Connect with us

WASANNI

Infantino Zai Kai Labari Kuwa?

Published

on


Kwamitin da’a na hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA, ya fara bincikar zargin da ake wa shugaban hukumar, Gianni Infantino na yin amfani da kujerarsa, wajen tasiri a kan sakamakon zaben shugabancin hukumar lura da kwallon kafar nahiyar Afrika.

Babban mai shigar da kara na Kotun wasanni da ke Switzerland Cornel Borbely, kuma shugaban kwamitin da’ar na FIFA, ya ce kaddamar da binciken, ya biyo bayan, wasu shaidu da aka gabatar musu, kan yadda Infantino ya taka rawa wajen tabbatar da an zabi Ahmad Ahmad na Madagascar a matsayin shugaban hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF watan Maris.

A ranar Lahadin da ta gabata, Jaridar the Guardian ta Birtaniya, ta rawaito wasu majiyoyi da ke cewa, kafin zabukan, Infantino da sakatariyar hukumar ta FIFA Fatma Samoura, sun yi alkawarin cewa hukumomin lura da kwallon kafa na kasashen nahiyar Africa, za su rika yin kwanciyar magirbi kan damin damasheren kudade, fiye da wanda hukumar ta FIFA ke ware musu a baya, muddin wakilansu suka zabi Ahmad Ahmad ya taka takara, ya kuma samu nasara.

Hakazalika majiyoyin sun ce Infantino ya dauki matakin ne, domin ya kawar da Issa Hayatou daga shugabancin hukumar CAF, kasancewar Hayatou bai goyi bayan takararsa ba, a lokacin da ya nemi darewa kujerar shugabancin hukumar ta FIFA.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI