Connect with us

BURIN ZUCIYA

BURIN ZUCIYA: Gishirin Ma’aurata: Shawarwari 60 Ga Mata Don Inganta Zaman Aure

Published

on


Daga Abban Umma

Wadannan shawarwari 60 ga matan aure domin samun zamantakewa mai inganci, da aure mai albarka. An dai san cewa mace ita ce ginshikin aure, ita ce ke iya tattalin gidanta har mijinta da sauran iyalin gidan za su sami kwanciyar hankali. Muddin kuma aka sami akasi har mace ta yi sake ba ta iya tattalin gidanta yadda ya dace ba, hakika za ta rasa gano kan yadda rayuwar aurenta za ta kasance. Ba don komai ba, sai domin gidan baki daya zai rasa alkibla sahihiya.

Ga shawarwarin kamar yadda wani manazarshi ya fito da shi, ya aiko mani, ni kuma nake son ‘yan’uwana mata su amfana da su. Ga su nan kamar haka:

 1. Abu na farko da ya kamata mace ta yi a daidai wannan tsarin shi ne, ta rike wa mijinta amana.
 2. Ta yi masa biyayya a kan duk abin da ba sabon Allah ba ne.
 3. Ta kula da dukiyarsa
 4. Ta kula da Sallah a kan lokaci. Da addu’ar zaman lafiya a kullum ta yi Sallah.
 5. Ta girmama shi a gaban idonsa.
 6. Ta kare girma da matsayinsa a bayan idonsa.
 7. Ta so abin da yake so,  ko da ba abin so ba ne a wajenta ba.
 8. Ta ki abin da yake ki, ko da ba abin ki ba ne a wajenta.
 9. Ta damu da duk abin da ya damu da shi.
 10. Ta kau da kai daga duk abin da mijinta ya kauda kai daga gare shi, muddin bai saba Shari’ah ba, ko da tana matukar kaunar abin.
 11. Ta yi fushi, da dukkan abin da ya yi fushi da shi don Allah.

12.Ta yarda da duk abin da ya yarda da shi, don Allah.

13.Idan ya ba ta kadan, ta ga yawansa

14.Idan ya ba ta da yawa ,ta yi godiya ga Allah, sannan ta yi masa fatan alheri.

15.Ta farka daga bacci kafin ya farka

 1. Sai ya yi bacci kafin ta yi

17.Ta yi hakuri idan ya yi fushi

18 Ta yi taushi idan ya yi tsauri

19.Ta lallashe shi idan ya hasala

 1. Kada ta nuna raki a gabansa
 2. Kada ta yi kuka alhali yana dariya
 3. Kada tayi dariya alhali yana kuka
 4. Kada ta tsaya kai da fata sai ya yi mata wani abu
 5. Kada ta matsa masa da bukatu
 6. Kada ta rika ganinsa kamar yaron gida
 7. Kada ta rika yi masa gyara barkatai, ba tare da basira ba.
 8. Kada ta rika kushe tsarinsa, ko da baya kan tsari mai kyau. Sai ta yi amfani da hikima ta gyara masa.
 9. Ta rika zuga shi a gaban danginta
 10. Ta rika girmama shi a wajen kawayenta
 11. Ta rika nuna masa abu mai kyau
 12. Ta rika boye abu mummuna
 13. Idan ya kawo wata damuwa gare ta, ta taimake shi ta yadda za ta iya, don ya samu ya warware matsalar.
 14. Idan ya nuna ba ya son wani abu, to ta gaggauta dainawa.
 15. Ta kwantar masa da hankali a lokacin damuwa.
 16. Ta sassauta masa idan yana cikin bakin ciki.
 17. Ta tsaya da jinyarsa idan yana rashin lafiya.
 18. Ta taimake shi lokacin da yake neman taimako.
 19. Idan yana cikin kunci ta sassauta bukatunta, sannan ta kame kai daga hangen na hannun wasu.
 20. Ta yi masa rakiya lokacin fitarsa, ta tare shi a lokacin da ya dawo.
 21. Ta tausasa harshe a lokacin da take magana da shi.
 22. Ta zama mai tsaftar gida iya iyawarta.
 23. Ta tsara dakinta sosai yadda zai birge mijinta.
 24. Ta yi masa bankwana a lokacin balaguro.
 25. Ta yi ado karshen lamba a duk lokacin da ta san yana nan, ko ma ba ya nan.
 26. Ta rika bayyana halaye masu kyau ga mijinta.
 27. Ishara ta ishi mai hankali da ta kula da tattalin gidanta a koda yaushe.
 28. Ta bayyana kanta a matsayin mace
 29. Ta iya murmushi da lafazi mai kwantar da rai
 30. Ta cika zuciyarsa da sonta da kwalliyarta
 31. Ta yi kokarin jan hankalinsa da abin da yake so.
 32. Ta mayar masa da kyakkyawa idan yay i mata mummuna.
 33. Ta yafe masa idan ya munana mata.
 34. Ta karbi uzurinsa, ko da sau dari ne a duk rana ta Allah.
 35. Kada ta yi sallar Nafila sai ta sanar masa.
 36. Kada ta dau azumi sai ya sani.
 37. Kada ta fita daga gida sai ya sani.
 38. Ta iya girki kala-kala don mayar da yawu.
 39. Kazantar jiki ta dade tana kashe aure, don haka tilas ta girmi wannan.
 40. Kada ta shigar da wani cikin lamarinsu, sai bukatar hakan ta taso.
 41. Kada ta nemi saki ko rabuwa haka kawai, sai da hakkin Allah.

 

Allah ya zaunar da mu lafiya da iyalanmu baki  daya, amin summa amin. Ina yi wa masu karatu fatan alheri, musamman mata da wannan shawarwarin ya fi shafa, ya kamata a karanta, a aiko mana sharhinsu. Shin kin yarda da wadannan shawarwari? Kina ganin akwai abin da ba za ki iya yi ba? Idan akwai wani tsauri a ciki, ki aiko mana a rubuce ta hanyar ‘TES,’ amma ba kira ba don Allah.

Za mu ci gaba da tattaro ra’ayoyinku masu karatu, Allah Ya sa mu dace.

Abban Umma (B/014/Z/KAD). 08033225331.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI