Daga Bello Hamza,
Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ya yaba wa babban Faston gidan gwamnatin jihar Mosignor Dabid Ajang, da saura malaman addinin kirsita na jihar, akan gudummawarsu na ganin an tabbatar da zaman lafiya a jihar, ya kuma yaba wa Faston akan jajircewarsa na shugabantar al’umma.
Wadanan yabon suna kunshe ne a takardar taya murna da jami’in watsa labarai na Gwamnan Dr Makut Macham, ya sanya wa hannun aka kuma aikawa Faston a bisa nada shi a matsayin shugaban cocin Katolika na yankin Lafia, ta jihar Nasarwa da aka yi kwananan nan.
Ya ce, sabon shugaban cocin katolika na yankin Lafia wanda ya samu sanya albarkacin Paparona Pope Francis, za a cigaba da tunawa da shi akan yadda ya jajirce na samar da zaman lafiya a fadin jihar Filato a tsawon zaman da ya yi a jihar.
Lalong ya kuma ce, yana da tabbacin Sabon shugaban cocin na Katolika na yankin Lafia zai gudanar da ayyukansa yadda ya kamata, zai kuma daukaka yankin ta hanyar kwarewarsa na gudanar da mulki.
Ya kuma mika godiyarsa akan yadda ya ke yin addu’ar zaman lafiya a jihar ba dare ba rana, ya kuma yi masa alkawarin goyon baya a sabon aikin da zai fuskanta a nan gaba.
A shekarar 1994 ne dai aka nada Ajang a matsayin shugaban cocin katolika na yankin Jos.