Connect with us

MANYAN LABARAI

RAHOTO: ‘An Samu Kwanciyar Hankalin Yin Ibada A Shekaru Biyun Gwamnatin Buhari’

Published

on


Daga Mustapha Ibrahim Tela Kano

An bayyana cewa hawan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a karkashin Jamiyar APC karagar mulki a shekaru biyu kacan an samu gagarumar nasara ta fannoni daban-daban musamman tsaro.

A sanadiyyar hakan, a yanzu ana gudanar da salloli da tafsirai da fadakarwa a masallatai da sauran ibadu da Musulmi ke yi da kuma na mabiya Addinin Kirista a coci-coci ba tare da dar-dar ba.

Ma’ajin jam’iyar APC na kasa, Honarabul Bala Muhammad Gwagwarwa ya bayyana haka a lokacin wani bikin raba tallafi ga mutane 1,141 da dan majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Dala a majalisar wakilai, Hon. Aliyu Sani Madakin Gini ya gudanar a dakin taro na Gidan Mallam Aminu Kano da ke Unguwar Gwammaja, Kano.

Gwagwarwa ya ce idan aka yi la’akari da yanayin da Gwamnatin PDP da ta gabata ta jefa kasar nan na rashin tsaro da fargaba da dar-dar a tsakanin jama’a a kasuwanni, makarantu, masallatai coci-coci da sauran wuraren aiki yanzu duk wannan ya kau. Don haka jam’iyyarsu ta APC ta samu nasara kuma kwalliya ta biya kudin sabulu a shekaru biyu da hawan ta karagar mulki.

Ma’ajin na kasa ya Shugaba Muhammadu Buhari a kan irin kokarinsa na yaki da cin hanci da rashawa da kuma samar da tsaro da zaman lafiya a wannan kasa, ya kuma kara da cewa APC na nan a dunkule ba wata rigima a cikinta.

Ita kuwa shugabar mata ta Kwankwasiyya, Hajiya Zainab Audu Bako ta bayyana cewa matsayin da Gwamnatin Ganduje ta ba mahaifinta a matsayin Gwamnan zamanin soja na daya da ya fi aiki a cikin shekaru 50 da Kano ta yi a matsayin jiha kana da ayyana  Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin Gwamnan farar hula da yazo na biyu a aiki abu ne da ya faranta mata rai sosai.

Shi dai wannan taro na ba da tallafi ga wadannan mutane da suka hada da maza da mata da matasa da datawan Dala ya kunshi baiwa mutum 210 tallafin mashina, mata 105 kekunan dinki, mutum 53 filayen gina gidaje sai kuma wasu membobi da dattawa da suka fito daaga mazabu 12 na karamar hukumar da suka samu tallafin kudade.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI