Connect with us

MANYAN LABARAI

RAHOTO: Akwai Kyakkyawar Alaka Tsakanina Da Buhari — Saraki

Published

on


Daga Mubarak Umar, Abuja

Shugaban Majalisar Dattawa, Alhaji Abubakar Bukola Saraki ya bayyana cewar dangantakar da ke tsakaninsa da Shugaba Muhammadu Buhari a kullum kara karfi take yi, ba kamar yadda wasu mutane ke kallo akwai sabani tsakanin bangaren Majalisar Zartaswa da na Dokoki ba.

Saraki ya fadi hakan yayin wata ziyara da Kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’ah Wa Ikamatus Sunnah (JIBWS) karkashin jagorancin Shugabanta, Sheikh Mohammed Sani Yahaya Jingiri a Majalisa ta kai masa makon da ya gabata.

A wata takardar da ya fitar ta hannun Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Jama’a, Mohammed Isa, Bukola Saraki ya musanta zarge-zargen da ake yi cewar akwai takun saka tsakanin bangaransu na Majalisa a kuma na Zartaswa, inda ya ce duka bangarorin biyu suna aiki kafada da kafada da juna ba tare wata tangarda ba.

“Ina mai tabbatarwa da al’umma cewar babu takun saka tsakaninmu da Fadar Shugaban Kasa, sai ma cikakken hadin kai da muke bawa juna wajen gudanar da ayyukanmu yadda suka kamata, muna bawa Muhammadu Buhari dukkan goyon bayan da yake bukata a matsayinsa na Shugaba Kasa.”

“Daga lokacin da muka shigo Majalisa, mun karbi takardun bukatun sahalewa daga Fadar Shugaba Kasa guda 196, ciki mun rattaba hannu a 185, guda 11 kacal muka yi watsi da su. Wannan ya nuna mun bada hadin kai wajen tabbatar da kudurori fiye da kaso 90 cikin 100.

“Na san za ku ci karo da maganganun kala-kala a gidajen rediyo, talabijin da jaridu, amma ina mai tabbatar maku wadannan murahu na gwamnati guda biyu suna aiki tare, fiye da majalisun da aka yi a baya. A watan Janairu, na ziyarce shi (Buhari) a Fadarsa kuma na tabbatar masa a shirye muke don mu ba shi goyon baya wajen yin aiki tare da juna. Mutane suna fadar abin da suka ga dama ne kawai, amma tsakaninmu babu wata matsala.

“Tun da har kun kawo min ziyara, to ga sako zan ba ku, ku sanar da mabiyanku da suke jin wasu maganganu a gidajen rediyo, su sani cewar Shugaban Majalisar Dattawa da sauran Sanatoci ba su da matsala da Fadar Gwamnatin Tarayya, tun bayan rantsar da mu komai tare muke yi, saboda haka akwai kyakkyawar alaka a tsakaninmu.” A cewar Saraki.

Saraki ya ce burin Majalisa Dattawa shi ne tabbatar da tsarin Shugabanci mai cike da adalci ta fuskar ci gaban kasa, tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma ganin dukkan kudire-kudiren da suke gaban Majalisa an rattaba masu hannu sun zama doka.

Baya ga haka ya ce, batun dokar Daidaita Jinsi wadda yanzu haka take gaban Majalisar, za a tabbatar da cewar ba taba mutuncin kowane addini ba, kasancewar an shirya yin adalci ga dukkan mabiyan addinai a kasar nan.

“Har ila yau, ina son shaida maku cewar batun doka Daidaita Jinsi, duk da ta shafi addinai, muna iya bakin kokarinmu don ganin mun tabbatar da ita matsayin doka ba kuma tare da taba wani bangaren na addini ba.

“Babu wata doka da za ta wulakanta addini, saboda haka dole mu sanya wannan a zukatanmu. Mun tattauna batutuwa da yawa game da hakan, rahoton karshe kawai mu jira wanda za mu yi nazari a kai, domin har yanzu dai tattaunawa muke yi, bukata ce aka gabatar, saboda haka babu batun a yi ta cece-ku-ce da ita da sunan addini. Ina tabbatar maku babu wata matsala.”

Game da batun ilmi, karatu da wa’azi kuwa, Sanata saraki ya ce akwai tsare-tsare masu yawan gaske da Majalisar za ta bullo da su domin saita al’amura. Ya ce hakika ana samu matsaloli nan da can, amma hakan ba zai hana a zauna da masu ruwa da tsaki don ganin a kamo bakin zare warware ta ba. Ya ce idan hali ya yi za a kira malaman addinai domin su bada tasu gudunmawar kan batun.

“Muna bullo da hanyoyi wadanda za su taimaka mana na ci gaba da kasancewa a matsayin kasa guda daya, shi ya sa muke son bin tsarin daidaito tsakanin addinai domin yin aiki tare da juna babu bambanci.” A cewarsa.

Da yake nasa jawabi, Shugaban JIBWIS, Sheikh Sani Yahya Jingir, ya yabawa Bukola Saraki sakamakon rawar da ya taka wajen kin amincewa da batun ‘yan takara Musulmi daga Jam’iyyar APC a matsayin Shugaban Kasa da Mataimaki a zaben 2015, a cewarsa Nijeriya kasa ce ta kowa da kowa ba ta wani addini ba, saboda haka akwai bukatar samar da daidaito a tsarin shugabanci.

Har ila yau Shehin Malamin ya jinjinawa Majalisa bisa tsayuwar daka da ta yi wajen yin wancakali da batun dokar halatta aure jinsi da kuma hukuncin kisa a laifukun da ba su kai na kisa ba, inda ya ce sam Musulunci ba ya tare da wannan tsari. Ya kuma bukaci Majalisar da ta yi wa kowa adalci a dokar Daidaita Jinsi da ake kokarin kafawa.

Ya kuma yi kira da a samar da daidaito wajen dibar ma’aikata da jami’an gwamnati a mukaman siyasa ta hanyar yin amfani da yawan al’ummar da kowane yanki yake da shi. Sannan ya jaddada bukatar da ke akwai na tabbatar da hadin kai tsakanin bangaren Zartaswa da na Majalisa.

Haka zalika Shehin Malamin ya nemi da Majalisa ta sake duba ga yanayin da ake gudanar da jarrabawa share fagen shiga jami’a (JAMB), domin salon da ake bi yana kawo nakasu matuka ga ci gaba ilmi a kasar nan.

A karshe ya yi addu’ar Allah ya bawa Shugaba Muhammadu Buhari lafiya wanda yanzu haka yake kasar Ingila inda ake duba lafiyarsa.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI