan ya sa mutane su ke ta zarge-zargen cewa wasu kudade su ka hada (su masu gidajen kallon) a ka ba wa gwamna. Ka ga wannan ba daidai ba ne kuma sannan rashin mashawarta ne. idan ma sharri ne, sai a yi, kuma cunkoson gurin bal ai ya fi na makarantar islamiyya, domin ai makarantar islamiyya a jere su ke, a shirye, ba kokawa, ba ihu, saboda ba jin dadi ne ba.

 

Idan mu ka koma bangaren tsaro, Gwamnatin Tarayya ta zargi sarakunan gargajiya cewa, su na da masaniya a kan hare-hare. Meye raayinka?

Wannan zargi da a ke yi wa sarakunan gargajiya cin mutunci ne. Duk abubuwan da a ke yi a Kudu, an taba jin an zargi wani basaraken gargajiya? Mu dai ba mu san ciwon kanmu ba! Haka shi ma Mai Magana da Yawun Shugaban kasa duk abinda Afenifere za ta fada kan ’yan Arewa ko a kan Shugaban kasa, Femi Adesina, bai taba magana ba, amma saboda Farfesa Ango Abdllahi ya yi magana, ya zo ya na mayar ma sa da martani. Sanda a kai ta kashe-kashe a irinsu Legos da wasu garuruwa, ka taba ji an ce sarakunan gargajine su ke kashe ’yan Kudu? Ba a taba fada ba, kuma sarakuna nawa a ka kashe a Katsina, kuma kamar Borno da Zamfara a ina ne ba a kashe sarkin gargajiya ba?

 

Yaya ka kalli shekara ta 223 za ta kasance bisa la’akari da yadda abubuwa su ka zama yadda su ka zama?

To, ni dai ba na duba, amma Ina fata ta kasance cikin alkhairi. Yanzu dai talakawa da al’umma sun shiga taitayinsu, domin tun Jamhuriya ta daya abinda a ka dauke mu ’yan tsaki, domin na ji an ce, wasu su na nan su na yin wani kwamiti. To, su sani, babu abinda zai yi mu su sai dai ya sake mai da mu baya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: