Connect with us

MANYAN LABARAI

BABBAN LABARI: Daminar Bana: Ga Koshi, Ga Kwanan Yunwa

Published

on


 • Farashin Kayan Abinci Zai Fadi Warwas Kwanan Nan — Ministan Noma
 • Wasu Gwamnoni Sun Tsame Hannunsu A Kan Taki — Kwamishina
 • Nazarin Yadda Kudanci Suka Yi Wa Arewa Fintinkau A Aikin Gona

Daga Sharafaddeen Sidi Umar, Sokoto, Muhammad Shafi’u Saleh, Yola, Ibrahim Ibrahim, Kaduna, Muhammad Awwal Umar, Neja, Hussaini Ibrahim, Gusau, Abdullahi  Muhammad Sheka, Musapha Ibrahim Tela, Kano, Khalid I. Ibrahim, Bauchi, Munkaila T. Abdullah, Jigawa, Abdulrahman Abubakar Masagala, Benin

 

A bayyane yake cewar a Tarayyar Nijeriya noma shi ne matakin farko na habaka da bunkasa tattalin arzikinta a shekaru da dama da suka gabata. Bayyanar Albarkatun Man Fetur ne ya zama silar da shugabanni suka yi fatali da bunkasa aikin gona tare da yi masa riko irin na sakainar kashi.

A yau bunkasa akin gona fiye da tsarin nan na daga-hannu-zuwa-baki, lamari ne wanda ke a karkashin manufofin Gwamnatin Tarayya da zimmar farfado da fannin na duke tsohon ciniki a matsayinsa na tushen arziki.

A wata tattaunawa da ya yi da jaridar LEADERSHIP, Ministan aikin gona da inganta yankunan karkara, Audu Ogbe ya bayyana cewa nan da makwanni biyu farashin abinci zai fadi kasa warwas a duk sassan kasar nan, domin gwamnatin tarayya ta kammala duk shirye-shiryen da suka wajaba dangane da haka. Inda ya ce yanzu haka gwamnatin na nan tana tattaunawa da manoma kan batun.

Ministan, wanda ya dora laifin tsadar abincin da ake ciki a kasar nan kan manoma, duk da irin tallafin da suke samu daga gwamnati, ya ce, “duk da yake tsadar abinci ba shi da dadi ga masu saye, amma yana da amfani ga kasa, domin zai zaburantar da wasu su koma gona, wanda a karshe abinci zai yawaita, kuma tilas farashi ya sauka.”

A bisa ga faduwar darajar farashin man fetur a kasuwannin duniya, babban abin da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke karfafawa a yanzu shi ne bayar da kulawa ga fannonin da ba na man fetur ba, musamman fannin aikin gona, wanda a shekarun baya shi ne ke rike da kasa da al’ummarta a matsayin abin dogaro.

Babbar manufa ita ce mayar da noma a matsayin babbar hanyar bunkasa tattalin arziki, ta hanyar mayar da shi fanni mai inganci na kasuwanci. Tuni Gwamnatin Tarayya ta karfafa wa Gwamnatocin Jihohi kan bayar da fifiko ga aikin.

Kodayake wasu masana harkar na ganin cewa ita ma gwamnatin tarayyar akwai gyara a rikon da ta yi wa noman, musamman bisa la’akari da kason da ta ware ma harkar a kasafin kudin bana, inda suke cewa bai kamata a ce an ware masa wannan karo mafi kankanci ba.

Duk da kasar noma mai yawa da ke akwai a wannan kasar, ya zuwa yanzu Nijeriya tana shigowa da abinci daga kasashen waje na kimanin dala bilyan uku zuwa dala bilyan biyar a kowace shekara.

A shekarar 2015, Nijeriya ta shigo da shinkafa tan dubu 580, wanda ya ragu zuwa tan dubu 58 a shekarar 2016 ta hanyar samun nasarar kaddamar da shirin bunkasa aikin gona. Sai dai har yanzu farashin shinkafar da ake nomawa a gida ya zarce na shinkafar da ake shigowa da ita daga waje, lamarin da jami’an Gwamnati ke ganin zai daidaita bayan an yi yabanyar amfanin gona a wannan shekara.

A yayin rangadin yakin neman zabensa, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa ‘yan Nijeriya alkawarin idan suka zabe shi zai bunkasa aikin gona. Ya ce, “dukkaninmu mun san cewar Gwamnatoci da dama da suka gabata sun watsar da aikin gona wanda shi ne babbar hanyar samun kudaden shigarmu. A yau ina tabbatar maku da cewar idan aka zabe ni zan inganta fannin aikin gona, zan mayar da aikin gona babbar hanyar samar da ayyukan yi.”

Shugaba Buhari wanda ya bayyana hakan a gaban daruruwan magoya baya a Jos, Jihar Filato a Janairun 2015 ya bayyana cewar “A bayyane yake cewar sama da kashi 60 na matasan Nijeriya ba su da ayyukan yi, don haka za mu bayar da kulawar musamman a wannan fannin domin samar da aikin yi.”

Duk da shirin inganta aikin gona na Maputo wanda ya ayyana kashe akalla kashi 10 cikin 100 na kasafin kudi a fannin aikin gona har zuwa yau Gwamnatoci da dama ba su fara amfani da wannan shirin ba.

Bincike ya nuna Gwamnatin Tarayya da Gwamnatocin Jihohi za su kashe kasa da kashi biyu cikin dari na Kasafin Kudin wannan shekarar ga aikin gona. Baki daya adadin Naira tiriliyan 13.5 ne za su je ga sashen duk da yekuwar da suka rika yi cewar za su bunkasa fannin aikin gona.

Nazarin kasafin kudi na Gwamnatin Tarayya da na Gwamnatocin Jihohi 30 ya nuna cewar baki daya za su kashe Naira bilyan 254 (kashi 1.8) a fannin aikin gona. Wannan adadin ya karu kadan a kan Naira bilyan 196.3 (kashi 1.6) da aka kashe a fannin a shekarar da ta gabata.

Kusan rabin adadin wadannan kudade za a kashe su ne wajen gudanar da wasu fannoni a ma’aikatar aikin gona da wadanda ke da alaka da su kamar Ma’aikatar Gandun Daji da Lafiyar Dabbobi, Ci gaban Yankunan Karkara da Ruwan Sha da sauransu.

Wannan yana faruwa ne a lokacin da Gwamnati ke yekuwar sadaukar da kai wajen bankwana da fannin man fetur zuwa fannin gona a matsayin hanyar dorewar tattalin arziki.

A shekaru da dama da suka gabata, farashin man fetur yana faduwa kasa ta hanyar jefa kasa cikin matsalar tabarbarewar tattalin arziki ta yadda jihohi da dama ke kasa biyan albashin ma’aikata ballantana gudanar da ayyukan ci gaban al’umma.

Daga cikin Kasafin Kudin wannan shekara na tiriliyan 7.3, Gwamnatin Tarayya ta ware Naira bilyan 123 (kashi 1.6) kawai ga fannin aikin gona. Albashi zai lashe bilyan 31.7 yayin da ragowar bilyan 91.6 za su je ga manyan ayyuka.

Kasafin Kudin Gwamnatin Tarayya na wannan shekara a aikin gona ya zarta na shekarar da ta gabata domin a shekarar da ta gabata an kashe Naira bilyan 75.8 (kashi 1.2). An kashe Naira bilyan 29.6 a fannin da ke da alaka da aikin gona, yayin da aka kashe bilyan 46.17 ga aikin gona.

Bincike ya nuna Gwamnatin Tarayya tana ware adadin da bai taka-kara-ya-karya ba tun daga shekarar 2011 zuwa yau. Misali an ware kashi 1.8 a 2011, kashi 1.6 a 2012, kashi 1.7 a 2013, kashi 1.4 a 2014, kashi 0.9 a 2015 da kuma kashi 1.6 a 2016.

Jihohi 30 ne za su kashe Naira bilyan 131 (kashi 2.1) a aikin gona daga cikin kasafin kudin su bakidaya na tiriliyan 6.2. Wannan ya nuna an samu karin Naira bilyan 11 idan aka kwatanta da Naira bilyan 120. 53 na shekarar da ta gabata.

Baya ga jihohin da ke da albarkar man fetur a Neja-Delta, sauran jihohi duka fannin aikin gona ne kashin bayan tattalin arzikinsu.

Kudaden da jihohin Arewa 19 ke kashewa a aikin gona yana raguwa. Daga cikin bakidaya kasafin kudin jihohin na tiriliyan 2.4 na bana, suna kashe Naira bilyan 88.4 kawai (kashi 3.6), abin da ra ragu sosai idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata na bilyan 97.07. Su kuwa Jihohin Kudu sun ware Naira bilyan 42.2 (kashi 1.1) na bakidaya kasafin kudin su da ya kama bilyan 3.8 na wannan shekara ga aikin gonan.

Yankin Arewa Maso Yamma zai kashe Naira bilyan 43.4 a aikin gona daga cikin baki daya jimilar adadin kasafin kudin yankin na tiriliyan 1.1 a wannan shekara. Wannan ya karu kusan biyu bisa uku na Naira bilyan 60.18 da yankin ya kashe a aikin gona a shekarar 2016.

Daga cikin adadin kasafin kudinsu na bilyan 593.1, Yankin Arewa Maso Gabas ya ware Naira bilyan 24 ga fannin gona. Wannan adadin ya yi kasa idan aka kwatanta da bilyan 29.62 da suka kashe a fannin a 2016. Abin damuwa shi ne, an samu raguwar kudaden ne duk da cewa yankin ya amince ya kara adadin kasafin aikin gonan zuwa kashi goma tun a shekaru uku da suka gabata.

Bayanan da LEADERSHIP Hausa ta samu ya nuna jihohi biyu ne kacal suka ware makuddan kudade a aikin gona, wato jihohin Sakkwato bilyan 14.6 da kuma Ogun bilyan 11.6. A shekarar da ta gabata ma wadannan jihohin biyu ne suka ware kudade mafi yawa wato Sakkwato bilyan 14.96 da kuma Ogun bilyan 10.2.

Jihohin da suka kebe sama da bilyan biyar a kasafin kudi kan aikin gona sune Kogi bilyan 8, Katsina bilyan 8, Akwai – Ibom bilyan 7.4, Borno bilyan 7, Bauchi bilyan 6.7, Kano bilyan 6.6, Jigawa bilyan 6.1, Yobe bilyan 5.7, Anambra bilyan 5.4 da kuma Filato bilyan 5.1. Wannan na nuna jihohin na Kudu sun kunyata na Arewa da ke ikirarin su ne masu arzikin kasar noma.

Da yake bayani kan shirin bunkasa aikin gona, Shugaban Kungiyar Manoma Ta Nijeriya (AFAN) Kabir Ibrahim ya bayyana cewar shirin ba zai samu nasara ba matukar Gwamnatin Tarayya ba za ta rika ware kashi 10 na Kasafin Kudi a fannin aikin gona ba a cikin wa’adin da aka tsara.

Shirin bunkasa aikin gona wanda Gwamnatin Tarayya ta kaddamar a shekarar 2016 ya kunshi tsare – tsare daban-daban kan magance matsalolin shigowa da abinci da ma wadansu matsalolin na daban.

Kamar yadda Ministan Aikin Gona, Cif Audu Ogbeh ya bayyana, “Bisa ga yanayin da muka samu kanmu a tsawon shekaru, yana da matukar muhimmanci mu sake inganta dubarun mu domin bunkasa shirin aikin gona. Daga shekarar 2016 zuwa 2020, shirin Nijeriya kan aikin gona yana bukatar magance wadannan matsalolin da muke fama.”

Abubuwa hudu da Gwamnatin Tarayya ta baiwa fifiko tare da hadin guiwar Gwamnatocin Jihohi sune samar da abinci, musayar abubuwan da ake shigowa da su, samar da ayyukan yi da fadada hanyoyin samun kudaden shiga  kamar yadda kundin bayanin bunkasa aikin gona da manema labarai suka ruwaito ya nuna.

Ministan na aikin gona ya yi bayanin cewar makasudin shirin bunkasa aikin gonan shi ne samar da hanya kwakkwara domin inganta kasuwancin aikin gona wanda zai magance kalubale har guda biyu da aka fi fuskanta.

“Fanni mai zaman kansa zai ci gaba da kasancewa a gaba yayin da Gwamnati za ta ci gaba da bayar da kulawa tare da samar da kayayyakin aiki da sanya idanu.” In ji Ministan wanda ya ce shirin zai yi la’akari da nasarori da darussan da aka koya daga shirin bunkasa aikin gona na Gwamnatin da ta gabata tare da cike gibin da aka samu a manyan tubalai guda uku wato tallata saka jari kan aikin gona, daukar nauyin shirye-shiryen inganta aikin gona da kuma bincike da kirkirar sababbin dabarun kyautata amfanin gona.

A daidai wannan lokacin da Gwamnatin APC ta cika shekaru biyu saman gadon mulki, Ministan Yada Labarai, Lai Muhammad ya bayyana cewar mutanen da dama sun mallaki milyoyin kudi a dalilin karfafa shirye-shiryen aikin gona na Gwamnatin Tarayya.

Ministan wanda ya bayyana hakan a makon jiya yayin da yake bayyana nasarorin rabin wa’adin zango na mulkin Shugaba Buhari, ya ce an karfafawa matasan manoma da dama ta hanyar shirin ‘Anchor Borrower’ da a karkashinsa ‘yan kasuwa ke zuba jari a aikin gona wanda Babban Bankin Nijeriya ya kirkiro da shi da kuma shirin inganta aikin gona na Ma’aikatar Gona ta Tarayya.

Muhammad ya bayyana cewar shirin wanda ya samu gagarumar nasara a fannin noman hatsi da shinkafa a jihohin Kabi, Kano, Jigawa, Ebonyi da Sakkwato ya sanya mutane da dama sun karkata ga aikin gona.

Ya bayyana cewar kokarin na Gwamnatin Tarayya ya taimaka wajen noma shinkafa a cikin gida da rage dogaro da shigowa da shinkafa daga wajen kasa.

Ministan ya kuma bayyana cewar Gwamnatin Tarayya ta yi kokarin rage farashin takin zamani daga Naira dubu tara zuwa Naira dubu biyar bisa ga yarjejiyar da Nijeriya da Kasar Morocco suka sanyawa hannu.

A halin yanzu kuma, domin bin diddigin yadda shirye-shiryen noman daminar bana ke gudana, wakilanmu na jihohi sun yi mana nazari daga bangaren abubuwan da gwamnatoci ke yi da kuma bangaren manoma tare da zakulo matsalolin da ka iya zama karfen kafa ga samun yabanya mai albarka.

 

 • Sakkwato

Baya ga fannin ilimi, sashen aikin gona ne Gwamnatin Jihar Sakkwato ta fi bayar da kulawar musamman a kai. A kasafin kudin wannan shekarar aikin gona ya samu Naira bilyan 14.6.

A makon da ya gabata ne Gwamnatin Jihar Sakkwato ta kaddamar da sayar da takin zamani na kimanin Naira bilyan 1.7 domin amfanin manoma a daminar wannan shekarar.

A jawabin da ya gabatar a Karamar Hukumar Bodinga, Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewar Gwamnatin Jihar ta siyo takin ne daga hannun Gwamnatin Tarayya a kan kudi Naira dubu 5, 500 a kan kowane buhu daya. Ya ce za a sayar da buhun taki daya kan Naira 1, 500 kowane domin karfafawa jama’a da dama kwarin guiwar shiga aikin noma.

Bugu da kari Gwamnan ya kaddamar da rabon iraruwan gero da shinkafa da injunan ban ruwa. Gwamnan ya gargadi jami’an da ke kula da rabon kayayyakin da su gujewa sanya siyasa wajen sauke nauyin da aka dora masu. “Ku sanya tsoron Allah wajen wannan aikin tare da rabawa ga manoman asali kadai. Ka da a baiwa manoman bogi.” Ya jaddada.

Tambuwal ya ce idan aka yi amfani da kayayyakin bisa ka’ida, to za a samu yabanya mai albarka. Daga karshe ya yabawa shirin bunkasa aikin gona na Gwamnatin Tarayya.

Shugaban Kungiyar Manoma Ta Nijeriya (AFAN) reshen jihar Sakkwato Alhaji Murtala Gagadu (Garkuwan Minnnata) ya bayyana cewar manoman da ke karkashin kungiyar sa sun shirya domin gudanar da aikin damanar wannan shekara kamar yadda suka saba.

Ya ce “Kamar yadda muka saba za mu kira kungiyoyin AFAN a Kananan Hukumomi 23 domin tunatarwa da fadakarwa kan muhimmancin gyara gonaki da kuma fara amfani da takin gargajiya gabanin samun takin zamani daga Gwamnati. A Jihar Sakkwato muna da Gundumomi 84, kuma ko’ina kungiyar mu za ta shiga domin kara ilmantar da su abubuwan da suka wajaba. Ko ba komai idan aka fara aikin damina cikin lokaci to akan samu amfanin gona mai yawa.”

A bangaren kulawar Gwamnati kan bunkasa aikin gona kuwa, Shugaban na AFAN ya bayyana cewar “Shakka babu mun gamsu da kokarin da Gwamnatin Jihar Sakkwato a karkashin jagorancin Aminu Waziri take yi kan inganta aikin noma a wannan jiha. A tarihi ba a taba siyo takin zamani mai yawa kamar na wannan shekara ba, haka kuma an yi rahusa sosai domin manoma su amfana. Wani abu mai muhimmanci shi ne wannan Gwamnati tana raba taki cikin lokaci ba wai sai damina ta yi nisa ba wanda hakan abin yabawa ne.”

Da yake tofa albarkacin bakinsa, Alhaji Musa Dan- Dodo Sarkin Noman Gindi ya nuna farin cikinsa tare da yabawa kwazon Gwamnan Jihar Sakkwato a kan kaddamar da sayar takin zamani cikin lokaci a farkon daminar bana.

Ya ce “Akwai alamun samun yabanya mai albarka, manoman gaskiya sun san albarka na nan zube cikin kasa sai in ba a tona ba. Don haka manoma su kara azama da kwazon noman wadata kasarmu da abincin da za muci mu kuma sayar.

A nasa ra’ayin, wani matsakaicin manomi Aminu Bello ya bayyana cewar daminar bana ta riga ta kankama kuma har zuwa yanzu taki bai shiga hannun su ba.

“Muna sane da cewar Gwamnati ta kaddamar da sayar da takin zamani cikin farashi amma matsalar ita ce manoman biro ne suke samun taki akasin manoman kwarai wadanda takin ke wuyar shiga hannun su. A kullum ana ce mana za a magance matsalar karkatar da taki, amma babu wani canji. Muna fatan a wannan karon Gwamnati za ta sanya idanu sosai. Baya ga wannan kudaden da aka kebe na kasafin kudi a fannin gona muna fatan Gwamnati za ta aiwatar da dukkanin abubuwan da aka tsara ba tare da kawar da kai ga wasu ayyuka da shiraruwan bunkasa aikin gona ba.” Ya bayyana

 

 • Adamawa

Manoma a Jihar Adamawa na ci gaba da kokawa game da rashin samun wani tallafi domin bunkasa harkokin noma daga gwamnatin jihar.

Da suke zantawa da LEADERSHIP Hausa, wasu daga cikin manoman a Yola sun ce har kawo wannan lokacin ba wani da sunan tallafi ga manoma da Gwamnatin jihar ta samar mu su.

Malam Adamu Liman wani manomi a Yola, ya ce tun cikin watan uku ya yi rijista domin samun tallafin noma daga Gwamnatin jihar amma har yanzu haka shi dai ba a bashi komai ba. Ya ce abubuwan tallafin ko an kawo ba ma asalin manoman ake bayar da shi ba.

“A cikin watan uku a ce mu yi rijista muka yi har yanzu babu bayani, sai kawai mu ji wai an bayar, wasu da ba manoma ba ne ke amfana da tallafin Gwamnati ga manoma”.

To sai dai gwamnatin jihar na cewa tana bakin kokarinta na ganin ta tallafawa manoma domin bunkasa harkokin noma a jihar, ta ce kan haka ne ta samar da taraktoci 105 domin saukake harkokin noman ga manoma musamman na karkara a jihar.

Da yake kaddamar da taraktocin, Gwamnan Umaru Bindow Jibrilla ya ce kowace karamar hukuma za ta samu taraktoci biyar a daukacin kananan hukumomin jihar 21, haka kuma gwamnatin jihar ta kaddamar da takin zamani a kan Naira dubu shida ga manoma.

Malam Ahmad Sajoh, Kwamishinan ma’aikatar yada labarai da tsare-tsare ta jihar, ya ce baya ga samar da taraktocin, Gwamnatin jihar ta kuma shiga wani shirin hadin gwiwa da wani kamfani domin samar da taki cikin farashi mai rahusa ga manoma.

Sai dai yanzu haka manoma a jihar na sayen buhun taki a kan farashin Naira dubu tara a kasuwa, baya ga kayan aikin feshin ciyayi da maganin kwari da duk su ka yi tashin gwauron zabi a kasuwannin, wanda bai rasa nasaba da rashin isar tallafin gwamnati ga manoman.

Hammatukur Ahmad Jada wani manomi a Karamar Hukumar Jada, ya ce su dai a karkara ba wani tallafin Gwamnati da suka gani a fannin noma, sai ya roki Gwamnan jihar da cewa ya yiwa Allah ya kawo wa manoman karkara dauki a fannin noma.

“Harkokin rayuwa ya yiwa talaka tsada matuka, idan ba tallafin da aka samu ba, ba zai yiwu ka iya seyen taki yanzu a kasuwa ba, domin muna cikin kuncin rayuwa ga komai ya yi tsada”, in ji shi.

Honarabul Hussaini Yusuf (Masta) shi ne shugaban Karamar Hukumar Girei, ya ce yana yin duk mai yiwuwa domin bunkasa noma da tallafawa manoma a karamar hukumar, kana ya ce “bunkasa noma shi ne abin da za ka yi ka taimaki talaka kai tsaye.

“Ka ga wadanan taraktoci biyar da mai girma Gwamna ya bamu zan yi amfani da su domin tallafawa manoma idan da ana biyan dubu talatin yanzu dubu ashirin za a biya.

“Mun yi hakan ne domin tallafa wa talakawa manoma na karkara kasancewar yanzu ba wani abu da za ka yi ka taimaki talaka da ya wuce ka samar da kayan aikin noma ya same shi cikin sauki”.

 

 • Kaduna

A sanin kowa ne a shekaru da dama a kasar nan idan damina ta kama, Gwamnatin Tarraya da Gwamnatocin Jihohi na mayar da hankali kacokan wajen ganin sun fito da wani shiri na musamman domin ganin sun tallafa wa manoma wajen samar masu da takin zamani cikin rahusa da inganci.

Ita ma Gwamnatin Jihar Kaduna ba a barta a baya ba, domin kusan tun  watanni uku da suka wuce, ta kirkiro da wani shiri na musamman wanda zai samar wa monaman jihar da takin zamani cikin inganci da rahusa.

A bincken da LEADERSHIP Hausa ta gudanar, ta gano cewa tuni wasu manoman sun riga sun  fara cin gajiyar shirin Gwamnatin Jihar Kaduna na basu rangwamen tallafin takin zamani. A bangare daya kuma, wasu har yanzu jin sunan shirin kawai suke yi a gidajen rediyo, amma har basu tabbatar da ingancin shirin ba.

Wasu manoma da wakilinmu ya zanta da su sun bayyana ra’ayoyinsu mabanbanta kan lamarin.

Alhaji Abubakar Tsoho Abdullahi, wani manomi da ke zaune a Kaduna, ya bayyana wa wakilinmu cewa, “ Eh gaskiya muna sane da wani shiri da Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin shirin Gwamnatin Tarraya na samar wa manoma da  takin zamani cikin rahusa bai daya.”

Ya ci gaba da bayyana cewa, “Gwamnatin Tarayya ta kaiyade kudin taki akan Naira dubu 5,500 akan ko wane buhun NPK, domin saukaka ma manoma. Amma wani abin haushi shi ne ba ko ina zaka iya zuwa ka sami wannan taki akan kayyadaden kudi, kamar yadda Gwamnatin ta shardanta tun da farko ba, domin har yanzu akwai sauran rina a kaba, amma duk da haka ni dai na ci moriyar wannan shiri, kuma muna godiya mai yawa wa gwamnati akan wannan kokari da ta yi.”

A bangare daya kuma ba haka labarin yake ba, domin wakilinmu ya zanta da wani manomi mai suna Malam Hassan Bala, wanda ke zaune a Hayin Na Iya a Unguwar Rafin Guza a Garin Kaduna. Ga kuma abin da ya shaida ma wakilinmu. “Maganar cewa wai mu manoma gwamnati na tallafa mana da takin zamani, wannan maganar banza ce, domin a maganar nan da muke yi da kai, yanzu haka a wannan daminar sai da na cire kudi daga aljihu na domin sayan takin zamani a kalla buhu 25 domin yin amfani da shi a gona ta.”

“Kuma duk wuraren da gwamnati ta ce wai ta kai takin zamani domin manoma muje mu siya, mun je karya suke yi babu wani takin sayarwa a wajen. Kawai dai har yanzu abin da bahaushe ne ke cewa wai an kyale ganga ana bugun taiki, har yanzu maganar raba taki ga manoma, gwamma jiya da yau, domin babu wani banbanci tsakanin gwamnatin da ta gabata da kuma wannan gwamnati, domin duk kanwar ja ce, duk tsiyar na nan a gidin ‘yan siyasa wanda su ne ummul aba’isin koma bayan duk wata gwamnati.”

Malam Hassan Bala, ya kara da bayyana cewa, “ Ina kalubalantar Gwamnatin jihar Kaduna, da su fito su bayyana mana wuraren da suka ce sun kai takin zamani domin manoma su je su siya, domin babu in da ba mu karade ba domin ganin mun sami takin, amma hakanmu ba ta cinma ruwa ba. Wallahi karya ce tsagwaronta irin na ‘yan siyasa.” A cewarsa.

Shi kuma wani matashin manomi daga kudancin Jihar Kaduna, mai suna Kwamared Adamu Barde Kagarko, ya bayyana irin nasa ra’ayin a kan cewa, tun da aka kafa kasar nan manoma basu taba cin gajiyar aikin noma kamar a wannan gwamnati ba, domin a cewar sa, saboda albarkar amfanin noman da suka samu a bana, ya nuna kusan kashi 80 na ‘yan Jihar Kaduna da za su tafi Aikin Hajji duk yawancin su manoma ne, wanda suka sami ribar amfanin gona irin wanda basu taba samu ba a tarihi ba.

Kwamared Adamu Barde ya kara da cewa, “Mu a kudancin Kaduna Allah ya albarkace mu da noman citta da dankalin turawa, kuma ina so na tabbatar maka da cewa, tun da muke noma a yankin kudancin Kaduna, ba mu taba noma citta da dankalin turawa mai yawa irin na wannan karo ba, kuma duk hakan ta  samu ne a dalilin kyakkyawan tsarin da gwamnati ta fito da shi, wanda hakan ya zama dole mu yaba mata a kan hakan”.

Kwamared Adamu Barde Kagarko ya roki gwamnati da ta inganta shirinta na samar da maganin feshi domin rage annobar kwari, domin a cewar sa, babban matsalar da suke fuskanta na koma baya bai wuce annobar kwari ba.

Idan ba a manta ba, a makwanni biyun da suka gabata, LEADERSHIP Hausa ta ba da rahoton bullar wasu tsutsotsi masu cinye amfanin gona musamman masara a Garin Jere da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a yankin Karamar Hukumar Kagarko, inda suka tasan ma mayar da gonakai kamar kufayi a yankin.

Shi kuwa da yake karin haske kan shirin da Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi wa daminar bana, Kwamishinan Aikin Gona na jihar, Farfesa Kabir Mato, ya bayyana cewa, babu hannun gwamnati a harkar shigowa da takin zamani, domin a cewar sa, gudummuwar gwamnati ita ce samar da wurare a kowa ne yanki domin  yin ajiyar takin zamani saboda saukake ma manoma wajen zuwa su siya.

Farfesa Kabir Mato ya kara da bayyana cewa, babu hannun gwamnati wajen sayar da taki, “domin a wannan karo tun daga matakin Gwamnatin Tarayya har zuwa na Jiha da Kananan hukumomi, an kayyade kudaden taki iri bai daya, babu wanda ya isa ya kara daidai da Naira daya a kan farashin da gwamnati ta kayyade”, in ji shi.

 

 • Neja

Ganin yadda Gwamnatin Tarayya ta mayar da hankali kan farfado da noma da kiwo a kasar nan a matsayin wata hanya ta bunkasa tattalin arziki, ita ma Gwamnatin Jihar Neja ba ta yi kasa-a-gwiwa ba wajen bin sawuta.

Kan haka, a kwanakin baya Gwamnan Jihar, Alhaji Sadik Sani Bello ya kaddamar da sayar da takin zamani a mafi saukin farashi.

LEADERSHIP Hausa ta zanta da kananan manoma kan yadda suke kallon tsarin da gwamnatin ta bullo da shi kan inganta noma da kiwo.

Malam Muhammadu Jibo wani manomi daga Karamar Hukumar Bosso ta Jihar Neja, ya ce “lallai gwamnatin ta nuna da gaske ta ke, domin manomi abu biyu yake bukata, kasar noma da kayan aiki. A shekarar da ta gabata muna sayen takin zamani a kan Naira 10,000 zuwa 12,000  kuma ga wanda ya samu halin ganin takin ke nan, shi ya sa ko abincin da aka noma a shekarar da ta gabata ya yi tsada a kasuwa, an yi noman sosai kuma an samu alheri amma matsalar takin zamani shi ya tursasa amfanin gonar ba a ci moriyarsu yadda ya kamata ba. To a wannan shekarar maigirma Gwamna ya kaddamar da sayar da takin zamani a mafi karanci kudi, yanzu muna sayen taki a kan Naira 5,500 kuma duk inda ka tsinka za ka iya samunsa, ka ga a nan an fara kama hanya ke nan. Yanzu babban matsalar da muke samu bai wuce na iri ba, domin a baya ana kawo mana iraruwa wadanda aka gauraya su da maganin kwari yanzu kuma babu, dan haka a cikin kokarin ita Gwamnati na farfado da harkar noma ya kamata a dawo mana da shirin nan na samar da iri wanda ya dace wanda kuma zai zama yana da garkuwa daga kwari da duk wani abu da zai zama barazana ga irin.

“Ka ga mu a Jihar Neja muna da yalwar daji ta yadda za mu iya fadada gonakinmu amma dole sai an kara saukakawa, dan haka kamar yadda aka samar mana da takin zamani akwai bukatar samar mana da iraruwa masu garkuwa da barazanar kwari da kuma tsutsotsi. Maganar kuma barazanar da shuka ke fuskanta a kan kwarin da ke cinye kananan shuka, mu dai a nan muna da sauki sosai, domin kafin huda muna yin feshi kuma bayan hudar ma muna yin feshin kwari, to hakan sai ya zame mana garkuwa ga kananan shukarmu daga kwarin da ke zama barazana ga anfanin gona, amma dai na ji a wasu sassan jihar ma sun dan samu irin wannan damuwar amma dai nan yankin Maikunkele zuwa makota abin da sauki sosai.

Dangane da batun kasuwancin anfanin gonan kuwa, manomin ya ce akwai wadanda suke zama kafar ungulu.

“Maganar samar da wani tsari na sayar da anfani gona a nan jihar dai babu shi, domin ‘yan soke ko in ce ‘yan sari suke lalata darajar anfanin gona a kasuwanni, wanda a karshe ma mu al’ummar jiha ba ma anfana da noman da muke yi. Domin sukan shigo kasuwanni su sai abinci da sauki sai su boye ko suyi gaba da shi, kuma su din ne ke dawo da shi kasuwa idan ya tsunke suna sayarwa yadda suka ga dama, ka ga hakan bai dace ba, domin mai wahalar daban mai cin anfanin abin daban.

“Ina ga ita Gwamnatin Jiha bisa jagorancin Alhaji Abubakar Sadik Sani Bello ya kamata su samar mana da kamfanonin da za su rika sayen abinci da daraja ta yadda karamin manomi zai iya anfana da wahalarsa, amma idan aka bar abin ya wuce haka zai zama ba a cinma nasarar da ake so. Irin wannan matsalar ma makiyaya ke huskanta wanda shi ya janyo da daman makiyaya yau suke watsi da yin kiwon”, in ji shi.

Hon. Usman Musa Kasuwan Garba da ke Karamar Hukumar Mariga ya bayyana cewa an samu canji wajen ci gaban aikin gona a jihar idan aka kwatanta da shekarar bara.

“Akwai canji sosai, domin a shekarar da ta gabata muna sayen takin zamani a kan Naira 10,000 zuwa 11,000 a lokacin masara ya kai 14,000 buhu ke nan, tau ka ga ba a fadi ba amma babban matsalar harkar noma ya fara komawa na zamani feshin magani kuma har yanzu a kasar nan sai an kawo mana maganin feshi irin su garmazon da sauran su. Ya kamata yadda Gwamnatin Tarayya ta hada kai da kasar Maroko aka fara yin takin zamani a Nijeriya; yau duk inda ka je a kasar nan takin bai wuce Naira 5,000 ba, ya kamata shi ma maganin feshin shuka a yi mai irin wannan gatar.

“Maganar gaskiya a shekarun baya mun wahala sosai da harkar noma, domin a lokacin muna sayen taki dubu bakwai zuwa takwas kuma buhun masara bai wuce dubu uku zuwa dubu hudu amma ka ga a bana an sayar da masara dubu goma sha hudu idan ka kwatanta koda ka saye taki akan dubu goma sha ne ba faduwa sosai, amma wannan shiri na Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jiha ta assasa mun yaba da shi, sai kamar yadda na fadi ne a baya ya kamata yadda aka samar da kamfanin takin zamani a kasar nan wanda hadin gwiwa ne da gwamnatin Moroko, a samar da wani kamfani da zai rika samar mana da maganin kwari wanda mukan yi amfani da shi kafin shuka da bayan shuka, lallai shi ma wani kadarko ne mai zaman kan shi a cigaban harkar noma”.

Hon. Usaman ya kuma yi kiran samar da wani tsari da zai hana ‘yan kasuwan bayan fage cin karensu ba babbaka, inda ya kara da cewa “maganar ‘yan kasuwan hatsi na bayan fage, muna bukatar sauyi kam, domin ‘yan na kama suna hana wa manoma cin anfani kayan nomansu da masu saye suna boyewa sai ya yi tsada su sayar. Lallai da bukatar Gwamnatin Jiha ko ita kanta ko kuma ta samu kamfanonin da za su rika sayen kayan anfanin gonar da daraja. Ko Gwamnatin da ta gabata ta Jonathan ta yi kokari wajen ba da taki ta hanyar waya, amma duk da hakan wadanda aka dorawa alhakin hakan sun yi abin da suka ga dama. Mu yanzu babban matsalar dai biyu ne da farko, maganar maganin feshi da ‘yan na kama-na-kama wato ‘yan baranda, amma yanzu tunda dimokuradiyya ake yi idan ka yi wani motsi a gwamnatance sai a ce ana neman abinci ne, ya kamata mu ma mu ji tsoron Allah, bai yiwuwa mutum ya dauki lokaci a duke yana wahala sai ya kawo kasuwa a karyar mai da shi, ya kamata ne a bar mutum idan ya kawo anfanin gonarsa a kasuwa ya sayar da kayan shi yadda ya gamsu. Sannan maganin feshin ma gwamnati na da rawar takawa wajen samar da shi da tsayar da ingantaccen farashi”.

A nashi bangaren, Malam Garba Umaru wani manomi a Karamar Hukumar Chanchaga, ya bayyana wa wakilinmu cewa, “maganar gaskiya gwamnati na haka rami ne ana mayar ma ta da kasa, ba wai Gwamnatin Muhammadu Buhari ba, gwamnatocin da suka gabace shi tun daga kan Janar Babangida har zuwan su Obasanjo da Jonathan ma da ba wani abin kirki ake nomawa a wajensu ba face ayaba da wasu abubuwan haka, ya taka rawar gani sosai a harkar noma idan aka yi la’akari da irin kudaden da ya fitar dan aikin noma.

“Wato kasar akwai kirkira amma ba a iya gabatarwa, in ma an gabatar to ba zai dore ba, misali a bara ma’aikatar aikin gona ta zo mana da shiri na noman waken suya, bayan mun cika ka’idar da suka zo da shi ba a ba mu iri da taki akan lokaci ba sai cikin watan Agustan shekarar kuma ana neman mu noma buhu biyu a kowani kadada, bayan mun kammala kudin da aka ce za a bayar na aikin ma ba a cika ba kuma bayan sun ce su ne za su sayi anfanin gonar tunda muka kai masu waken suyan da muka noma yau watanni hudu ke nan ba a ce mana komai ba balle mu ji karfin cigaba da noman kamar yadda gwamnatin ta ke bukata.

“Ka ga ke nan kamar ni ba yadda zan noma abu a ce gwamnati na bukata in tsaya jiran ta, idan ma gwamnatin ba ta san me ke faruwa ba ne ta sani tana turbe ne ana mayar mata da kasa baya, ya zama dole maigirma shugaban kasa da gwamnonin jihohi in har da gaske suke a yi tsayin daka kamar yadda aka yi wa boko haram, wadannan na gaba wasu kuma na baya inda aka tsinbere sai na baya su gyara, domin maganar gaskiya ‘yan bokon mu na Arewa kuma ma’aiktan gwamnatin mu ba yadda za su bari a cigaba domin duk wata kunbiya-kunbiya su ke aiwatar da shi.

“Saboda haka maganar aikin noma sai mun yi kamar yadda kasar Barazil ta yi, ya zama gwamnati ta shigo sosai da sosai dan ganin an kauda jama’a daga zaman kashe wando, ina da tabbaci nan da shekaru uku zuwa hudu in dai gwamnati ta mayar da hankali da gaske sai dai mu rika daukar abinci zuwa waje ba wai a shigo mana da abinci a kasar nan ba.

“Yanzu yadda maigirma shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya dage a kan maganar taki da sauran bangarorin ma za a sanya musu ido ina da tabbacin lallai gwamnati za ta cimma muradunta, amma babban matsalar ita ce duk abin da aka faro ba a mayar da hankali a kan shi, abin da ya faru a kan mu a shekarar da ya gabata ya isa ya zama madogara a wajen mu. Saboda mu ya faru da mu kuma za mu iya ba da shaidar abinda ya faru din, yanzu masu noman waken suya aka yiwa wannan, masu noma sauran bangarori ma yana iya faruwa da su, domin an ba mu taki da iri mun noma bayan mun noma mun kai ba a mayar mana da kudaden mu ba.

“Shawarar da na ke son baiwa wadanda wannan alhaki ya rataya a kansu, in dai ga gaske kamar yadda na fahimci shugaban kasa yana son yi, to a kowace karamar hukuma an san manoma na kowani bangaren abinci, a zauna da su a saurari matsalolinsu kuma a magance shi nan ta ke ba tare da jan kafa ba, sannan ‘yan uwanmu na karkara ba mu ce dole a yi masu hanya a zuba kwalta ba, a dai tabbatar an samar da hanyoyin da abubuwa za su rika isa gare su cikin sauki.

“Kamar yadda na fahimta, duniyar ma kakar man fetur ya zo karshe, kowa na kokarin bullo da wani abu da zai iya maye gurbin man fetur din nan ne, mu kuma tun farko ma noman ne ya samar da man fetur kuma aka yi watsi da shi, to tunda yanzu an farga kuma ana son a dawo mai tau kar a yi fargan jaji a tabbatar an dawo kan harkar noma da dukkan kafa biyu, domin shi ne hanya daya tilo da zai iya kawo karshen zaman kashe wando tare da samar da aiki ga dubban ‘yan kasa masu aikin da marasa aikin, ba a iya rayuwa ba tare da abinci ba, in ko haka ne lallai a lalubo kowace irin hanya ce da zai iya dawo da martaban noma a kasar nan”, kamar yadda ya bayyana.

 

 • Zamfara

Da yake Allah ya albarkaci Jihar Zamfara da kasar noma, noman ya kasance abin tunkahon tattalin arzikin al’ummar jihar da kashi 90 bisa 100.

Wannan ne ya sa Gwamnatin mai ciyanzu ta dau alkawarin saida wa manoma takin zamnai a kan farashin Naira 1000 kudin kowa ne buhu a zangon farko na Gwamnatin Abdul’Aziz Yari. Amma a wannan zangon kuwa sai al’amarin ya canza.

Yanzu haka wasu manoma sun yi nisa da shuka, wasu ma na gab da fara noman farko.

Wani manomi daga Jangemi cikin yankin Dansadau, Malam Maharaji Altine ya bayyana cewa har yanzu ba su ga wani tallafi ba daga bangaren gwamnati.

“Ba Gwamnatin Zamfara ba; a bara koda daga Gwamnatin Tarayya da ita Gwamnatin Jihar babu wani tallafin da manoma suka samu a cikin wannan jiha ta mu. Duk da cewa Gwamnatocin nan biyu na Jiha da Tarayya ba za su bada tallafi ba sai an yi kungiya kuma mu manoma mun saida abincin mu mun yi kungiyar babu wani tallafin da mu ka samu. Babu kudin Rijistar kungiya, babu tallafi ka ga wannan yaudara ne. Kuma a lokacin Kamfen Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce za ta saida taki kan Naira dubu Daya amma sau daya ta saida akan wannan farashin. Kuma a bara ma babu wani tallafin taki ko na iri, maganin haki da kwari da gwamnatin jiha ta bamu. Kuma bana ma muna jin ana raderadin cewa wai Gwamnati ta kawo taki kuma za ta saida shi akan Naira dubu shida na Gwamnatin Tarayya ne Naira dubu biyar da dari biyar. Idan gwamnatin da talaka ya zabe ta ta yi masa haka lallai bata yi mata adalci ba. Dan wannan noman da shi ne talaka ya dogara kuma idan al’umma su ka samu wadatacan abincin arzikin garin da jihar da kasa zai wadata, idan kuma aka samu akasin haka wallahi akwai matsala.

“Dan haka nake kira ga Gwamnatin Jihar Zamfara da ta fid da san rai wajen bunkasa noma dan shi ne tinkahon al’umarta kuma shi ne ginshikin samun dawamamen zamnan lafiya da dorewar arzikinta”, kamar yadda ya bayyana.

Daga bangaren Gwamnatin Jihar Zamfara kuwa, Kwamishinan Gona Injiniya Lawal Jibril Jangebe ya bayyana wa wakilinmu cewa shirye-shiryenta na bunkasa noma sun yi nisa.

Ya ce, “Gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Aldul’aziz Yari Abubakar ta kamala shirinta na bunkasa Noma a fadin jiha. Da farko akwai Hukumar Raya Karkara Noma da Ruwan Sha watau (IFAT0) ita wannan hukumar hadin gwiwa ne tsakanin Gwamnatin Tarayya da jihohi da kuma Bankin Duniya wanda kowace jiha ta ke ba da kasonta dan samun tallafi daga Gwamnatin Tarayyar da Bankin Duniya kuma tuni Jihar Zamfara ta bada nata kason. Kuma an ba da tallafin a wannan jihar ta hanyar kungiyoyi na manoma. An basu taki da iri da maganin kwari da dai sauransu a kan farashi mai rangwame.

“Kuma akwai wani shiri shi ma na Noman Fadama Kashi na Uku wanda shima tuni hukumar wannan shiri ta kammala shirye-shiryenta dan ba da tallafi a wannan jihar ga wadanda suka cancanta.

“Batun noman damina ta bana yanzu haka runbun Jihar Zamfara cike suke da takin zamani dan saida wa al’umma cikin farashin mai sauki kuma ina mai sheda maka cewa wasu jihohin na saida takin sama da Naira dubu biyar, wasu ma shida amma mu a wannan jihar ta Zamfara ba zai wuce Naira dubu uku ba. Nan ba da jimawa ba Gwamna Abdul’Aziz Yari zai kaddamar da saida shi.

“Kuma ina mai sheda wa al’ummar Jihar Zamfara cewa shirin gwamnati na bunkasa harkar noma a wannan jihar gwamnatin ta yunkoro sosai, kan haka nake kira ga al’umma da su ci gaba da yi mata addu’a dan ganin shirin ya samu nasara”, a cewar Kwamishinan.

 

 • Kano

Jihar Kano na cikin jihohin da Allah ya hore wa kasar noma, wanda duk wani iri da aka shuka kasar na karbarsa. Hakan ta sa Jihar Kano shahara ta fuskar noma musamman Gyada, auduga da sauran kayan cimaka.

Duk shekara Gwamnatoci kan shelanta aniyarsu ta inganta harkar noma, a wasu lokutan sai ka ji shiru kamar an shuka dusa. Tun shigowar Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje an ji irin hobbasar da take yi na ganin an habaka harkar noma domin ciyar da jihar gaba. Ko a shekarar data gabata hukomomi a Jihar Kano sun tabbatarwa da Duniya cewa an samu karin albarkar noman shinkafa inda a kakar girbin shinkafar da ta gabata ta shekara ta 2016, an samu tan Miliyon 17.7, wanda ya zarta abin da aka girba a shekarar 2015 inda aka samu tan Miliyon 9.

Domin jin tanadin da Gwamnatin Kano ta yi wa harkar noma a wannan shekarar, LEADERSHIP Hausa ta zanta da Kwamishinan Harkokin Noman Jihar, Dakta Nasiru Yusif Gawuna, wanda ya bayyanawa wakilinmu cewar ba a taba samun yanayin noma mai kyau irin wannan shekarar ba. A cewarsa, Gwamnatin Gaduje ta zuba makudan kudade a harka noma wanda ya sa yanzu manoma a Kano ke murmushi, wannan ya biyo bayan shiga tsakani da Gwamna Ganduje ya yi.

Gawuna ya ci gaba da cewar Gwamnatin Ganduje ce kadai ta rungumi ba da lamuni mai rangwamen kudin ruwa wanda ya kai na Naira Biliyon guda wanda aka ba kungiyar manoman shinkafa. Hakan ya haifarwa Jihar Kano da mai ido inda aka yiwa harkar noman shinkafa garambawul.

Wasu manoman da wakilinmu ya zanta da su, sun bayyana cewa idan har abin da Gwamnan Kano Ganduje ya ambata za a aiwatar dashi, ko shakka babu za a samu ci gaba a harkar noma. Sai dai kuma sun nunar da cewa babbar matsalar manoma ita ce rashin samun taki da wuri kuma ga bakar tsada da takin ke zuwa hannun manona a kansa. Suka ce idan ana bukatar cika wancan buri na ciyar da kasa abinci, ya zama dole gwamnatoci su samar da tallafin takin zamani, iri da magungunan kwari. Amma sai ga shi a wasu wuraren an fara girbin shinkafa amma har lokacin taki bai isa ga manoman gaske ba.

Shi ma Alhaji Ubale Tanimu wanda aka fi sani da Sarkin Noma ya ce, “muna fatan kar a sa ke fadawa irin halin da manoma suka fada bara, domin kuwa saboda matsin rayuwa har gonakanmu ake bin mu da kudi a buhu a saye amfanin gonar da muka noma, saboda tsananin wahala ko wanda za mu tanada domin noman badi da yawa wasu basu yi tanadinsa ba. Sannan kuma wanda aka samu kaiwa kasuwanni musamman a Kasuwa Abinci ta Dawanau, akwai attajirai daga makwabtan kasarnan da suke wasoson saye abincin ana ficewa da shi kasashen waje. Wannan shi ya haifar da karancin abincin da har yanzu mai karamin karfi ke fuskanta.

A nasa bangaren, Shugaban Kungiyar Manoma ta Kasa, reshen Jihar Kano (AFAN) Alhaji Faruk Rabiu Mudi ya tabbatar da irin kokarin da Gwamnatin Jihar Kano ta yi ta hannun Mai’aikatar Gona cewa Gwamnatin Kano ta tsaya tsayin daka wajen samar da bashi da tallafi ga manoma kamar yadda jawabi ya gabata a baya. Mudi, wanda har ila yau shi ne shugaban kungiyar masu noman alkama ya ce a shekarar da ta gabata (2016), an samu tan na alkama sama da dubu 20, ya yin da a wannan shekara ta 2017 ya kiyasta cewa akalla su manoman alkama sun samu sama da ton dubu 100 na alkama, wanda ya nuna kwalliya na biyan kudin sabulu a bangaren bunkasa harkar noma a Jihar Kano, duk da sa-toka-sa-katsi da aka samu tsakanin manoma da hukumomin ba da lamunin noma na cewa an basu abubuwa a makare.

A cewarsa, “idan za a bada bashi a bayar da wuri, manomin da ya ga an makara kada ya karba don kaucewa matsala, wanda kuma ya ga alokacin ba a makara ba sai ya karba, amma ci gaba shi ne a dawo dashi da wuri, idan har Jihar Anambara za ta iya maido da bashin da ta karba akan lokaci, babu dalilin da zai hana Kano dawo da nata, wannan zai iya zama babbar illa ga ‘ya’ya da jikokinmu nan gaba.

“Hana shigo da abinci da aka yi hakan ya bunkasa tattalin arzikin kasa da manoma, inda gonaki da dazuzzuka suka zama wuraren bubbugo da kudade sabanin a baya da ake tafiya Abuja neman kudi. Kasancewar mu a nan AFAN mutanen da suka yi rijistar noma a ‘yankin Karamar Hukumar Warawa kawai ‘yan asalin Warawa basu wuce 120 ba, amma ‘Yan birni ‘yan kwalisa sai da mutum sama da 1,800 suka yi rijistar komawa gona wanda a baya basa yi, kaga rufe iyakoki ya samar da  ayyukan yi ga matasa. Kuma abin da muke fata jama’a su fahimta ana kara yawan noma abinci na kara saukowa da haka har mu iya rike kanmu”, in ji shugaban na AFAN

 

 • Bauchi

A Jihar Bauchi dai za a iya cewa manoma sun kasu kashi uku, a yayin da wasu manoman suka kammala sharan gonakansu da shirin fara kai taki gona, haka kuma da kokarin tayar da haro ko kunyayyakin noma, wasu manoman kuwa suna kan sharan filin noma a halin yanzu musaman manoman kudancin jihar, a yayin da kashi na ukun kuma suka fara yin shukan amfanin gonarsu.

A bisa haka ne LEADERSHIP Hausa ta tuntubi masu ruwa da tsaki a harkar noman don jin yadda aka kwana. Pharmacies Sama’ila Adamu Burga daya daga cikin manyan manoman Jihar Bauchi wadanda suke ribantar amfanin gona a duk shekara, yakan samu sama da buhu dubu 10 a duk shekara, ya yi mana bayanin halin da harkar noma ke ciki a jihar Bauchi, inda ya fara da cewa “yanzu haka manoma a Bauchi mun kammala sharan gona, sai kaftu, haro da kuma yin kunyayyaki da kuma yin shuka. Sabili da masana harkokin ruwa sun nuna cewar daga sassa daban-daban na Jihar Bauchi shuka ya fara ne tun daga ranar 8 ga Mayu, yanzu haka a kan hakan muke. kuma samun ruwan sama sai mu ce Alhamdullah.”

Da yake magana kan taki kuma, manomin ya bayyana dan sarkakiya a cikin lamarin, “a kamfanoni an ce za a bayar da takin nan akan kudi Naira dubu biyar-biyar, a jikin takin kuma an rubuta cewar kada a sayar da takin nan ya haura dubu da dari biyar. Misali yanzu dila zai dauko taki daga Kaduna zuwa Jalingo-Taraba. Daga nan kuma sai a ce za a kai sa Manbila, anya takin nan zai kai wajen a kan Naira dubu 5 da dari 5? Don haka akwai wannan matsalar a kasa. Idan ka tafi kasuwa neman taki ba za a ce maka babu ba; ba kuma za ka samu kwantitin da kake nema ba, tun da gwamnati ba ta fito karara ta nuna sito-sito da aka kai kaya kamar yanda aka saba kaiwa ba balle manoma su je su fara neman wannan takin”. A cewar manomin

Da yake mana karin bayani kan matsalolin da manoma suke fuskanta a daidai wannan lokacin, Burga ya bayyana cewar “Muna cikin matsalolin rashin taraktoci da za a yi aikin noman da su a mafiya yawan wuraren noma. Babbar matsalar da take jawo mana koma baya a harkar noma shi ne matsalar talauci, kuma wannan matsalar tana matukar dakusar da shirin nan na a koma gona domin sai da wadata ake noma, maganar gaskiya kenan, da mutum ya je ya nemo dubu daya da ya sanya a gona gara ya sayi abinci a gida. A kasashen da suka ci gaba babu kasar da ba ta bayar da tallafin gona wa manoma amma ban da mu, Gwamnatocinmu sun gaza kan hakan. Don haka muna amfani da wannan damar wajen yin kira ga gwamnatoci da suke karfafa wa manoma guiwa ta fuskacin basu tallafi da kuma sayen amfanin cikin daraja mai ma’ana domin karya farashinsa wa kasuwa”. In ji shi.

Abubakar Ja’afaru Ilelah, Dakratan fadakarwa da yada labarai na Hukumar Bunkasa Aikin Noma ta Jihar Bauchi, ya yi karin bayani kan yanda manoman ya kamata su yi a daidai wannan lokacin, ya bayyana cewar babban abin da manoma suke da bukata a kowani lokaci shi ne neman shawarorin masana noman daga wajen malaman gona da turawan gona don bin matakan da suka kamata.

“Daminar da ake yi a shekarun baya ba irinsa ba ne ake yi a irin wannan lokacin, don haka idan manoma basu neman shawarwarin malaman gona da turawan gona hatta irin da mutum zai shuka dole ne sai ka nemi shawarar masana matukar kana son samun nasara a ribar nomarka. Daminar bana irin ta bara ce, don haka za mu daura ma’auninmu kan na bara”.

Ya gargadi manoma da kada su yi amfani da dogon iri mai daukan nisan zango a irin wannan lokacin domin a cewarsa hasashen da masana suka yi ya nuna irin noma mai amfani da karin zango ake neman yin amfani da shi “A irin wannan daminar idan ta kubuce wa manomi bai shuka iri mai yado ba, to mafi a’ala shi ne ya nemi irin taki mai tsuguno, tun da shi ma yana yi da kuri koda kuwa ya yi latti na shuka, kwanakin da aka yi wannan waken sai ka ga sun wadaci nomarka”.

Masanin ya ce idan manomi ya nemi irin da zai dauki watanni alhali yanayin da ruwan lokacin ya nuna ba irin wannan irin ke bukata ba; ya nuna hakan a matsayin abun da bai kamata ba, a bisa haka ya ce dole ne manoma su neman shawarwarin da suka dace.

 

 • Jigawa

A Jihar Jigawa, tun bayan darewar Gwamnan jihar, Alhaji Muhammad Abubakar Badaru kan karagar mulki ya lashi takobin sauya akalar tattalin arzikin jihar daga dogaro da manfetur zuwa dogaro da kai ta hanyar bunkasa fannin noma tare da samar wa matasan jihar ayyukan yi a wannan fanni.

Wannan dalili ya sanya Gwamnan ware wani kaso mai tsoka har kimanin Naira bilyan 6.15 cikin kasafin kudin wannan shekara ta 2017 domin bunkasa noman rani da na daminar wannan shekara.

Haka kuma Gwamnan a lokacin da yake bayaninsa yayin wata ziyarar gonaki a garin Kafin Hausa ya ce, bisa tallafin da Gwamnati za ta baiwa manoma a jihar akwai kyakkyawan zaton manoman jihar za su samar da da shinkafa wadda yawanta ya haura tan milyan 1.5 a wannan shekara.

Sannan shi ma da yake karin bayani ga manema labarai, babban sakataren Ma’aikatar Noma ta Jihar Jigawa, Alhaji Gambo Ibrahim Aliyu ya ce a wannan damina Gwamnatin jihar ta yi shiri na musamman wadda tuni aka fara baiwa manoma horo na musamman karkashin shirin nan na noman rukuni-rukuni.

 

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI