Abdullahi Muhammad Sheka" />

An Kusa Jana’izar APC A karamar Hukumar Kumbotso–Abubakar Kadawa
Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano
A shirye shiryen da babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ke yi A Jihar Kano, an bayyana cewa kadan ya rage ayi Jana’izar Jam’iyya mai Mulki ta APC, Jawabin haka ya fito daga bakin wanda ya taba yin takarar kujerar Majalisar dokokin Jihar Kano daga karamar Hukumar Kumbotso a karkashin Jam’iyyar APC a wancan lokacin, kafin yada kwallo mangwaro da ya yi domin ya huta da kuda, matashin dan siyasa mai kishin raba matasa da zaman kashe wando, Alhaji Abubakar Salisu Kadawa na wannan jawabi ne a lokacin da yake zantawa da Jaridar LEADERSHIP A YAU LAHADI jim kadan da kammala bikin raba Babura masu kafa biyu da kuma bada tallafin rage radadin zaman gida da ake fama dashi a halin yanzu ga matasan karamar Hukumar Kumbotso.
Abubakar Kadawa wanda matasa ke masa lakabi da wake dan wuri ya bayyana cewa Jam’iyyar APC ta zama buhun kusa domin ta gaza, musamman ganin yadda aka kyautatawa Jam’iyyar zato, amma sai gashi ta baiwa kowa kunya, wanda hakan ga dukkan alamu ke nuna cewa, mu dai a karamar Hukumara Kumbotso lokacin kadan ya rage mu kakkabe ta daga karamar Hukumar mu baki daya, domin rungumar Jam’iyyar PDP wadda a Jihar Kano ko hasidin iza Hasada ya dubi irin ayyukan da limamin Kwankwasiyya ya yi a cikin shekarun da Allah ya bashi dama kowa zai aminta da cewa, jagorancinsa kwalliya ta biya kudin sabulu.
“Mu daman kamar yadda kowa ya sani tare muke da al’ummar mu , bama gudunsu wanda hakan tasa suma basa gudunmu, mun jima muna yiwa tafiyar APC kallon tsanaki wanda har sai da muka kure mata gudu, muka fahimci ashe kaska ce rabi mai jini. Don haka Matasa lokaci ya yi da za’a daina daureku da igiyar zato. Ko ba komai duba da irin tsare tsaren da Gwamnatin APC ke bujiro dasu, zaku yarda dani cewa ba talakawa ne agabansu ba. Wannan tasa muka shata layi kuma muke neman taimakon ubangiji domin ya bamu ikon kwato al’ummar mu daga bakin kura.
Da aka tambayeshi kan kiranye kiranyen da ake masa na fitowa takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya, Kadawa ya bayyana cewa, jama’a su kara hakuri da sauran lokaci, kamar yadda aka sani mu al’umma ne a gabanmu ba kwadayin mulkin ba, saboda haka muna kara baiwa masoya hakuri cewa muna nan muna tuntabar abokanmu da aminai tare da mikawa Allah bukatunmu, domin ya zaba mana abinda da zai zama alhairi garemu da al’ummar wadanda ke nuna mana wannan tsananin kauna” Inji Kadawa.
Alokacin wannan taro an raba Babura masu kafa biyu, tallafin kudade, kayan sana’a ga mata da matasa, sannan kuma da raba takardun daukar aiki da aka samawa matasa masu yawa daga yankin karamar Hukumar Kumbotso. A karshe ya jinjinawa alummar Kumbotoso bisa zabar Jamiyyar PDP a zaben majalisar dokokin Jihar Kano wanda ya gabata, hakan kuma ‘yar manuniyace dake haska fitilar cewa zabe mai zuwa Jamiyyar APC da yardar Allah sai buzunta.

Exit mobile version