Connect with us

RAHOTANNI

Published

on

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da kungiyar RAYAAS Ta Shirya Gabatarwa Cikin Wannan Shekara Da Izinin Allah Jama’a Salamu Alaikum! Bayan dogon hutun da mu ka tafi, na rashin gudanar da tarukan kungiya da kuma wasu muhimman aiyukan da kungiyar RAYAAS ta saba gabatarwa yau da kullum, a sakamakon bullar cutar sarkewar numfashi ta Corona virus a tarayyar Nijeriya, Alhamdu Lillahi yanzu komai ya fara daidaita in sha Allahu zamu ci gaba da dorawa daga inda aka tsaya. Bayan haka muna kara godewa Allah madaukakin sarki da ya takaita mana yaduwar wannan cuta da mace-mace sanadiyyarta a kasashen Afirka, da kasarmu Najeriya, zuwa sauran jihohi. Har ila yau muna godewa membobi da shugabannin da su ka taimakawa ‘yan uwa da abokanen arziki da kayan abinci a cikin RAMADAN da kuma lokacin da aka bada umarnin zaman gida a wasu jihohi, Allah ya saka da alkairi. Sannan kamar yadda sanarwa ta gabata in sha Allahu za mu fara ci gaba da gudanar da wasu daga cikin muhimman aiyukan kungiyar RAYAAS bisa dokokin da hukumar lafita ta shimfida na takaita cunkoson mutane da gujewa haduwar jama’a guri daya, tare da bin shawarwarin likitoci na yawan wanke hannu da kuma addu’a takobin mumini.

kafin zuwan lokacin zan yi amfani da wannan dama wajen yin bayani dalla-dalla, a takaice na wasu daga cikin muhimman abubuwa da ke gabanmu a yanzu….

 1. Shugabanninmu su kara hada kai da juna guri daya a dukkanin matakai, wajen zaburar da membobin kungiya tare da kara musu karsashi da ‘kwarin guiwa game da ci gaban wannan tafiya.

 2. Sannan mu ci gaba da aiyukan bada taimakon jin”kai wanda mu ka soma a baya, kamar zuwa gidan marayu, asibitoci, gidan mahaukata, fursuna, da makarantun gwamnati, da kuma aikin gayya irinsu gyaran makabarta, gyaran lambatu da

 3. A matsayinmu na ‘yan kungiya kowa ya fara tunanin rawar da zai taka wajen tsare-tsare da shirye-shiryen gabatar da taron kungiya na kasa baki daya a babban birnin tarayya Abuja, in sha Allah

 4. Bayan haka akwai manyan tarukanmu na shiyoyi guda uku da kungiya ta ke da shugabanci, kamar haka: Wato a Shiyyar Arewa ta tsakiya b. Arewa maso yamma c. Arewa maso gabas

 5. Kulla alaka mai karfi da kafafen yada labarai na cikin gida da na waje domin su ci gaba da taimaka mana wajen yada kyawawan manufofin wannan kungiya mai albarka.

 6. Kaddamar da yin garanbawul ga wasu daga cikin tsofaffin tsare-tsare da shirye-shiryenmu da su ka daina aiki tare zakulo sababbi masu tafiya daidai da zamani.

 7. Hada hannu da manyan kungiyoyi na duniya masu zaman kansu domin su karawa kungiyar karfi ta tsaya daram da kafafuwanta.

 8. Ci gaba da kokarin bude cibiyar koyawa mata da matasa kananan sana’o’in hannu.

 9. kirkiro da sabuwar gasar kulla zumunci da sanayya tsakanin membobin jihohi mabanbanta da yankuna.

 10. Bayan haka akwai albishir na musamman zuwa ga shugabannin jihohin da su kafi kokari wajen gudanar da ayyukan kungiya cikin wanna shekara, in sha Allahu.

Akwai sauran muhimman batutuwa, amma zan takaita anan, sai mun hadu a rubutu na gaba.

Daga karshe ina mika sakon godiya ta musamman zuwa ga daukacin yan uwa da abokanen arziki da suka yi ta cikiyata a kafafen sadarwa (social media) da wadanda suka kirani da ma wadanda basu kirani ba duk naji sakon ku, na gode sosai. Allah ya kara dankon zumunci.

 

RUWARMU A YAU YOUTH AWARENESS ASSOCIATION RAYAAS

DOKOKIN kUNGIYA TARE DA HUKUNCINSU

 1. Wajibi Ne Ga Duk Dan Kungiya Ya Kiyaye Dokokinta Tare Da Yin Biyayya Gare su. 2. Wajibi Ne Yin Biyayya Ga Shugabanni Da Bin Umurninsu Muddin Ba Su Karya Dokokin Kungiya Ba.

 2. Haramun Ne Dan Kungiya Ya Tura Hotuna/bideos/Audio Na Batsa. 4. Haramun Ne Tura Hotuna/bideo/Audio Na ‘Yan Siyasa Ko Kuma Yawan Hotuna Barkatai A Shafukan Kungiya Ba.

 3. Cin Mutuncin ‘Yan’uwa Babban Laifi Ne. 6. Ba A Yarda Ayi Sa-In-Sa Ko Gardama Marasa Amfani Wadda Zai Iya Tada Jijiyar Wuya Ko Fada Ba. 7. Cin Zarafin ‘Yan’uwa Ta Inbod Ko Pribate Babban Laifi Ne. 8. Babban Laifi Ne Rashin Fitowa A Kungiya Har Tsawon Kwana Uku (3) Ba Tare Da Wani Bayani Ba.

 4. Wajibi Ne Shugabanni Su San Lambobin Wayar Membobinsu Don Isar Da Sako Kai-Tsaye. kA2 10. Babban Laifi Ne Nuna Bangarancin Addini Ko Akida Ko Siyasa. 11. Dakatar Da Duk Wani Posting A Lokacin Da Ake Gudanar Da Wani Shiri A Kungiya.

 5. Wajibi Ne Mutum Ya Fassara Duk Wani Rubutu Da Ya Sanya A Zauruka Ko Shafukan Kungiya Zuwa Harshen Hausa.

 6. Laifi Ne Rashin Sanar Da Kungiya Abin Farin Ciki Ko Akasin Haka Don Taya Mutum Murna Ko Jajantawa. 14. Babban Laifi Ne Ficewa Daga Kungiya Ba Tare Da Wani Gamsasshen Bayani Ba. 15. Kowane Memba Na Da Ikon Yin Rubutu A Zauruka Da Shafukan Kungiya Muddin Bai Taka Doka Ba. 16. Babban Laifi Ne Rashin Halartar Mitin Na Kungiya Har Sau Uku (3) Ba Tare Da Wani Bayani Ba.

 7. Laifi Ne Yin Magana Ko Kiran Waya Ko Amsa Waya A Lokacin Mitin (Meeting) Har Sai An Baka/Ki Dama. 18. Babban Laifi Ne Rashin Biyan Kudin Da Kungiya Ta Sanya Ko Cin Tara.

 8. Wajibi Ne Ayi Wa Duk Wani Sabon Memba Bayanin Dokoki Tare Da Amincewarsa Kafin A Sanya Shi Cikin Kungiya. 20. Babban Laifi Ne Dan Kungiya Ya Bayyana Sirrin Kungiya A Waje Ga Wanda Ba Dan Kungiya Ba.

 9. Dukkan Soyayya Wadda Ba Ta Aure Ba Haramun Ce A Kungiya Ko Kuma Bin Mace A Pribate Ba Tare Da Yardarta Ba, Ko Tura Ma Ta Sakon Batsa.

 10. Wajibi Ne Idan Ka Ga Wadda Ta Yi Ma A Kungiya Ka Sanar Da Shugabannin Kungiya Don Kauce Wa Nema Kan Nema.

 11. Babban Laifi Ne Cin Kudin Kungiya Ko Damfarar Wani Da Sunan Kungiya Ko Amfani Da Logo Ko Sunan Kungiya.

 12. Dole Ne Duk Wani Sabon Memba Ya Bi Ta Hannun Shugaba Na Jaharsa Kafin A Sanya Shi Cikin Kungiya. 25. Ba A Yarda Wani Memba Ya Sanya Sabon Memba A Zaurukan Kungiya (Groups) Ba Sai Da Izinin Shugabanni. 26. Dole Ne Dukkan Memba Ya Cike Form Tare Da Mallakar Katin Shaidar (ID Card) Zama Dan Kungiya Kafin Ya Zama Cikakken Memba.

 13. Duk Wanda Ya Saba Dokokin Kungiya Za A Hukunta Shi Komai Girmansa Da Mukaminsa.

 14. Wajibi Ne A Sanar Da Shugaba Na Kasa Dukkan Hukunci Da Za A Zartar Tare Da Yi Masa Bayani Akan Laifin Da Mutum Ya Aikata Gabanin Aiwatar Da Hukunci.

 15. Babban Laifi Ne Matar Aure Ta Shigo Wannan Kungiya Ba Tare Da Izinin Mijinta Ba.

HUKUNCE-HUKUNCE

(1) Jan Kunne Ga Wanda Ya Aikata Laifi Na Farko. (2) Aikata Laifi Sau Biyu Zai Sa A Dakatar Da Mutum Na Wani Lokaci Tare Da Biyan Tara.

(3) Aikata Laifi Sau Uku Zai Sa A Sauke Mutum Daga MukaminsaTare Da Dakatar Da Shi Na Wani Lokaci. (4) Sannan Ko An Maida Kai Zaka Biya Tara Kuma Ka Yi Hasarar Mukaminka.

(5) Aikata Laifi Sau Uku Ga Memba Kora Ce Kawai Ba Tare Da Mayarwa Ba.

(6) Wanda Ya Fita Kungiya Ba Tare Da Kwakkwaran Dalili Ba, Ba Za A Dawo Da Shi Ba.

Da Fatan Allah Ya Ba Mu Ikon Kiyaye Doka Da Oda Tare Daa Yin Biyayya Gare Su Amin_

Daga Ofishin Shugaba Na Kasa, Shehu Na Amo Dange, (Ubandawakin Dange).

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: