Connect with us

RAHOTANNI

RAHOTO: An Yaba Wa Ganduje Kan Ciyarwar Azumi

Published

on


Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

An bayyana ciyarwa a azumin da Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ke yi da cewa abin a yaba ne kwarai da gaske.

Wannan jawabi ya fito daga bakin shugaban Majalisar Mahaddata Alkur’ani reshen Jihar Kano, Gwani Sunusi Abubakar a lokacin da tawagar manema labarai ta ziyarci tsangayarsa wadda ke cikin cibiyoyin da Gwamnatin Ganduje ke samar da abincin buda baki ga al’umma.

Gwani Sunusi Abubakar ya ci gaba da cewa “mu majalisar Mahaddata Alkur’ani reshen Jihar Kano muna godiya kwarai bisa samar da irin wadanan cibiyoyi da ake samar da abinci domin amfanin masu bukata. Halin da ake ciki ya tsananta kwarai, domin magidanta da yawa ne ke zuwa domin karbar nasu abinci, haka kuma muna aikawa ga tsangayu da kuma masallatai da wuraren zaman jama’a domin sa albarka ga wannan aikin alhairi da Gwamna Ganduje ke aiwatarwa”.

Da aka tambaye shi ko adadin kwano nawa ake dafawa a duk rana? Sai ya amsa da cewa “muna dafa kwano goma zuwa sha biyu a duk rana, bayan kunu, kosai, fanke, dabino har da ruwan sha ake sakawa a duk roba guda. An umarce mu da mu tabbatar da samar da ingantaccen abinci wanda kowa zai iya ci tare da gamsuwa”.

Saboda haka ya bukaci Alarammomi a Jihar Kano da su ci gaba da sa wannan gwamnati cikin addu’o’in a wannan wata mai albarka.

Jama’ar da wakilinu ya samu zantawa da su sun bayyana godiya tare da yabawa da irin abincin da ake dafawa a wannan cibiya, inda suka ce ko shakka babu abincin ya kai duk yadda ake bukata “muna yiwa Gwamna Ganduje addu’ar fatan dorewa da wannan aikin alhairi”.

 

 

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI