Connect with us

SIYASA

NAZARI: Tunkarar Zabukan 2019 A Gombe: Ko Haruna Garba Zai Karbu?

Published

on


Daga Abubakar el-Mansur

A yadda ci gaban siyasa ta kasance karkashin mulkin dimokradiyya a yanzu, musamman tun daga shekara ta 1999 zuwa yau, yawancinmu da kaddara ta sa muka zabi wakilai daga mazabu daban-daban, abin takaici da bakin ciki shi ne hakarmu ba ta cimma ruwa ba, domin rashin tabuka abin a zo a gani da yawancinsu su kayi, ban da ‘yan kalilan wadanda suka dan taka rawar gani. Haka ya zama dole ne a sake dubawa da idon basira, domin zakulo nagari. Saboda haka, a yanzu mun shirya tsaf, domin ba za mu sake yarda abyi mana sakiyar da ba ruwa ba, inda muke sa rai wajen zaben mutane aminttatu wadanda za su rike amana a cikin jerin ‘yan takarar da muke da su a shekarar 2019 idan Allah Ya kai mu.

Tunda akwai muhimmancin zaben ‘yan takara nagari wadanda ke kaunar al’ummarsu a zuciya, ba na yaudara ba, haka kuma ya zama tilas kujerar gwamna a yayin da ya sauka bayan wa’adinsa na biyu kuma na karshe kamar yadda kundin tsarin mulki Kasa ya shimfida, a samu mutum nagari, adali, mai kyawawan dabi’u, da rikon amana, kuma nagartacce wanda zai tabattar da ci gaban ayyukan gwamna mai ci a yanzu yayin da ya sauka, harma ya dora akan wadada ya tarar ya gaje shi.

Idan muka dubi jerin sunayen mutane wadanda ke rububin neman shiga Gidan Gwamnatin Jihar Gombe a 2019, yawancimu na tunanin ko suna da kwarewar haye wannan kujera ta gwamna, amma duk da haka, tunaninmu shi ne na kwarai zai kasance a cikinsu.

Kungiyarmu wacce ta kunshi mutane amintattu, masu sanin ya kamata, rikon amana tare da sadaukar da kai ganin an samu shugabanci nagari, ta yi gagarumin aiki na tankade da rairaya akan cancanta ko akasin hakan na duk ‘yan takara da suka fito a yanzu da ma masu shirin fitowa nan gaba. Ta yin hakan, sai muka hango cewar mutum daya tilo cikinsu shi ne ya cancanci shiga gidan gwamnatin Jihar Gombe a 2019. Kuma wannan bawan Allah ba wani bane face Ambasada (Sanata) Haruna Garba (Magayakin Gombe).

Idan muka dubi rawar da ya taka a fannoni da dama tare da kwarewa wajen ayyuka da kuma matsayi daban-daban wanda ya rike a lokuta da yawa wadanda suka hada da kwararen ma’aikacin gwamnati, ma’abucin wasanni, mai kishin raya ilmin Islamiyya da na zamani, kana mai kyauta da taimakon al’umma, kuma fitaccen dan siyasa. Alal hakika, ta kowace alkibla ka dube shi, za ka san yana da kwarewa da kuma masaniya akan harkokin mulki wanda zai kai Jihar Gombe tare da al’ummar ta zuwa matakan rayarwa da ci gaba. Haka kuma, idan muka bi daki-daki wajen gogewarsa da kuma nasarorin da ya samu a fannoni daban-daban, lallai shi ya kamaci mu ba shi goyon baya fiye da kima, saboda ya ci gaba da kyawawan ayyukan gwamna mai ci a yanzu.

Babu shakka, har yau, muna tunawa tare da farin ciki a zuciyarmu yadda ya yi fice a lokacin yana Daraktan kula da kudaden aikace-aikace na hukumar raya aikin gona na Jihar Bauchi wadda aka fi sani da BSADP, inda ya nuna kwarewa kwarai a matsayinsa na masanin aiki, har ya kai hukumar ga abin koyi wadda ya sa ya sami yabo na musamman daga ciki da wajen kasar nan, sakamakon jajircewarsa. Shi ya sa a lokacin da aka kirkiro da Jihar Gombe a shekarar 1996, Kantoman Soja na farko wato  Gruf Kyaftin J. I. Orji Mai Ritaya, ya hakikance tare da gaskatawa a ransa cewar babu wani dan jiha da ya cancanci lura da aikace-aikacen kudaden sabuwar jihar da ya wuce Magayaki. Saboda haka, sai ya nada shi Akanta Janar na farko na Jihar Gombe daga bisani ya zama Kwamishinan Kudi a lokacin tsohon gwamnan farar hula na farko Mai girma Alhaji Abubakar Habu Hashidu, saboda shi ne kadai wanda aka san zai iya sarrafa kudade ‘yan kalilan wadda ke shiga asusun jiha.

Bisa jajircewar wajen yin aiki tukuru, sai aka ga ya kamata a kara masa da mai lura da harkan kasafi da dabarun kashe kudi, wadda har yanzu ana tunawa da ci gaban da ya kawo wa jiha.

Har ila yau, al’umma na sane da yadda ya tashi haikan wajen aiki babu kaukautawa kuma na gaba-gaba da nuna jarumtaka tare da wasu fitattun ‘yan asalin jiha da ya hada da wadda suka rasu da kuma na raye, inda a yau wadda suke rayen, idan za a tambaye su ba da shaida, lallai za su gaskata irin rawan ganin da Ambasada Haruna Garba ya taka wajen yakin kirkiro Jihar Gombe,wadda babu numfasawa har sai da haka ta cimma ruwa har ya kai an samu biyan bukatar samun Jihar Gombe mai cike da dimbin tarihi a 1 ga watan Oktoban 1996.

Idan muka sake dubawa a sauwake da kuma idon basira, zamu ga lallai Magayaki ya ci gaba da samun girmamawa da kuma fice daga al’umman jiha da yawa wanda ya taimaka har suka zama wani abu. Hakan  ya hada da ‘yan wannan Kungiya wadanda har yanzu muke morewa da kuma alfahari da shi wadda har duniya ta nade ba za mu manta ba.

Fannoni da dama wadanda ya taimaka wa al’umma daga wurare da dama a fadin jihar Gombe, sun hada da samun guraben ayyuka daban-daban a ma’aikatun gwamnatin jiha da na Tarayya, da ma cibiyoyi da hukumomi da dama ga ‘yan asalin wannan jiha, har ma da bada tallafin karo karatu na (Scholarship) ga masu sha’awar karo ilmi, ban da taimakon kudade ga daidaikun mutane wanda ke bukatar taimako. Hakan ya sa ya zama na farko a duk fadin Jihar Gombe wajen taimakawa al’umma.

Saboda haka, ba tare da musantawa ba, shi Magayaki, kowa ya sani mutum ne mai sakin fuska tare da saukin kai kwarai, wanda Allah Ya yi wa baiwa ainun, kuma babu kokwanto domin shi ne Allah Ya nuna mana zai ba mu kyakyawan shugabanci idan muka zabe shi a matsayin gwamnan Jihar Gombe a 2019 Insha-Allah, kuma muna da tabbaci, zai kai mu tudun mun tsira.

A bisa wadannan halaye na dattijantaka muka ga babu wani mai cancantar takarar kujerar gwamnan Jihar Gombe a 2019 da ya wuce shi, tuni muka mika wuya tare da yin mubaya’a a gare shi wajen kiran sa da babbar murya da ya fito takarar wannan kujera mai daraja ta daya a Jihar Gombe wadda muka yarda gaba dayanmu a bisa cancantar sa na mutum adali, mai rikon amana, gaskiya da kuma tsoron Allah, zai yi mana kyakyawan jagoranci.

Da yawanmu na sane da cewar Haruna Garba, shaharraren dan kwallon kafa ne a zamaninsa, wanda kuma a gaba ya rike kungiyar kwallon kafan Gombe United inda ya kai ta matsayin ciwo wa wannan jiha lambobin yabo da dama. Hakan sun faru ne ta wajen kashe makudun kudade daga aljihunsa kuma mun hakikance idan duk muka zabe shi a matsayin gwamna a 2019, zai yi fiye da haka.

Abin alfahari da yadda ya zama dan takaranmu daya tilo, ya samo asali ne a lokacin da aka zabe shi Sanata mai wakiltan Gombe ta Arewa a 2003. Nan da nan ya zama gwarzo abin yabo da karfafa gwiwa ga sauran ‘yan majalisan dattijai. Magayaki ya ci gaba da samun girmamawa inda aka dube shi a matsayin kwararen dan siyasa kuma masanin dokokin majalisa. Wadannan kyawawan dabi’u tasa ya sa aka nada shi a lokuta daban-daban a mataimakin shugaban kwamitin wasanni a majalisar dattijai. Haka kuma aka sake zaben shi a mataimakin shugaban kwamitin harkokin sojojin ruwa da kuma na fannin noma inda kujerarsa a majalisar dattijai ya zama cike da kai wa da komowa.

Nuna kauna da burin son ci gaba da yi wa kasar sa hidima yasa ya samu gawurtaccen yabo daga Shugaban Kasa na da watau Goodluck Jonathan har ya kai ga an nada shi Ambasada a kasar Kuwait.

A yadda yake mutum mai cikakkiyar kwarewa a fannonin mulki da sha’awar aikace-aikace, da ya hada da son bautawa al’umma tare da yi musu hidima, wanda kuma ya ke kyamar cin hanci da rashawa, babu wanda muke ganin ya dace da shiga gidan gwamnatin Jihar Gombe a 2019 a matsayin Gwamna da ya wuce Haruna Garba.

Saboda haka, duk mu illahirin ‘Yan Kungiyar Son Gaskiya, Rikon Amana da tabbatar da Shugabanci na Gari na Jihar Gombe wadda a turance akafi sani da “Association for Credibility and Good Gobernance” mun bada goyon bayanmu dari bisa dari ga Magayakin Gombe da ya fito takarar kujeran Gwamna a 2019 in Allah Ya kai mu.

 

el-Mansur dan jarida ne mai zaman kansa, ya rubuto mana wannan ne daga Gombe.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI