Sulaiman Ibrahim" />

Kungiyar kwallon kafar Manchester City ta yi nasara a karar da ta daukaka kan matakin da aka dauka na haramta mata shigar gasar Zakarun Turai tsawon shekara biyu.

Kotun daukaka kara kan wasanni ta bayar da sanarwar cewa an wanke kungiyar “game da fakewa da biyan kudin hannun jari a matsayin gudunmawar daukar nauyi” a wasanni.

A watan Fabrairu UEFA ta haramta wa City buga gasar Turai saboda “keta doka” game da harkokin kudi tsakanin 2012 zuwa 2016.

Kazalika an rage tarar da aka ci City daga euro 30m zuwa euro 10m.

A yayin da take yanke hukunci ranar Litinin, kotun ta ce City ta “gaza bayar da hadin kai ga hukumomin UEFA” amma ta soke hukunci kan dogaron da UEFA ta yi kan hukumar da ke sa ido kan harkokin kudin kungiyar wajen haramta mata buga gasar ta Turai.

City ta ce hukuncin “tabbaci ne na matsayin da kulob din yake kai da kuma irin hujjojin da ya gabatar don kare kansa”.

“Kulob din ya gode wa mambobin tawagar alkalan bisa kokarinsu da kuma sanin ya kamata da suka nuna,” a cewar Man City.

Exit mobile version