Connect with us

MANYAN LABARAI

NAZARI: Jaridun Da Ake Bugawa Da Harshen Nijeriya Da Kuma Ci Gaban Kasa

Published

on


Wannan wata makala ce da Shugaban kamfanin buga Jaridun LEADERSHIP, Sam Nda-Isaiah ya gabatar a taron kwana 2 da aka gabatar a dakin taro na gidan Sardauna na Arewa House da ke Kaduna, wanda aka gudanar ranar Litinin 15 ga watan Mayun da ya gabata. Wannan makala tana da muhimmanci sosai, domin akwai ilimantarwa a ciki. Albdullahi Usman ne ya fassaro mana.

Har yanzu ban san dalilin da masu shirya wannan taron suka zabe ni da in gabatar da wannan jawabi ba, amma kila saboda LEADERSHIP Group, wanda ni ne shugabanta kuma wanda ya kafata, tana da sashen buga jaridar Hausa. Duk da cewa ni ba kwararre ba ne a wannan bangare, amma LEADERSHIP Hausa ina da ta cewa a kanta. Wannan tabbas ne.

Kowa ya san cewa manyan mutane ba su san muhimmanci da daraja ko karfin da jaridun da ake bugawa da Harshen kasa suke da shi ba. Da sun sani, da sun fahimci cewa Jaridun da ake bugawa da harshen kasa na da darfi sosai. Amma bisa dukkan alamu kasashen duniya sun fahimci haka sosai fiye da mu. Shi ya sa muke da BBC Sashen Hausa, BOA Sashen Hausa da kuma irinsu mallakin kasashen Faransa, Jamus da Chaina. Sannan muna sane da tashar talabijin ta Arewa24, wacce kasar Amurka ta kaddamar kwanan nan don yakar ta’addanci.

Akwai jaridu da dama da ake bugasu da harshen kasa, amma wadanda a wannan bangaren muka fi sani, ita ce ‘Gaskiya Ta Fi Kwabo,’ wacce kamfanin buga jaridu na ‘New Nigeria’ ke bugawa. Abin bakin ciki shi ne yadda aka bar jarida mai muhimmanci irin ‘Gaskiya Ta Fi Kwabo’ ta mutu. Sannan akwai ‘Albishir,’ wacce gwamnatin jihar Kano ke bugawa a karkashin jagorancin jaridar ‘Triumph.’ A bangaren Yarbawa kuwa muna da ‘Alaroye,’ sannan a bangaren Igbo kuma ‘Ogene.’

Kamata ya yi jaridun da ake bugawa da harshen Nijeriya su zama manyan jaridu. Jaridar da aka fara bugawa a Nijeriya ita ce ‘Iwe Iroyin fun awon Ara Egba ati Yoruba,’ wacce ake bugawa da harshen Yarbanci. Ma’anar wannan suna shi ne, ‘Jaridar Yarbawa da Egba’. An fara buga ta ne a shekarar 1859, kuma Rabaran Henry Townsend na Cocin Anglican da ke Abeokuta ke bugawa.

Kamar yadda muke gani wannan jarida an fara ta ne kafin a hade yankunan kasar nan a kira su da sunan Nijeriya. Manufar kafa wannan jarida shi ne ya ilimantarwa. Wannan manufa ta sa don taimakon al’umma ne, ba don samun kudi ba. Wannan jarida ta bude kofar fitowar wasu Jaridun da dama. Amma kusan dukkansu sun mutu saboda ba za su iya rike kansu ba.

Jaridar ‘Gaskiya Ta Fi Kwabo’ ce babbar jaridar da aka yi a Arewa da harshen Hausa, an kafata ne a shekarar 1939, sannan kamfanin ‘New Nigerian Newspaper’ suka karbi tafiyar da ita a shekarar 1966. An ci gaba da buga ‘Gaskiya Ta Fi Kwabo’ har zuwa shekarar 2013. Wannan na nuna cewa ta dore har sama da shekaru 70. Wannan ci gaba ne sosai. Ita kuma ‘Triumph’ masu buga jaridar ‘Albishir,’ wadda ita ma ta yi suna zamanin da ake bugata. Amma yanzu dukkansu sun yi doguwar suma.

Babban ci gaban da aka samu a bangaren buga jaridu da harshen Nijeriya a lokaci guda shi ne kafa jaridun ‘Amana’ ta harshen Hausa, ‘Isokan’ ta harshen Yarbawa da kuma ‘Idoka’ da harshen Igbo, Wanda Cif MKO Abiola ke wallafawa. Abin takaici shi ne dukkan wadannan jaridu ba su tsallake ba, bayan mutuwar shi Abiola a shekarar 1998.

A yanzu manyan Jaridun Hausa da muke da su, sun hada da LEADERSHIP Hausa, Aminiya, Rariya (Wadda yanzu ake bugawa ta yanar gizo) da kuma mujallu irinsu ‘Muryar Arewa,’ Mujallar ‘Fim’ da kuma ‘Mahangar Arewa.’

Jaridun kasa ba sa samun ci gaba yadda kamata saboda ba ko’ina ake samun su ba, kuma ba sa samun talla, ballantana su iya rike kansu. Har yanzu ba wata jaridar kasa da ake bugawa kullum, amma kimar wannan jarida ba ya misaltuwa. Su ne hanyar samun labarai ga talaka. Wannan ne ya maida su babbar hanyar ciyar da kasar nan gaba. Sannan suna da hadari ga marasa gaskiya. Sannan Hausawa masu amfani da kafar sadarwar yanar gizo na da yawan gaske, domin ana kwatanta su da cewa suna da yawa a duniya.

Akwai wasu harsunan da har zuwa yanzu ba a ba su muhimmanci, kuma ina zaton ba wata jarida da ake bugawa da wadannan harsuna. Wannan harshe ya fi kusan dukkan harsuna girma, ina nufin ‘Pidgin English,’ wato ‘Broken English.’ Namu Brokin da ake yi a Nijeriya shi ma harshenmu ne. Yaranmu suna fara yinsa ne tun suna kanana. Mafi yawansu tun kafin su fara karatun Firamare. An kiyasta cewa mutane Miliyan 30 ne ke amfani da shi a Nijeriya, sannan mutane sama Miliyan da 100 ne ke yinsa a Yammacin Afirka. Sannan kowane harshe sama da 400 da ke Nijeriya akwai masu jin Brokin. Duk da cewa kowane daga cikin wadannan harsuna suna da yadda suke amfani da shi ko kuma yadda suke yinsa.

Ya kamata mu yi gaggawar yin amfani da wannan harshe da Allah ya ba mu, mu kyautata shi domin yana da matukar amfani ga al’ummar mu. Saboda kowace kabila na jin sa. ‘Pidgin English’ kamar yaren ‘Afrikaans’ ne a mutanen Kudancin Afrika, wanda za mu iya kiransa da ‘Pidgin Dutch,’ amma Turawan Afirka ta Kudu sun yi kokarin yi masa kwaskwarima, domin yanzu haka yana daya daga cikin harsunan da aka amince da amfani da su a gwamnatance. Haka kuma ana amfani da shi a kasashen Namibia, Botswana da kuma Zimbabwe.

Kamar yadda Turawan Afirka ta Kudu suka yi wa ‘Afrikaans’ kwaskwarima, mu ma ya kamata mu yi wa ‘Pidgin’ kwaskwarima, domin yanzu haka akwai ‘Lorraine Bible’ na mabiya addinin Kirista da aka wallafa da ‘Pidgin English’ domin amfanin sama da mutum Miliyan 100 da ke amfani da ‘Pidgin’ a Yammacin Afirka. Ya zama wajibi mu samar da jaridar ‘Pidgin English’ a Nijeriya.

Bari na ba ku wani misali da ya faru. Biyu daga cikin ‘ya’yana na karatu awata makarantar kwana a kasar Switzerland. Makarantar na da dalibai daga ko’ina a duniya, amma Turanci ne yaren da ake amfani da shi a makarantar. Ana yin Faransanci a matsayin daya daga cikin darussan da ake koyarwa a makarantar. ‘Ya’yana sun dawo hutu gida, wata rana sai na ji suna yin ‘Pidgin English.’ Na yi mamaki kwarai. Kafin su tafi makarantar ba su san me ake nufi da ‘Pidgin English’ ba. Lokacin da na ji suna yin wannan Brokin din da kuma tare da ni, da kun fahimci yadda abin ya ba ni mamaki ta fuskata. Lokacin da suka ga ban damu ba, sai suka fara yi min dariya. Suka ce ai a makaranta suka koye shi.

Wato abin da ya faru, makarantar akwai ‘yan kasar Rasha da dama da kuma Larabawa. Saboda haka sai wadannan Rashawa da Larabawa suke takura masu da yarensu. Wato kamar sukan yi gulmarsu da yare, kamar dai yadda yara ke yi a ko’ina. Sai ‘yata ta fada min cewa ‘yan Nijeriya kalilan din da suke wannan makaranta, musamman ‘yan Kudu sai suka fara yin ‘Brokin English’ a tsakaninsu. Don haka sai ‘ya’yana suka bi su suka koya karfi da yaji. Saboda haka sauran daliban wasu kasashen da sun ji ana yin Brokin sun san ‘yan Nijeriya ne. Sai ya zamana ko masu jin Turanci ba su fahimtar abin da daliban Nijeriya ke cewa lokacin da suke hirarsu da ‘Pidgin English.’ ‘Ya’yana suka ce ta haka ne suka sami kwatar ‘yancinsu a wajen sauran daliban makarantar. Hakan har ya sa daya daga cikin daliban da suka zo makarantar daga kasar Saudiyya ya nemi da su koya masa. Na ji dadin labarin sosai. A wannan lokacin ne na san muhimmancin ‘Pidgin English’ har na fahimci akwai arzikin da Allah ya yi mana da yawa, amma muna barnatar da su a banza.

Kammalawa

Jaridun da ake bugawa da harsunan kasa na gurguncewa ne saboda mafi yawan masu buga su, suna buga su ne don ilimantar da mutane ne ko kuma sanar da su wani abu ko kuma don cimma wani buri na siyasa. Jaridar da ake bugawa da harshen kasa kamar kowace jarida ce, ya zama wajibi a yi ta a matsayin kasuwanci matukar ana son dorewarta. Wannan ce kadai hanyar da ya kamata a bi.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI