Connect with us

KIWON LAFIYA

KIWON LAFIYA: Inshorar Lafiya Hanya Ce Mafi Sauki Don Samar Da Kiwon Lafiya

Published

on


Ranar 12 ga watan Disamba ce aka ware don shirin karade Afirka da kiwon lafiya a karon farko a Afirka. Wannan ya nuna cewa tun da aka ware wata rana ta musamman don wannan shiri a duniya an sami ci gaba don cimma burin karade Afirka da kiwon lafiyar al’umma. Ita wannan rana, rana ce ta wayar da kan al’umma da kuma dora wa shugabanni nauyin samar wa al’umma ingantacciyar hanyar kiwon lafiya.

Inshorar kiwon lafiyar al’umma abu ne da ya zama wajibi a Afirka, saboda lafiya ce babbar ‘yancin dan Adam a dukkan dokokin duniya, bugu da kari, shi ne dukkan kasashe sun amince cewa za a iya samar da Inshorar Lafiya.

Me yake zuwa maka a rai idan aka ambaci shirin kula da lafiya bai-daya? Su wa ke shiga cikin shirin? Mene ne tsawon lokacin yinsa? Mutum nawa ya kamata su shiga cikin shirin? Wane irin ingancin kiwon lafiya ake bukata? Cimma shirin kiwon lafiya bai-daya siyasa ce ko kuwa wani abu ne da ya zama wajibi? Me ya sa wasu kasashe suke da tsarin lafiya bai-daya wasu ba su da shi?

Samar da kiwon lafiya bai-daya abu ne da ya fi karfin a kira shi siyasa, amma abu ne da ke da sarkakiya sosai, amma kowa ya amince cewar ana bukatar samar da Inshorar kiwon lafiya bai daya a ko’ina a duniya. Kuma an amince cewa Inshorar kiwon lafiyar al’umma na bai-daya na daya daga cikin kudurorin cimma muradun karni na ‘Sustainable Debelopment Goals (SDGs)’ na shekarar 2015.

Duk da matsalolin da ake fama da su, shirin kiwon lafiyar al’umma na bai-daya, wanda aka zartar a taron Thai, kuma aka yi wa gyaran fuska, sannan Hukumar lafiya ta duniya ta amince da shi, har yanzu ingantaccen tsari ne. Domin shi ne kadai tsarin da al’ummar kasa baki daya za su sami ingantaccen kiwon lafiya duk da cewa ba samun kudinsu daidai yake kuma ba. Ma’ana, mai kudi da talaka za su sami kulawar da ta dace daidai gwargwado ba tare da nuna fifiko ba.

Kasashe da dama da ba su da wadatacciyar hanyar samun kudi, suna samun cikas wajen cimma burin Inshorar kiwon lafiya na bai-daya, ko dai saboda rashin baiwa shirin muhimmanci ko kuma rashin sanya kudaden da suka kamata wajen wannan tsaro. Ko kuma rashin sanya harajin kiwon lafiya yadda ya kamata, ko kuma kasa karbar harajin daga wajen masu amfana da tsarin.

Tunda kasashe da dama sun fahimci wannan matsalar, akwai bukatar sanya mutanen kirki a cikin tsarin da kuma sanya al’umma su jagoranci irin wannan tsaro do tabbatar sa da kuma kawo sauki wajen cimma wannan shiri na samar da kiwon lafiya na bai-daya a kasahen da na mawadata tun da ana bukatar shirin Inshorar Kiwon lafiya ba al’umma.

Inshorar kiwon lafiyar al’umma, (Community based health insurance) (CBHI), shiri ne na ganin dama don samar da ingantacciyar hanyar kiwon lafiya wanda za a iya aiwatarwa a Unguwanni tsakanin al’umma. Za a yi tsari ne kamar na bankin al’umma, wanda al’umma za su hada kudi tsakaninsu don tallafa wa kansu ta fuskar kiwon lafiyarsu da na iyalinsu.

Tsarin kiwon lafiyar al’umma da ake da shi yanzu an bullo da shi ne a shekarar 2010. Kamar yadda rahoton Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ya bayyana, cewa wannan tsari na kiwon lafiya ya kunshi daidaikun mutane, mutanen Unguwa, ma’aikata, kabila, addinai da sauransu. Haka nan wannan shiri dai ya kunshi yadda al’umma za su hada kudaden su su taimaki kansu da kansu ta fuskar kiwon lafiyar su ba tare da tunanin samun riba ba.

Tare da Dakta Abubakar Kurfi

+2347052003824

[email protected],

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI