Connect with us

RAHOTANNI

RAHOTO: Gwamnatin Kaduna Ta Kaddamar Da Irin Masara Na Zamani Ga Manoma

Published

on


Daga Ibrahim Ibrahim, Kaduna

A yunkurin Gwamnatin Jihar Kaduna na ganin ta kyautata ma kananan manoma ta hanyar wadata su da kayan iri na noman zamani, Kwamishinar Ma’aikatar Raya Karkara da Birane ta Jihar Kaduna, Hajiya Balaraba Aliyu Inuwa ta kaddamar da wani shiri na baiwa kananan manoman jihar tallafin irin masara na zamani.

Irin wanda a turance ake kira “Bossting maize production through balue-kits, an kaddamar da shi ne a Garin Banki da ke Gundumar Leren Dutse a Karamar Hukumar Kubau da ke Jihar Kaduna.

A yayin da take jawabi a bikin kaddamarwar, Kwamishinan Karkara da Raya Birane, Hajiya Balaraba Aliyu Inuwa, ta bayyana cewa, wannan shiri na hadin gwiwa ne tsakanin Gwamnatin Jihar Kaduna da Kamfanin Bunkasa Noman Masara na Zamani, wanda suka hada hannu domin samarwa kananan manoma da irin masarar da zai bunkasa masarar da suke nomawa da fiye da kashi 80 cikin 100.

Kwamishinar ta kara da bayyana cewa, a karkashin wannan shiri za a rarraba irin masara har guda 2,500 ga manoma 800 wanda suka yi rijista a karkashin wannan shiri, wanda za a fara kaddamar da shi a yankuna uku da ke fadin Jihar Kaduna, da suka hada da: Anguwar Banki da ke Karamar Hukumar Kubau, da Anguwar Wahala da ke Karamar Hukumar Kajuru, sai kuma Anguwar Moroa da ke Karamar Hukumar Jama’a.

A cewar Hajiya Balaraba Aliyu, Gwamnatin Jihar Kaduna a karkashin jagorancin Malam Nasiru El-rufai, ta yi tunanin bullo da wannan shiri ne domin ganin ta sauwake ma kananan manoman Jihar Kaduna da ingantattun irin noma na zamani domin su yi kafada da kafada da sauran takwarorinsu manoma da ke fadin duniya. Wanda a cewar ta, an ware ma wannan shiri kudi har naira miliyan 70 domin ganin wannan shiri ya wadatu ga manoma.

Shi ma a nasa jawabin, Shugaban riko na Karamar Hukumar Kubau, Honarabul Kabir Aliyu, ya bayyana jin dadinsa game da wannan shiri da Gwamnatin Jihar Kaduna ta kirkiro da shi, musamman domin samar wa manoma wata hanya a saukake domin inganta albarkatun abin da suka noma fiye da yadda sukeyi a da.

Shugaban Karamar Hukumar ya roki manoman da za su ci gajiyar wannan shiri, da su tabbatar sun yi amfani da wannan dama da suka samu domin ganin sun wadatar da Jihar Kaduna da abinci.

Wani babban jigo a fannin noma da ke Karamar Hukumar Kubau, Malam Hashimu Garba, ya bayyana wannan shiri na noman zamani a matsayin abin da tuni wasu kasashe suka dade suna cin gajiyarsa. Sannan ya yi godiya ga Gwamnatin Jihar Kaduna musamman a kan yadda ta yi tunanin fara gabatar da wannan shiri a yankinsa na Karamar Hukumar Kubau.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI