Connect with us

LABARAI

APC Ta Samu Karuwa A Kebbi

Published

on


Daga Umar Faruk, Birnin Kebbi

A makon da ya gabata ne jam’iyyar APC ta gudanar da bikin karbar wasu manyan jigajigan ‘yan jam’iyyar PDP da su ka canza sheka tun daga matakin shuwagabanin mazaba zuwa na jihar.

Manyan jigajigan jam’iyyar PDP da suka canza shekan sun hada da Daraktan Janar na kamfen din tsohon Gwamnan Jihar Kebbi a jam’iyar PDP Saidu Usman Nasamu Dakingari da kuma dan takarar Gwamna a shekara ta 2015, Manjo Janar Bello Sarkin Yaki mai ritaya, da Ambasada Isah Muhammad Argungu, shugaban jam’iyyar  PDP, da  Alhaji Bello Doya Zuru tsohon mukadashin kakakin majalisar dokoki ta Jihar Kebbi, Jafaru Zuru wanda a kafi sani da (clean) da kuma tsoho sakataren Gwamnatin jihar, Alhaji Nura Kangiwa.

Sauran sun hada da ‘yan majalisar dokoki jihar masu ci a yanzu su uku da suka hada da Mamba Sani LoLo, mai wakiltar Bagudo ta Yamma, Mamba Samai’la Muhammad Bagudo, mai wakitar Bagudo ta gabas, muhammad Tukur, mai wakiltar Shanga tare da dubban magoya bayansu.

Har ila yau, akwai tsofaffin kantommin kananan hukumomi, kwamishinoni da masu ba da shawara ga tsohuwar gwamnatin Saidu Dakingari da ta gabata, su ma sun canza sheka zuwa APC tare da magoya bayan su duk a cikin makon da ya gabata.

Da yake jawabin maraba, Shugaban jam’iyyar APC, Barista Attahiru Maccido ya bayyana jindadin sa da Allah ya nuna ma jam’iyyar sa ta APC wannan rana ta bukin karbar manyan jigajigan jam’iyyar PDP a jihar ta Kebbi inda ya ce ba zai yi mamakin canza sheka da wadannan manyan jigajigan suka yi ba, domin abokanin siyasar shi ne tun farko, iyaka siyasar da ta gabata ne ta raba su.

Barista Attahiru ya kara da cewa “daga yau mun zama abu daya, babu wani banbanci da su da suka shiga jam’iyyar APC yau da mu da muka kafa ta duk daya mu ke ga dokar jam’iyyar”.

Bugu da kari, shugaban jam’iyyar  ya ja kunnen ‘ya’yan jam’iyyar ta APC tun daga mazaba wato (polling unit)  har zuwa matakin jihar (state lebel) da kada wanda ya nuna ma kowa banbanci, ya ce “dukkan ku daya kuke in ji dokar jam’iyyar APC”.

Wadanda suka sauya shekan, sun bayyana cewa sun yi haka ne saboda irin shugabancin da Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya yi a cikin shekara biyu da kuma irin rikicin da ke  cikin jam’iyyar PDP tun daga matakin sama har zuwa jahohi.

Da yake jawabin sa, Gwamna  Abubakar Atiku Bagudu  ya gode wa Allah da da kuma mutanen Jihar Kebbi bisa ga irin goyon bayan da suke bashi har ya iya cinma  nasarar da aka samu a cikin shekara biyu.

Ya kuma gode wa manyan jigajigan da suke canza sheka zuwa jam’iyyar sa ta APC da kuma irin yadda suka lura da irin yadda ya tafiyar da mulkin sa a cikin shekara biyu.

Har ila yau, Gwamna Bagudu ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar tasa da su hada kai da mutanen da suka dawo cikin jam’iyyar domin a kara ciyar da Jihar Kebbi da ma Nijeriya baki daya gaba. Inda ya ce zai kara hinma wurin ganin ya kawo kanfunan da za a saka hannun jari domin jama’a su amfana.

Daga nan ya ce Babban Bankin Nijeriya ya amince da baiwa manoma dubu dari da arba’in tallafin noma a Jihar Kebbi, kana ya yi addu’ar Allah ya kai kowa gidan lafiya.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI