Muhammad Awwal Umar" />

Dole Sarakuna Su Nemi Majalisa Ta Ba Su Aiki – Awaisu Giwa

ALHAJI AWAISU MUHAMMAD GIWA shi ne ko’odineta mai kula da mu’amalar al’umma na Gwamnan Jihar Neja kuma mai rike da sarautar Wakilin Gbagyi Nupe. A hirarsa da manema labarai ranar Juma’ar makon jiya, ya nuna takaicinsa kan yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya ya kasa samar da hurumin da zai bai wa sarakunan gargajiya ayyukan da ya kamata su rika yi wa al’umma, inda hakan ya kai ga ‘yan siyasa su na taka su yadda su ka ga dama. Wakilin LEADERSHIP A YAU, MUHAMMAD AWWAL UMAR, ne ya rubuta hirar, kamar haka:

Ranka ya dade, jama’a na ta tsokaci kan yadda ‘yan siyasa ke taka sarakunan gargajiya ba tare da la’akari da darajarsu ba. Shi ka na ganin wannan ya dace?
Da farko ina bakin cikin irin yadda ake taka sarakuna musamman a Arewacin kasar nan, domin lokacin da turawan mulkin mallaka suka shigo kasar sun iske mu da al’adun mu, da shugabannin mu wato sune sarakunan gargajiya, turawan nan sun mulke mu tsawon shekaru arba’in amma duk cewar basu da al’ada da addini bai hana su zama suna shawara da sarakunan mu ba. Kuma ba su taka mu kamar yadda a yanzu da muke da yawan al’umma, yawan kasa da hanyoyin kudaden shigar mu ba, sai dai sun dan taba wasu sarakunan, irin wannan abin idan ya cigaba da wanzuwa za a mai da gidajen sarautun mu kamar gidajen siyasa, in ko hakan ya faru lallai sai wata rana an nemi baiwa mutum sarautar gargajiya ya tsallake yaki karba, ya kamata a ja layi haka nan, domin ba daidai ba ne dan kana gwamna ka rika kirkirar laifi kana daurawa sarki dan ya fadi gaskiya ko dan kayi kuskure ka gyara sai kuma ya zama ka dora mai karar tsana.

Shin to me ya janyo hakan, musamman idan a ka dubi abinda ya faru da Sarkin Musulmi Dasuki, Sarkin Gwandu Muhammadu Jakolo, sannan kuma yau ya fadawa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II?
Gaskiya ne, da man irin abinda a ke tsoro ke nan ya cigaba da faruwa. Tun farko rahoton Dasuki da ya gabatar lokacin da a ke son shirya kundin mulkin kasar nan, bai wa sarautun gargajiya adalci ba, domin rahoton ne aka yi anfani da shi kuma aka zartas inda aka nuna komai girman sarauta tana karkashin shugaban karamar hukuma ne, kuma wani abu a baya sarakunan nan sune ke ikon kula da tsaro a masarautun su, sune alkalai kuma suke samar da kudaden shiga ta hanyar karban kudin jabgali daga hannun jama’a, yau duk an kawar da su. An mayar da sarakunan mu tamkar kawa ne a wajen taro, an bar su kawai da rawunan su, sanduna da tutoci ba su da wani aikin yi kuma komai lalacewar abu ba su da halin yin magana.
Maganar gaskiya idan aka yi shiru duk gidajen sarautun mu sai an tarwatsa su, dubi abinda ya faru kwanakin nan a jihar Kano, wai a ce ana kallo saboda fadar gaskiya an irin wannan cin mutuncin, wannan ai ba siyasa ba ne sarki yafi kowa kusa da talaka, shin idan sarki bai iya fadawa gwamnati gaskiya da bukatun jama’a ga gwamnati to waye zai fadi, shi ke nan mu yau a Arewa ba mu da manya, ba mu da wadanda ya kamata su tsawata a saurare su, ko kuma shi ke nan dole sai kowa ya amince da abinda gwamnati ta tsara sannan ne za a zauna lafiya, to ina amanar da aka baiwa shugabannin, ya kamata ‘yan siyasa su dawo daga nisan tafiya da suka yi na fadawa daji domin idan aka karya sarakuna a Arewacin kasar nan lallai mu sani halin da za mu samu kan mu sai mun yi nadama.

Amma ba ka ganin kamar fadawar sarakuna a harkokin siyasa shi yake janyo irin wannan yanayin?
Shin idan ba su yi siyasar ba, to me zasu yi. Babu wani dokar da aka tanadar masu na yin aikin al’umma an dai ce su iyayen kasa ne kuma iyayen al’umma, in ko haka ne dole su rika fitowa suna fadawa gwamnati gaskiya, ai bisa al’ada uba shi ke da hakkin tsawata wa ‘yayansa kuma dole su rika sanar da shugabannin halin da talakawa ke ciki domin hakkin su ne, amma ba wai dan sarki ya fito ya jawo hankalin gwamnati kuma sai ya zama abokin gaba ba.

Amma ai kusan idan ka duba yau wasu sarakunan suna siyasan tar da rawunan su ta hanyar nuna goyon baya ga wasu jam’iyyu da ‘yan takarar?
Na ji, to mu dauki misali a jihar Kano, laifi dan mai martaba Muhammadu Sanusi ya fito ya cewa jama’a su yi cancanta kuma ya cewa kotu tayi adalci. Wannan kuskuren na kundin dokokin kasar nan ne, domin da, da gaske kamar yadda ake ce masu iyayen al’umma gaskiya ne da an ba su rawar takawa wajen jawo hankalin shugabannin siyasa, baiwa yiwu mutum ya taka ubansa kuma ya zauna lafiya in har dan kirki ne.

Yanzu ina mafita?
Mafitar nan ita ce, su sarakuna su garzaya majalisar dokokin kasa domin aja layi akan irin wannan sannan ayi dokar da za ta tsare mutuncin sarakunan gargajiya ta hanyar samar masu ayyukan yi domin su yi anfani da shi wajen samun martaba ga jama’ar su kuma ayi dokar da zata hana kowani irin gwamna taba rawanin sarki saboda siyasa muddin ba sun keta hurumin talakawa ba ne.

Kamar take hakkin talakawa kuma?
Yauwa, bari in baka misali da jihar Neja kuma masarautar Minna, domin dukkanin masarautun takwas da muke da su kowani basarake na taka rawar gani gwargwadon iko wanda jama’a ke na’am da shi. Marigayi sarkin minna Bahago mai rasuwa ya kafa turaku masu anfani ga jama’ar masarautar nan, wannan sarkin na yanzu mai martaba sarkin minna, Alhaji Umar Faruk Bahago ya kai shekaru arba’in da doriya akan mulki, saboda girma da bunkasar da masarautar ta ke da shi saboda tubalan da aka dora ta akai, gwamnatin Neja ta Alhaji Abubakar Sani Bello ya dubi wannan ya nemi masarautar tayi gyara musamman na janye kudurinta akan yadda take kokarin baiwa wadanda ba alhalin ba sarautun, ka ga wannan shi ne dattako, ai sarauta ba mukamin gwamnati ba ne balle ka ce zaka rika canja rawunan zuwa wasu wuraren, ita sarauta ana baiwa alhalin ta ne da jama’a suka amince da shi.

Wani shawara za ka baiwa sarakuna, ‘yan siyasa da sauran jama’a mabiya?
Da farko ina baiwa sarakuna shawarar da su cigaba da fitowa dan kare martabar jama’ar su, sannan su kiyaye hakkokan jama’ar da suke jagoranta. Kar su yarda su sanya idanu a cigaba da kirkirar abubuwan da ba zasu anfani kasa da jama’a ana anfani da su wajen cin zarafin jama’ar. Sannan ‘yan siyasa musamman ‘yan majalisar tarayya da su tabbatar sun samar da dokokin da zai baiwa sarakuna abin yi ta yadda zasu iya daga darajar masarautun su da kare martaban jama’ar su, sannan gwamnoni kar su yarda ‘yan fasa kowa ya rasa su cigaba da samun damar kutsowa kusa da su dan ba su miyagun shawarwari domin hakan bai haifar da komai dai mayar da su baya.
Jama’a ina kiran ku da babbar murya ku zama masu martaba sarakai a matsayin su na iyayen kasa, ku taimaka masu wajen samun nasarar ciyar da kasa gaba, sannan ku zama masu biyayya a gare su.

Exit mobile version