Daga Nasir Jibril, Kaduna
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, wato INEC, hukuma ce da gwamnatin tarayya ta kafa domin ta riƙa gudanar da zaɓe a ƙasar nan a duk bayan zangon shekaru huɗu, amma fa ya kamata jama’a su fahimci ƙarfin ikon INEC ya zarce gudanar da zaɓe kawai.
Nazarin da mu ka gudanar ya nuna cewa, hukumar ta na wasu muhimman ayyuka da ta ke iya gudanarwa baya ga zaɓe, waɗanda idan da a ce za a iya wayar da kan talakan ƙasar har ya fahimci yadda ƙarfinta, babu tantama za a rage yawancin maguɗin zaɓen da ke wakana a Nijeriya, wanda shi ne ya ke haifar da samar da shugabanni bara-gurbi. Kuma hakan zai taimaka shi kansa ɗan siyasa maras ƙarfi ya samu tudun dufawa a lokacin da a ka nemi a yi ma sa murɗiyar zaɓe irin wanda a ka riƙa zargin tsohuwar jam’iyya mai mulkin ƙasar, wato PDP.
An kafa INEC a sheharar 1998 zamanin mulki sojoji ƙarƙashin Janar Abdulsami Abubakar, domin ta gudanar da zaɓen 1999, zaɓen da ya maida Nijeriya ka turbar dimokradiyya bayan sojoji sun shafe shekaru su na mulki bayan kifar da Jamhuriya ta Biyu da sojojin su ka yi wa gwamnatin Shehu Shagari.
Gayyar ba ta yi nisa ba, domin sojoji sun rushe hukumar bayan juyin mulkin 1966. Amma kuma bayan shekara biyu sai shugaban mulkin sojoji Ganar Olusegun Obasanjo ya sake farfado da ita a cikin 1978, aka dora mata nauyin gudanar da zaɓen 1979, wato jamhuriya ta biyu. FEDECO ta kuma gudanar da zaɓen 1983.
Daga nan kuma kuma a cikin 1995 sai Janar Sani Abacha ya kafa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, NEC da nufin ta shirya zaɓe. Rasuwar Abacha cikin 1998 ne sai Janar Abdulsalami ya rushe hukumar ya kafa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC wacce tun a lokacin, har yau ta na nan daram da kafafun ta, itace ta shirya zabukan 1999, 2003, 2007, 2011 da kuma na 2015.
Wannan Hukumar Zaɓen ce a yanzu ke hannun Farfesa Mahmood Yakubu domin ci gaba da shirya zabuka a ƙasar nan. Ganin cewa ga zaɓen 2019 nan da ke a gaban Farfesa Mahmood Yakubu, ya dace a fshimce ayyuka, karfin iko da kuma kalubalen da ke gaban wannan hukumar.
An kafa INEC a karkashin dokar ƙasa ta 1999, sannan kuma duk wasu ayyukan hukumar da kuma karfin ikon ta ya na cikin Sashe na 15, Kashi na 1 na Sadara ta 3 da ke cikin Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 da ke cikin Bangare na 2 kamar haka:
Shirya gudanar da zaɓe da kuma tsarawa da shirya zabukan da suka hada da na: Gwamna da Mataimakin sa, Majalisun Dattawa da na Tarayya da kuma uwa-uba ma Shugaban Ƙasa da na Mataimakin sa.
Yi wa dukkannin jam’iyyun siyasa rajista tare da tabbatar da sun kafu ne a bisa dokar da kundin dokokin Nijierya ya gindaya.
Sa-ido a kan al’amurran jam’iyyun siyasa, bin diddigin yadda su ke gudanar da tarukan gangami, yawan kudin da kowace jam’iyya ke kashewa da kuma yadda su ke gudanar da zabukan fidda gwani.
INEC ke da alhakin yi wa masu zaɓe rajista, tabbatarwa sai wanda ya cancanta za a yi wa rajista da kuma sabunta fajista a lokacin da hakan ya taso.
Hukumar Zaɓe ceke da ikon sa-ido a kan yadda kowace jam’iyya ke gudanar da yakin neman zaɓe, kuma ita ke da ikon tsara wa jam’iyyu ka’idar yadda za su rika gudanar da kamfen din na su.
INEC ke da ikon shirya tsare-tsaren wayar wa jama’a kai a kan rajistar jefa kuri’a..
Hukumar ceke da alhakin wayar da kan jama’a domin a muhimmancin gina ingantacciyar dimokradiyya a Nijeriya.
INEC ke da Karfin ikon shirya kiranye a bisa sharuddan da dokar ƙasa ta gindaya.