Connect with us

LABARAI

Za A Kashe Dala Miliyan 1.5 Kan Gyaran Filin Kwallo Na Abuja

Published

on

Ministan Wasanni da cigaban sha’anin matasa, Sunday Dare, yace za akashe kimanin dala miliyan daya rabi 1.5m don gyaran Filin wasa Na Moshood Abiola dake Abuja Birnin Tarayya.
Ministan ya sanar da hakan ne a yayin ziyarar da yakai filin, yace kudin gyaran za a samar dasune ta hanyoyi masu zaman kansu.
“Za a kashe kusan dala 1.5m don gyaran filin amma akwai hanyoyi da za abi aga an cimma hakan, dole zamu duba kamfanin dayafi dacewa da yin wannan aikin.” Dare yafadawa manema labarai lokacin kai ziyarar.
“muna kan matakin karshe ne, na wanda zamu kawo ma’aikata filin, saboda haka, ina kiran ‘yan Nijeriya dasuka kara hakuri. Muna bin tsarine kafin Muzo kan aikin filin, amma filin zai dawo aiki bada jimawa ba.
Ya kara da cewa: ” kana ganin ai filin yana aiki don kashi 70% zuwa 80% yana aiki. Wurin wankan linkaya yana aiki, Dakin wasanni yana aiki, akwai kujerun zama 60,000 wadanda sun cika sharudan kungiyar kwallon kafa ta duniya – FIFA. Ayi hakuri, sauran gyaran yana nan zuwa ba jimawa.
” Abun tambayar shine, yaushe za a gyara filin kwallon kafa, amma bayan haka komai na aiki. Fitilar lantarki tana aiki, Jami’an tsaro sun dawo, ruwa ya dawo, abunda ya rage kadai shine filin kwallon kafa.” Yafada hakan.
Advertisement

labarai