Connect with us

TATTAUNAWA

Published

on

Tun daga lokacin da wasu gwamnonin jihohin arewacin Nijeriya suka

dauki matakan kwashe almajirai zuwa jihohinsu, wasu malaman addinin

musulunci da wadanda ke jagorantar wadannan makarantu a jihar Kaduna

suka fito suka nuna rashin goyon bayansu ga matakan da gwamnan jihar Kaduna ya dauka.

Kan haka, wakilinmu a Zariya, ISA ABDULLAHI GIDAN Bakko, ya sami

damar tattaunawa da babban sakarataren  kungiyar Malaman Makarantun Allo na

Reshen jihar Kaduna, MALAM ATIKU SHEKH MU’AZU, at da wakilinmu ya warware zare da abawar  dalilansu na kin

goyon bayan da suka yi ga gwamnatin jihar na matakan da ta dauka, kan

makarantun Allo, ya yi kuma tsokaci ga al’amurra da dama da suka shafi

takwarorinsu malamai da suke goyon bayan wannan shiri da gwamnatin

jihar Kaduna ta aiwatar.

Ga dai yadda tattaunawarsa da wakilinmu ta kasance,

 

 

Tun daga lokacin da gwamnatin jihar Kaduna ta fara kwashe

dalibanku zuwa jihohinsu na asali, wasu matakai ku ka dauka ?

 

 

Babu ko shakka, a lokacin da gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da(

umurnin kwashe dalibanmu zuwa garuruwansu, lokaci ne dab a jihar

Kaduna kawai ba, Nijeriya ke wani hali na kunci, wato na bullar cutar

koronabairos, sai mu ka ba gwamnatin jihar Kaduna goyon bayan ta aiwatar

da wannan tsari da ta sa gaba, amma abin da gwamnati ta ce da farko

shi ne a rage cinkoson dalibanmu, saboda wannan cuta da na ambata,

Ba tare da bata lokaci ba, mu da kan mu, mu ka fara kwashe dalibanmu(

zuwa wajen iyayensu da kudinmu da kuma kudin iyayen dalibanmu, amma ba

gwamnati ta fara kwashe wa ba, kamar yadda ta ke furtawa cewar ta

kwashe dalibai zuwa jihohinsu, said a bayan mun fara, tad an kwashe

wasu.

 

Me ya sa ku tun da farko ku ka goyi bayan tsarin kwashe dalibannaku ?

 

 

To, mun goyi bayan tsarin da gwamnatin jihar Kaduna fito da shi ne,

domin a tunanimu, ta fara rufe makarantun firamare da sakandare da

sauran makarantu da suke karkashinta, mu tunaninmu, mun goyi bayan

tsarin ne cewar, da zarar gwamnatin jihar Kaduna ta bude wadannan

makarantu da suke karkashin ta, mu ma sai mu dawo da dalibanmu su ci

gaba da karatun da suke yi, sai a karshe mu ka fahimci gweamnatin

jihar Kaduna abin da ta ke da shi a boye ne, sa daga baya mu ka

fahimci haka, dalilin day a sa mu ka fito mu ka nuna mu ba mu goyi

bayan rufe makarantun da gwamnatin jihar Kaduna ta yi ba.

 

 

Daga lokacin da ku ka fahimci abin da gwanatin jihar Kaduna ke

nufi, wasu kuma matakai ku ka dauka ?

 

 

Matakin farko da mu ka dauka shi ne na ganin mun nuna wa(

takwarorinmu wukar kugun da gwamnatin jihar Kaduna ke da shi, na

haramta karatun Alkur’ani a makarantun Allo a fadin jihar Kaduna, mun

nuna ma su ka das u tayar da jijiyar – wuya tsakaninsu da gwamnatin

jihar Kaduna, ka da kuma su fito su yi zanga – zanga a kan wannan

matsala da gwamnatin jihar Kaduna ta fito da shi.mu ka nuna ma su

cewar, cikin ilimin da Allah ya ba mu, mu fito, mu bayyana wa

gwamnatin jihar Kaduna kuskuren tad a kuma bayyana ra’ayinmu na nuna

rashin goyon bayanmu baki daya.

 

Ka nufin za ku gurfanar da gwamnatin jihar Kaduna a gaban kuliya ke nan ?

 

 

Babu ko shakka, ba mu da niyyar kai gwamnatin jihar Kaduna kotu, ba(

mu da niyyar yin wata zanga – zanga ko kuma yunkurin aiwatar da wasu

abubuwa day a kauce wa ilimi da mutunci da tarbiyyar addininmu, duk

babu a cikin tsarin da mu ka saw a gaba a halin yanzu, mu ba ma su

kudi ba ne da za mu dauki lauyoyi ba mu da wadanda suka tsaya ma na,

babu ko shakka a matsayinmu na almajirai, mun kai kukanmu ga wanda ya

halicci duk wanda ked a hannu a kuntata ma na da aka yi.

 

Ai gwamnan jihar Kaduna ya dade ya na furta cewar, duk abubuwan(

day a ke dauka, day a shafi addinin musulunci, bay a yanke shawara,

sai ya tuntube ku, ku malamai,me za ka ce a kan wannan batu day a dade

ya na furta wa ?

 

 

Wannan batu day a ke yin a cewar ya na tuntubar malamai kafin ka(

yanke wasu wasu hukumcin aiwatar da wasu abubuwa, babu gaskiya a cikin

wannan magana, sai dai zan yadda in ya na tuntubar wadanda suke goyon

bayan abin day a ke so, in haka ya furta, na yadda da abin da yadda da

maganarsa cewar, ya na tuntubar malaman da suke kin karatun Alkur’ani

kafin ya yanke duk wasu batutuwa da suka shafi addinin musulunci a

jihar Kaduna.

In gaskiya ne, a manyan malaman jihar Kaduna , a kwai Shekh Malam(

Sani Khalifa da Shekh Malam Mai Nasara Tudun Wadan Zariya da Shekh

Malam Umar Mu’azu da ke Zariya, dukkaninsu, babu wanda ya ce an

tuntube she kan wani batu da ya shafi addinin musulunci a jihar

Kaduna.

Ai aa kwai kungiyar makarantun Allo na jihar Kaduna, amma duk

abin da gwamnatin jihar Kaduna ta yi day a shafi makarantun Allo, ta

na fitowa ta bayyana ra’ayinta, ka na nufin ba ku tare da wannan

kungiya ?

 

 

Abin da na ke son ka fahimta a nan shi ne, ita kungiya ko wacce(

iri ce, tamkar jam’iyyar siyasa ce, in waccan manufofin ta ko ayyukan

da ta ke yi ba ka gamsu ba, sai ka shiga wadda ka ke ganin ka gamsu da

manufofin tad a ayyukanta, wadannan dalilai suka sa mu ka kafa wannan

kungiya ta ma su makarantu Allo na gaskiya, sboda mu ba mu yadda wata

kungiya ta ci albasa da bakinmu ba, a nan ne na ke tabbatar ma ka da

cewar, mu ba mu yadda da wata kungiya ba, in ma da ita, ta mu ta

gaskiyar ce.

 

 

Zuwa yau, tun da gwamnatin jihar Kaduna ta ja dagar hana karatun(

Allo da kuma almajranci a jihar Kaduna, wasu matakai na karshe ku ka

dauka kan wannan matsala da ta shafe ku kai tsaye ?

 

 

Matakin da mu ka dauka shi ne na farko mu na tuna wa gwamnan(

jihar Kaduna cewar, ya tuna fa shi kadai ya yi wannan doka ta hana

karatun Allo, maimakon a ce majalisar jihar Kaduna ne ya dace ta yi

dokokin, daga nan gwamnan ya sa hannu a dokar, san nan ya aiwatar da

dokar, kuma kafin ma a fara amfani da ko wace irin doka, ai tsarin

mulkin Nijeriya ya yi tanadin a ji ra’ayoyin al’umma da suke jiha,

kafin majalisa ta yi doka, daga sauraron jama’ar ne, majalisa za ta yi

dokokin da al’umma su ke bukata, tun da tun farko, kamar yadda na

bayyana a baya.Abin tambaya a nan shi ne, shin an bi tanadin da tsarin

mulkin Nijeriya ya tanada ? Shi ya sa kungiyar ma su makarantun Allo

na gaskiya ke yi wa gwamna tunin yadda aka yi wannan doka.

 

 

In gwamnatin jihar Kaduna ba ta canza shawara ba, wani tunani ka(

ke yi wa matasa a gobe ?

 

 

Tabbas, in har hakan ya tabbata, barna ta tabbata a kasa ba a jihar(

Kaduna kawai ba, domin matasan da aka hana su samun ilimin Alkur’ani

da kuma na addinin musulunci an jefa su a rijiya mai gaba dubu, da

fitowarsu sai yadda Allah ya yi, tun da babu wasu tsare–tsare da

gwamnatin jihar Kaduna ta yi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: