Connect with us

LABARAI

Published

on

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kai ziyarar ta’aziyya a gidan iyalan surukansa, Sanata Abiola Ajimobi wanda ya rasu ranar Alhamis sakamakon cutar korona.

Bayanin da mai taimaka wa gwamnan kan shafukan zumunta Yusuf Shuwaki ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Asabar ya ce gwamnan da tawagarsa sun je gidan iyalan marigayin da ke Lagos, inda ya rasu, domin mika ta’aziyyarsu.

Idris Ajimobi, wato dan gidan marigayin wanda kuma miji ne ga Fatima Ganduje, shi ne ya tarbi tawagar gwamnan, ciki har da mai dakinsa Hajiya Hafsatu Ganduje.

Sanata Ajimobi wanda ya yi gwamnan Oyo na tsawon shekara takwas ya rasu yanada shekaru 70 a duniya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: