Connect with us

MANYAN LABARAI

TATTAUNAWA: Abin Da Ya Kamata ‘Yan Nijeriya Su Yi Bala’o’in Kasar Su Kau — Shaikh Dahiru Bauchi

Published

on


SHAIKH DAHIRU USMAN BAUCHI, yana daya daga cikin manya kuma fitattun Malaman Addinin Musulunci a Nijeriya. Kamar yadda ya saba duk shekara idan watan Ramadan ya kama yakan tare a Kaduna domin gabatar da Tafsirin Alkur’ani maigirma, a bana ya yi hakan. LEADERSHIP Hausa ta samu sukunin tattaunawa da shi jim kadan kafin ya fita zuwa Masallacin da yake Tafsiri a Unguwar Tudun Wada Kaduna a makon jiya kan tsarabar garabasar da Azumin Ramadan ya kunsa. Sannan ya bayyana irin yadda ya kamata duk wani Malami mai Tafsiri ya kasance wurin gabatar da karatunsa. Bai tsaya nan ba, ya kuma lissafto abubuwan da ya ce su ne ummul’haba’isin matsalolin da Nijeriya ke kaka-ni-ka-yi a ciki kana ya kawo mafita a kai. Wakilinmu, KHALID I. IBRAHIM ne ya tattauna da shi kamar haka:

Me Shehi zai bayyana kan wannan wata mai alfarma na Ramadan da muke ciki?

Da fari muna kara gode wa Allah da ya sanya mu cikin al’umman Manzon Allah (SAW), al’umman da Allah ya karrama su. Mu ne wadanda Allah ya kebance mu da samun Annabi Muhammadu, fiyayyen Annabawa, kuma shugabansu kuma ya kebance mu da samun Alkur’ani, babban littafin da ya fi kowani littafin da ya fito daga Allah. Daren da aka saukar da shi ma sai aka ce wa daren, daren Lailatul Kadiri, watan da aka saukar da shi Alkur’ani yana da wata darajar da ya zama dole sai mun azumci watan. Dalili kuwa, Mala’ika ne ya kawo Alk’ura’ni, Annabi ne ya fassara a kuma cikin wannan watan. A bisa haka ne sai mu yi kama da shi Mala’ikan da ya kawo Kur’ani. Mala’ika ba ya cin abinci, ba ya shan ruwa, ba ya aure. Dare da rana tasbihi yake muma da rana sai mu yi kama da wannan Mala’ikan, ba za mu ci abinci ba; ba za mu sha ruwa ba; ba kuma za mu yi saduwar aure ba. Shi kuma Annabi (SAW) shi ne ya fassara mana Alkur’ani ya zuwa gare mu. A dare kuma sai mu yi kama da Annabi muna cin abinci muna shan ruwa, muna kuma kwana wajen iyalanmu. A sabo da haka ne aka kallafa mana wannan Azumin domin mu yi wa Allah (SWT) godiya, Allah da ya bamu Annabi ya ba mu Alkur’ani. Kana domin mu gode wa Allah da ya bamu shiriya. Azumin ya zamana godiya ne wa Allah, nafilfilun da muke a cikin dare su ma sukan zama godiya ne ga Allah, haka za mu yi ta yi har zuwa watan ya kai karshe.

Idan kuma watan ya kare, a washe gari sai mu fita, mu kira mutanen kauye mu hadu a fili, mu taru mu yi kabbarbaru mu gode wa Allah da ya bamu Annabi da Kur’ani.

Shi kuma Daren Lailatul Kadri, dare ne wanda ya fi wata dubu wanda babu irin wannan kwanan a ciki. Wata dubu dai ya fi shekaru 80, wato a cikin rayuwarmu kullum muna kara shekara 80 idan Azumi ya zo, banda falalar sauran kwanakin. A sauran kwanakin kamar yanda ka san idan mutum ya karya azumi sai ya biya wata biyu, ashe kenan kowane wuni yana daidai da wata biyu akalla. Haka shi ma dare, haka shi kuma idan daren Lallatul Kadir in ya zo yakan ninninka fiye da wata dubu. Mun gode wa Allah da ya bamu wadannan alkhairan a cikin wannan watan na Ramadan.

 

Mene ne ya kamata mutane su shagala da su a wannan watan na Azumi?

Mu shagala da zikirin Allah, mu yawaita karatun Alkur’ani, Salatin Annabi, mu kuma yawaita tuba ga Allah (Istigfari) a cikin wannan watan na Ramadan. Domin wata ne na alfarma koda wani ya zage ka ba za ka rama ba sai ka ce masa to ni dai ina azumi! Ni dai ina azumi!! Ni dai ina azumi!!!. Haka kuma yana da kyau a watan azumi mu shagalta da yawaita sadaka, mu yawaita ciyar da mutane bayin Allah, mu yawaita bayar da sadaka domin samun falalar da ke cikin watan na Azumi. Wata ne wanda yake cike da alkairai a cikinsa, tun da an saukar da Alkur’ani a cikinsa, tausayi, kyawawan halayya, kamewa daga sabo don ana son kowa ya shagaltu da wadannan a cikin wannan watan mai alfarma.

 

Yaya matsayin wajibcin Azumin ga Musulmi?

Wajibi ne, dole ne a kan kowani musulmi mai lafiya, balagagge yin Azumin watan nan dole ne a gare sa. Idan ya karya Azumin da rana ma dole ne sai ya biya watanni biyu, ko kuma ya ‘yantar da bawa ko kuma ciyar da miskinai 60. Don haka dole ne yin Azumi matukar babu wani dalili na shari’a. Mutum haka kawai ba zai ce shi ba zai yi Azumi ba.

 

Idan muka dawo cikin watan, akan gabatar da Tafsirai da kuma sauran wa’azozi, mece ce hikimar hakan?

Shi watan da yake na Alkur’ani ne dole ne dare da rana ka ji Alkur’ani, ana karantawa ana fassara da ku kowani baki tun da Annabi (SAW) Manzon kowace kabila ne, kowace kabila Malamin cikinta wakilin Manzon Allah ne cikin isar da sakon Allah. Akan yawaita karanta Alkur’anin ne domin watan sa ya zo, kamar yadda idan watan Rabi’u Auwal ya zo, watan da aka haifi shi Manzon Allah (SAW) kenan to dare da rana za ka ji ana anbaton Annabi (SAW). Ina aka haife sa?, ina ya yi rayuwa? Yaya rayuwarsa? Yaya aka aiko masa da aika? Ta yaya ya isar da aikan?, har watan ya kare za ka ji ana ta ambatonsa domin watan da ya zo kenan. Kamar yanda shi wannan watan na Ramadan wata ne na Alkur’ani don haka shi ma dare da rana za ka ji ana karanta Kur’ani ana kuma fassarawa ta kowace irin lugga daga cikin luggogi. Saboda Manzannin da suka gabata, ana aiken kowani Manzo wajen jama’arsa da harshensu ne, amma da yake shi Annabi Muhammadu (SAW) an aiko shi ga dukkanin duniya ne sai ya zama a kowace kabila yana da wakilinsa, wanda ya ji larabci ya fada musu a cikin yaren da su ke ji. A bisa haka ne dare da rana za ka ji ana karanta sakon Allah ga mutane.

 

A matsayinka na babban Malami kuma jagora, me za ka ce wa sauran Malamai masu Tafsiri a wannan watan kan dora al’umma a kan hanya madaidaiciya?

Mu da muke wakiltan masu Tafsiri ko na ce mu da muke kwaikwayon Tafsirin masu Tafsiri ya kama ta mu ji tsoron Allah. Idan fa mutum ya rike Alkur’ani yana fassarawa, ma’anarsa Allah ne yake magana wa Annabi, Annabi yake isar wa duniya kai kuma mai tafsiri wakilinsa ne. Idan fa ka yi karya wa masu sauraronka ta hanyar kari ko shigo da wasu abubuwan da ba’a muhallinsu suke ba; ka fadi abin da Allah bai fada ba ka ce wa masu sauraronka haka Allah ya fada’ ka yi wa Allah karya, Allah zai kama ka. Idan kuma ka yi kari ne zai kama ka, idan ka jirkita ma za a kama ka, gara idan ka rage kai ragaggene. A bisa haka na ke cewa a ji tsoron Allah ban da fassara Alkur’ani da son zuciya, ban da kuma fassara Alkur’ani da jahilci, ban da fassara Alkurani da zagin wadansu mutanen da shi Alkur’anin bai zage su ba. Idan kai ne kake son zaginsu sai ka karkata aya ka zage su ka ce ayar tana nufin wadansu mutane, alhali ko wadanda Alkur’anin yake nufi daban, Allah zai kama ka kuma zai hukunta ka. Don haka kai mai yin haka ka ji tsoron Allah. A kuma daina ce-ce-ku-ce a fagen Tafsiri domin komai iliminka akwai wadanda sun fika ilimi. Wadanda kuma suka fika ilimi dole ne su fadi maganar da kai baka sani ba; idan sun fadi maganar da kai baka sani ba, sai ke nemi sanin maganar ba wai ka kama musu kan maganar ba; ka ce wai kai bai yiwuwa, bai yiwuwa, to malam ai yana yiwuwa mana, iliminka ne dai ya dan gaza, a nan kuma sai ka nemi sani a wajen masana. Saboda haka malamai mu ji tsoron Allah ka da a yi wa Allah karya da sunan Tafsiri, kada kuma a jirkita wa Allah maganarsa, da ka yi haka gara ka hakura ya fi maka alkairi.

 

Akwai falala, daraja, daukaka ko alfanu da musulmai suke ribanta da su a cikin wannan watan?

Ai alfanun kenan, darajar kenan, za su samu ‘yanci a cikin wanna watan, a cikin wannan watan ne Allah zai ‘yantar da mutum. A cikin wannan watan ne Allah zai yafe wa mutum zunubansa, a ciki ne mutum yake iya samun duk wata alfanu da yake nema. Don haka ka ga babu wani watan da mutum zai ribance shi fiye da wanan watan na Ramadan.

 

Ko kana da shawarwari ga al’ummar Nijeriya a daidai wannan lokacin?

Mutanen Nijeriya gabaki daya muna kiran juna da cewar mu koma ga Allah, mu yawaita tuba wa Allah, Salatin Annabi, ambaton Allah zikiri, mu yawaita karanta Alkur’ani mai girma mu kuma yawaita neman Allah ya yaye mana abubuwan da muke ciki. Abubuwan da muke ciki na bala’i da kashe-kashe, sace-sacen da ake yi a cikin kasar nan, satar mutane, satar dabbobin da ake yi duk wadannan bala’o’i daga Allah suke. Allah kuma ya ce musiba ba ta sauka a kan mutane sai sun sabe shi, su ne suke rikito wa kansu wannan musibar, ba don ma Allah yana ragewa ba.

Zagin Waliyyai, zagin Sahabbai duk wadannan suna jawo bala’i cikin kasa! A daina zagin Waliyyai idan ana son zaman lafiya. Idan mutum ya yi gaba da Waliyyi zai fuskanci fushin Allah. Allah ya ce duk wanda ya yi gaba da Waliyyina zan yake shi, yau ko Amurka ne ta ce za ta yake ka ya zaka kare balle Allah? Muna zaune a kasa daya da masu zagin Waliyyai suna kafa makarantu don koyar da zagin Waliyai, zagin zikirin Allah da sauransu. Wadanan abubuwan su ne suke jawo mana bala’o’i na kisa, satan da ake fama da su da sauran bala’o’in da muke ciki a yanzu. Allah ya karemu ya kuma yaye mana wadannan bala’o’in albarkar Annabi (SAW).

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI