Connect with us

WASANNI

Me Ya Hada Dani Da Maradona?

Published

on


Gwarzon dan wasan kwallon kafa na Argentina Diego Maradona, ya bayyana Dani Albes dan kasar Brazil, da ke kungiyar Jubentus, a matsayin Sakarai da bai san abinda yake ba.

Maradona ya bayyana haka ne cikin fushi, a lokacin da ya ke maida martani kan hirar da Albes ya yi da wata kafar talabijin, inda Albes din ya ce bai kamata a rika kwatanta bajintar Maradona a fagen kwallon kafa da Lionel Messi ba.

A cewar Albes yin satar amfani da hannu wajen zurawa kasar Ingila kwallo da Maradona ya yi, a wasan kusa da na karshe, na gasar cin kofin duniya, a shekarar 1986, ya isa abin kunya ga tsohon dan wasan, wanda kuma ‘yan baya bai kyautu su kwaikwaye shi ba, don haka, bai kamata ma ya rika gama kansa da Messi ba, domin a cewarsa ko bada kwallo bai iya ba wato passing a Turance.

Shi kuwa Maradona a martaninsa, cewa ya yi Dani Albes, wanda ya bayyana a matsayin sakarai, cikin kowane rarraba kwallo 28 da ya ke yi, yayin da ya ke buga wasa, sau hudu kawai yake samu daidai, wanda takwarorin da suka rike lambarsa a baya kamar su Cafu, da Maicon ba haka suke ba.

 

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI