Connect with us

WASANNI

A Shirye Nake Na Amsa Kiran Real Madrid — Hazard

Published

on


Dan wasan gefe na Chelsea Eden Hazard ya ce zai duba bukatar Real Madrid idan ta bukaci sayensa, amma kuma ya ce zai ci gaba da zama a Chelsea na karin shekaru masu yawa.

Akwai jita-jita mai karfi da ke danganta Hazard wanda ya ji rauni a idon sawunsa a lokacin atisaye a tawagar kasar Belgium, da Zakarun Turan.

Dan wasan na Belgium ya sheda wa jaridar Het Laatste Nieuws cewa; “Dukkanninmu muna da buri. Zai iya kasancewa Spain, zai kuma iya kasancewa ci gaba da zama a Chelsea.’’

“Amma dai ba abin da nake tunani ba ne a yanzu. Amma zaiyu agan abin da zai faru.’’

Real ta doke Jubentus 4-1 ta dauki Kofin Zakarun Turai a karo na 12, wanda ya kasance na uku a cikin shekara hudu.

Hazard ya kara da cewa, idan har zan je Real Madrid, zan iya kasancewa a benci ni ma, saboda haka abin da nake duba wa kaina shi ne zabi na gari.

Dan wasan mai shekara 26, wanda ya koma Chelsea daga Lille a watan Yuni na 2012, ya taimaka wa Blues din ta dauki kofin Firimiya a kakar da aka kammala.

Da aka tambaye shi ko zai iya barin Chelsea, sai ya ce, a kwallon kafa ba ka san abin da zai faru ba, amma dai a yanzu ya ce ba wannan abu a ransa.

Ya kara da cewa shi har yanzu dan wasan Chelsea ne, yana da sauran shekara uku. Amma zai ga abin da zai kasance.

A game da ko Chelsea za ta bukaci ya tsawaita kwantiragin nasa, sai ya ce a yanzu dai kungiyar ba ta bukace shi da hakan ba, amma dai za ta iya ba shi.

Hazard ya ce a ‘yan shekarun da suka gabata kowa yana maganar cewa zai koma PSG ne, a bana kuma Real Madrid ake cewa, shekara mai zuwa kuma wata kungiyar za a ce.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI