Ministan Sufuri, Chibuike Amaechi, ya sha alwashin cewa zai shawo kan ababen da suke faruwa a jihar Ribas da zarar ya dawo a 2021.
Amaechi, wanda tsohon gwamnan jihar ne, ya ce nan kusa zai koma jihar domin cigaba da tafiyar da harkokin siyasa gaban-gaban.
Ministan ya bayyana cewa tsohon shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan ya ba shi damarmaki da daman gaske domin ya tsaya a cikin jam’iyyar PDP amma ya ki sakamakon cewa shi din baida kabilanci a tare da shi.
Amaechi wanda ke wannan maganganun a sakatariyar jam’iyyar APC da ke Fatakwal sa’ilin nan da wasu mambobin jam’iyyar PDP suka sauya sheka zuwa APC.
Wadanda suka koma jam’iyyar APC daga PDP sun hada da Cif Alabo Michael West, Dr. John Bazia, Chima Obinna, Chief Salbation Ezengwogwo, gami da dandazon mutane.
Amaechi ya ce, zai koma harkokin siyasa a jihar ne da farawa da addu’o’i.
Ya ce duk da bukatar da Jonathan ya yi ta masa, amma ya zabi ya taimaka wa nasarar shugaba Muhammadu Buhari saboda ba zai taba zama mai fadan kabilanci ba.
Ya ce, tsohon shugaban kasar ya yakesa ne bisa barinsa cikin jam’iyyar PDP, har ma ya kara da cewa Amaechi ya samu nasara ne domin Allah na tare da shi.
Amaechi ke cewa: “A shekara mai zuwa, za mu fara addu’o’i. Kun sani lokacin da Goodluck ya yake mu, ni bai yake ni ba, yaki ya yi da Allah, na kuma sani ba zai samu nasara kan hakan ba.
“Ku shaida musu, daga shekara mai zuwa, addu’o’i za su fara ba-kakkautawa. Zan zo Fatakwal kamar yadda na saba zuwa, kuma, na ce wannan zai faru kuma zai fadu din.
“Bar na fada muku waye ni; ba na shaye-shaye. Ban taba shan kayan maye ko giya a rayuwata ba. Ba na shan taba ta wiwi ko ta sigari. Ba na da kabilanci. Walau jihar Ribas ko Nijeriya, ni dai ba na nuna kabilanci ko kasancewa cikin masu kabilanci.
“Da zan yi kabilanci da na yi, Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ba ni dukkanin wata dama domin na tsaya cikin jam’iyyar PDP. Amma na zabi bin Buhari saboda kawai ba zan nuna kabilanci ba.”
A cewar Ministan lokacin da ya fice daga PDP, kashi 90 cikin dari na ‘yan siyasan jihar sun sameshi gami da jinjina masa bisa wannan matakin da ya dauka.
Ya taya wadanda suka shigo jam’iyyar murna da lale tare da nuna musu cewa barin PDP don APC da suka yi shine matakin da ya dace garesu.
Chief Ibinabo Michael West, wanda ya jagoranci tawagar masu sauya shekan, wanda ya kasance dan takarar gwamna a lemar PDP, kuma wanda ya shiga majalisar dokokin jihar Ribas a matsayin dan majalisa sau biyu, ya kuma yi kwamishina a zamanin da Amaechi ya ke gwamnan jihar.