Connect with us

MANYAN LABARAI

RAHOTO: Jami’an Tsohuwar Gwamnatin Shema Za Su Amayo Naira Bilyan 55

Published

on


Daga Sagir Abubakar, Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta ce ba ta taba samun abin da ya kai Naira miliyan dubu hudu a cikin wata guda daga asusun Gwamnatin Tarayya a cikin shekaru biyu da tayi bisa karagar mulki ba.

Gwamna Aminu Bello Masari ya tabbatar da hakan a lokacin da shugaban Kwamitin binciken kudaden da suka salwanta da kaddarori daga gwamnatin da ta gabata, maishari’a Ado Mohammed Ma’aji ya gabatar da rohoton wucin gadi.

Kamar yadda Gwamnan ya ce, kowane wata abin da gwamnatinsa ke samu daga lalitar tarayya kadan ya ke haura Naira miliyan dubu uku. Ya yi nuni da cewa da farko a gwamnatance jimlatan abin da ya salwanta daga waccan Gwamnati ya kai  milyan dubu 73 a madadin Naira miliyan dubu 55 da hukumar binciken ta gano.

Ya ba da tabbacin cewa za a gabatar da wannan rohoton na wucin gadi a zaman da majalisar zartaswa ta jiha za ta yi domin tattaunawa.

Gwamnan ya bayyana cewa an kafa kwamitin binciken ne domin ba jami’an gwamnatin da ta gabata dama su kare kansu daga zargin da ake yi masu na almundahana da kudaden.

Alhaji Aminu Bello Masari ya ce babu wata niyya ta yafe abin da ba na shi ba ne na al’ummar jihar ne.

Ya gode wa shugaban kwamitin da sauran membobinsa kan yadda suka amince su yi ma mutanen jihar aiki.

Da yake gabatar da rohotan, shugaban kwamitin Barista Ado Mohammed Ma’aji ya bayyana cewa hukumar ta amshi muhimman takardu na neman bayanin wasu ayyuka da aka gudanar guda goma sha uku a inda biyu daga cikinsu ba a yi matsaya a kansu ba, guda uku kuma su ma ba wani matsaya a kansu sai kuma guda daya a matsayin shawara.

Ma’aji ya kara da cewa sama da Naira miliyan dubu hamsin da biyar ne hukumar ta gano cewar sun yi batan dabo daga shuwagabannin gwamnati da ta gabata.

Ya ce kwamitinsa yana ba da shawarar cewa duk wanda ke da hannu game da salwantar kudaden a tilasta masa ya maido da su ko kuma a dau matakin hukunta shi don magance afkuwar hakan a nan gaba.

Ya gode wa Gwamna Aminu Bello Masari, da al’ummar jihar da sauran masu ruwa da tsaki a kan gudummuwa da hadin kan da suka ba da wajen samun nasarar aikin.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI