Connect with us

WASIKU

WASIKU: ‘Batun Koyar Da Darussan Kimiyya Da Lissafi A Harshen Gida’

Published

on


Hakika, yana da mutukar muhimmanci, idan gwamnatin Nijeriya za ta sa ana koyar da darussan kimiyya (Sciences) da lissafi (Mathematics) cikin manyan harsunanmu na kasa, wato; Hausa, Yarbanci da Igbo, a makarantun Furamare da Sakandire, domin idan za a koyarwa dalibai darussan da yaren su da suka fi iyawa, za su fi koyon darussan cikin sauki, saboda wadannan darussan na kimiyya da lissafi suna da mutukar sarkakiya; akwai wasu abubuwan da idan da turanci za a koyarwa dalibai ba za su fahimta yadda ya kamata ba, shi yasa kasashe da dama a duniya  da yaren kasar su suke koyarwa, irin su; Indiya, Sudan Chana, Iran da de sauran su, wanda suma wasun su rainon Ingila ne.

Daga Muhammad Babangida Kiraji, Gashua, 08029388699.

 

 • Kira Ga Dan Majalisar Katsina

A yayin da wasu Jama’a ke yin murna har sukan zuba ruwa a kasa su sha; dariya baki har kunne game da sam barka da Allah ya yi sakamakon zaben wakili na kwarai da suka yi a Majalisar Wakilai da ke Abuja, kasancewar yadda wakilin nasu suke zama a cikin su game da share masu hawaye ta hanyar samar masu da abubuwan inganta rayuwa.

Mu a karamar hukumar Katsina a kasin haka aka samu. Domin mu muna cizon yatsa ne game da yin da mun sani. Wakilin namu datan dabo ya yi mana tunda muka ingiza keyar sa Abuja ba, zuwa ba aike mun rasa ruwan da ya ci mana shi. Shin ko maka-makan gine-ginen Abuja ne suka dauke hankalin sa?

Da fatan zai yi koyi da takwarorinsa masu kyautatawa jama’ar su shi ma ya rika kulawa da nasa Jama’ar domin masu iya magana na cewa ‘Don tuwon gobe ake wanke tukunya.’

Daga Haruna Muhammad Katsina 07039205659

 

 • Nijeriya kasarmu ta gado

Allah ya hore mana yawan al’umma wanda ko a duniya muna sahun gaba-gaba wajen yawa amma mun kasa yin amfani da yawan da muke da shi wajen ciyar da kasarmu gaba, a nahiyarmu ta Afirka mun fi kowace kasa yawa – mune na daya, muna da kasar noma muna iya yin noma rani da damina, Allah ya hore mana ma’adanan karkashin kasa kala-kala da dai sauran arziki bila’adadin wasu mun gano wasu ba mu gano su ba duk Allah ya bamu su amma kash! har yanzu talakan Nijeriya na fama da matsalar:

 1. Ruwan sha
 2. Ilimi
 3. Hanyoyi
 4. Wutar lantarki
 5. Da kuma fannin kiwon lafiya da sauransu.

Wadannan abubuwa sun gaza samuwa a wajen talaka a wadace. Idan muka yi duba da irin arzikin da kasarmu ke da shi, sai mu ga cewa ko kusa talaka ba ya morar arzikin kasar, wasu mutane ne kalilan ke kasafta dukiyar kasar su cika aljifansu. To wai sai yaushe talakan Nijeriya zai sha romon Dimokradiyya ne?

Kowace gwamnati haka take zuwa ta wuce ta bar lodin alkawuran da ta dauka ba tare da ta cika su ba. Cikin ikon Allah yau Allah ya kawo mana Baba Buhari wanda muna masa kyakkyawan zato matukar muka yi hakuri da juriya cikin ikon Allah zai cika mana alkawuran da ya dauka, Ya Allah Ka kara masa lafiya.

Daga Nasiru Kainuwa Hadejia (Masoyin Baba Buhari) 08100229688/09073801967

 

 • Allah Ka Bawa Baba Buhari Lafiya!

Salam gidan Jaridar LEADERSHIP  Hausa da  fatan kuna lafiya. Yau ma na shigo gidan nan naku dan neman iziniku dan yiwa shugaba Buhari Addu’a.

Tabbas, Shugaba Buhari na cikin jin jiki matuka, ya kuma kamata mu kara dukufa don yi masa addu’ar samun lafiya. Domin duk wanda ya taimaki wani ta hanya mai kyau shi ma Allah zai taimaka masa, wanda kuma ya yi fatan sharri ga wani Allah ya zai mayar masa abinsa.

Wasu na murnar rashin lafiyar Shugaba Buhari domin rashin kishin Arewa. Wadannan mutane na bin Buhari da mummunar manufa saboda rashin gaskiya da suka tabka don a ganinsu za a zakulo su da sannu-sannu, to amma in sha Allah za su kunyata, da yardar Allah Buhari zai warke ya kuma dawo bakin aiki don gyara mana kasarmu. Allah ka ba Baba Buhari Lafiya don alfarmar Nabiyyun Rahma, amin.

Na gode Leadership Hausa Allah ya kara daukaka.

Daga Ibrahim Maazu Mada Bakenawa, Gusau, Jihar Zamfara 08166494442, 07084400431

 

 • Kira Ga Gwamnonin Nijeriya

Salam Edita. Don Allah ku bani dama in yi kira ga GwamnoninNijeriya, da su yi abin da ya kamata ga al’ummarsu ganin yadda Shugaba Muhammmadu Buhari yake basu makudan kudade don yin ayyuka,  amma haka wasun su suke karkatar da kudin ta wata hanyar da ba ta dace ba. Haba Gwamnoninmu ina kuke kai hankalinku? Kun manta da cewa duk abinda kuke karba a bayyane yake? Kun mata da cewa duk abinda kuke kashewa kan albashi da ayyukan Gwamnati shi ma a bayyane yake? Wane aiki kuke yi wa al’umma da suka zabe ku kudaden da ake baku?

Haba Gwamnoninmu,  shin kuna tunanin Talakawa sun manta da irin ikirarin da ku ke yi na cewa babu kudi? To ya kamata ku gyara ko talakawa su gyara ku don kuwa gyaran shi ne canji idan lokacin zabe ya yi, da fatan wannan kira zai kai ga kunnuwan Gwamnoninmu.

Daga Sani Mohammed Chindo, Unguwar Karofin Madaki, Bauchi 08030918913

 

 • Gwamna Masari Ka Tuna Wannan?

Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina, ya kamata ka sani kyawun alkawari cikawa, kuma ana wanke tukunya ne saboda gobe. Da fatan zaka gaggauta cika wa Katsinawa dimbin alkawurran da ka daukar masu musamman na inganta rayuwar al’umma. Kamar yadda ka yi masu alwashi a lokacin da kake barar kuri’ar su, domin kuri’arsu na nan ajiye kuma 2019 na nan zuwa.

Daga Haruna Muhammad Katsina, Shugaban Kungiyar Muryar Jama’a 07039205659

 

 • Matsalar Wutar Lantarki A Hadeja

Wato ya zama kamar wata al’ada duk lokacin da watan azumi ya kama al’ummar cikin garin Hadejia mun yi ban kwana da samun hasken wutar lantarki. Hakika abin akwai takaici sai ka rasa daga ina matsalar take. Daf da za mu dauki azumi a bana mun shafe akalla kwana biyar ba hasken wutar lantarki sai labari ya bazu cewa ma’aikatan wutar lantarkin ne suke gyara hakan sai ya sanya al’umma farin ciki domin zaton gyaran da aka ce suna yi zai zama silar da za mu sami wutar a wadace cikin watan azumi. Amma kash! Muna shiga watan Ramadan sai mu ka ga azumin bara ma mun fi samun wutar akan na bana.

A gaskiya talaka na shan wahala domin duk wani kuncin rayuwa akansa yake karewa a kasar nan, gidansa janerato, wasu ma ba wutar an yanke ta saboda sun kasa biyan kudir, matsalolin dai da yawa sai dai muce Allah ya kawo mana saukinsu.

Kamfanin KEDCO (Kano Electricity Distribution Company Plc) Allah ya muku abin da kuke mana in khairan ku ga khairan idan kuma kuna kuntatawa al’umma ne da gangan don wata boyayyar manufa muna rokon Allah, albarkacin wannan wata mai alfarma Allah ya mayar maku kanku ya wargaza kamfanin ya kawo silar da gwamnati za ta kwace iko da wutar lantarkin tunda zalunci ne a zuciyarku.

Nasiru Kainuwa Hadejia 08100229688/09073801967


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI