Connect with us

RAHOTANNI

Published

on

Manyan ‘yan siyasan Nijeriya 10 suna daga cikin Mutum 689 da suka rasu sanadiyyar cutar ta Korona.
Kusan wata 5 kenan da Nijeriya ta tabbatar da bullar Korona a kasar a ranar 27 Ga Feburairu, 2020. A yanzu haka akwai mutum 30,748 da suka kamu da cutar, akwai mutum 12,546 dasuka warke sannan mutum 689 da suka rasu daga cutar ta Korona a Nijeriya

Manya Daga cikin wadanda suka Mutu Sanadiyyar Cutar Korona sun hada da:

Abba Kyari
Cutar ta fara daukar rai ne daga Villa, inda Shugaban Ma’aikata fadar shugaban kasa Abba Kyari ya rasu a ranar 17 Ga Afrilu,2020. A asibiti dake ikoyi jihar Lagos. Marigayi ya rasu yana da shekara 67. An birne shi a makabarta dake Gudu a Abuja.

Adebayo Sikiru Osinowu
Senata Adebayo Sikiru Osinowu (APC, Gabashin Lagos), Ya rasune a as I bit in  Cardiology consultant, asibitin da Abba Kyari ya rasu. Ya rasune a 15 Ga Yuni, yana mai shekara 64 a duniya

Abiola Ajimobi
Tsohon gwamnan Jihar Oyo, senata Abiola Ajimobi. Ya rasu a 25 Ga Yuni, yana mai shekara 70 a duniya.

Suleiman Adamu
Dan Majalisar Jihar Nasarawa ne, ya rasu 30 Ga watan Afrilu.

‘Yan Majalisa jihar Borno 2
Umar Audi Jauro da Wakil Bukar, suma sun rasu acikin watan Mayu.

Shuaibu Danlami
Ma’aikacin Gidan Gwamnatin jihar Gombe ne, Darakta ne a ma’aikatar kula da ayyuka na musamman akan harkokin Siyasa dake Ofishin Sekataren Gwamnatin jihar.
Ya rasu a watan Mayu, 31 Ga watan.

Wahab Adegbenro
Kwamishinan ne a fannin Lafiya, ya rasu ne 2 Ga watan Yuli, 2020.

Aminu Adisa Logun
Shugaban Ma’aikata fadar Gwamnatin Jihar Kwara ne, ya rasu  7 Ga watan Yuli, 2020.

Tunde Buraimoh
Dan Majalisar Jihar Lagos ne, ya Rasu jiya Jumua da dare.
Advertisement

labarai