Connect with us

RIGAR 'YANCI

Published

on

Akalla sojoji 10 tare da wasu mahara kimanin 20 ne aka kashe, a wani harin kwanton-bauna, wanda mayakan Boko Haram su ka kitsa yi wa sojoji a kan hanyar su; tsakanin hanyar da ta tashi daga Maiduguri zuwa Damboa da Biu a jihar Borno.

A gefe guda kuma, wani soja daya ya rasa ransa kan hanyar da ta tashi daga garin Pulka zuwa Ngoshe; a wata musayar wutar da ta barke.

Kamar yadda mabambantan majiyoyi su ka tabbatar, al’amarin ya auku a bangarori daban-daban daf da wani wajen da ake kira Dogon Waye, mai kimanin tazarar kilo mita 45 tsakanin hanyar Maiduguri da Damboa.

Yayin shi kuma daya harin wanda aka kai shi a hanyar garin Pulka zuwa Ngoshe, inda majiyar mu ta shaidar da cewa, “An kai harin ne a cikin yankin kauyen Bokko, na gundumar Pulka/Bokko a karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno, wanda ya jawo mutum 10 sun samu manyan raunuka sannan kuma wasu sojoji sun yi batan-dabo. Duk da ance sojojin su na kan tafiya zuwa mazaunin su da ke garin Ngoshe a lokacin da harin ya abku.”

“Haka kuma, kauyen Bokko ya na kan hanyar da ta biyo Pulka zuwa Ngoshe, ta bayan tsaunin Gwoza-Mandara wanda ya hada kan iyaka da Jamhuriyar Kamaru.” Ya nanata.

daya daga ganau kuma wani fasinjan da ya tsallake rijiya da baya daga harin, Ali Isa, ya ce “Mayakan Boko Haram ne da dama su ka kai harin kwanton-bauna kan hanyar Damboa da misalin karfe 2:00 na rana, inda su ka budewa motocin sojojin da ke raka jama’a. Yayin da musayar wuta tsakanin bangarorin biyu ya barke, al’amarin da ya jawo mutuwa, wasu kuma su ka arce zuwa cikin daji, don tsira da ransu.”

Har wala yau ya bayyana cewa, kwambar jami’an tsaron, sun hada da gamayyar yan sintiri (CJTF), tare da jami’an tsaro da ke raka motocin jama’a, wadanda su ka fuskanci yan ta’addan, lamarin da ya kazanta sosai da sanya da dama sun arce a daidai lokacin da ake gumurzun.

Haka zalika kuma, shima wani daya daga yan Cibilian-JTF, wanda bai yarda a bayyana sunan shi ba, wanda ya tsallake rijiya da baya a cikin harin kwanton-baunar, ya tabbatar da cewa, sama da yan ta’addan 20 ne aka kashe tare da karin sojoji tara (9) wadanda su ka kwanta dama a cikin harin.

“A cikin musayar wutar, sama da yan Boko Haram 20 ne aka kashe. Kuma cikin rashin sa’a, mun rasa sojojin mu tara (9), wadanda su ke raka matafiya daga Maiduguri zuwa Damboa. Sannan kuma maharan sun arce da daya motar yan sntiri, wadda mu ke aiki da ita, duk a cikin wannan kwambar da ke raka matafiyan,” in ji jami’in sa-kan.

Shi ma wani direba, Usman Abdullahi, wanda harin ya rutsa da shi amma ya yi sa’ar daka-ribas ya dawo Maiduguri, ya ce maharan ba su basu tunkari matafiyan ba.

Amma har lokacin kammala wannan rahoton, rundunar sojojin Nijeriya ba ta ce uffan ba dangane da kai wannan sabbin hare-haren, duk da yunkurin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar- Kanal Sagir Musa, abin ya ci tura.

Advertisement

labarai