Connect with us

BURIN ZUCIYA

BURIN ZUCIYA: Guzuri Ga Ma’aurata Matakan Tabbatar Da Kwanciyar Hankali Da Zaman Lafiya

Published

on


Daga Fatima Ahmad

Da sunan Allah mai rahma mai jinkai. Allah (SWT) yana fada a Suratul Rum cikin Alkur’ani mai girma, “Kuma daga ayarSa ne ya halitta daga gare ku mataye domin ku samu natsuwa daga gare su kuma ya sanya tsakaninku kauna da tausayi hakika wannan aya ce ga ma’abota hankali.”

Wannan aya ta tattare duk wani ma’ana na aure a cikinta saura namu mu farfasa mu auna mu gani shin ma’anar aure da abin da yake cikinsa kuwa kaman yanda Allah ya nuna mana hakan muke yi.

Da farko Allah ya ambaci Ma’aurata da ababen samun nutsuwa duk da a nan Ya kawo jinsin mata ne. To amma ai mun sani idan har macen ba ta samu natsuwa ba, shi kansa namijin natsuwarsa ragaggiya ce. Tambaya a nan TA INA MA’AURATA ZA SU SAMI KWANCIYAR HANKALI?

Na farko a samun natsuwar aure shi ne hadafin yinsa. Bai taba yiwuwa aure ya kasance an gina shi kan wani hadafi sannan ya zamo dorarre. Wannan shi ya sa Annabi (SAW) bayan ya zayyano kaso na matan da ake aure, karshe ya ce “Na hore ku da ma’abociyar addini.”

To hakika abun nufi a nan shi ne ba wani hadafin da zai haifar maka da cikakkiyar kwanciyar hankalin aure sai hadafin tarayya domin Allah. Gina auren don Allah, zaman auren don Allah. Hakuri da juriya da tabbatar da cewa ibada ce daga bangaren miji har mata idan ta batama ka tuna matan Annabi (SAW) sun bata masa sai ka danne. Haka ita ma mace komai za ta gani a aure ta sa ibada take, ta hakure domin Allah to hakika wannan shi ne jigon samun natsuwar Aure.

  1. Sanin Hakkin juna: Jigo na biyu a cikin aure mai kawo natsuwa kenan. Hakika a yau mun yi sake tare da wasarairai da hakkin junanmu ta yanda ta kai har wasu abubuwan ma an shafe su daga rayuwar aure sai a wajen mutane jefi-jefi. Daga hakkokin auren kuwa shi ne:

 

  • Bangaren Namiji:

Hakkin ciyarwa dole ne ya fita ya nema ya ciyar da iyalinsa tare da adalci abun nufi ba ya kasance don an ce ya ciyar da su ba ya fita ya ci mai dadi, ya kawo musu ci-kar-ka-mutu.

Na biyu hakkin tufatarwa wannan Musulunci ya masa rangwame da ya kawo daidai karfinsa kuma ba a ce tilas koyaushe ba, amma akalla kar ya bar iyali cikin tsiraici. Na uku, hakkin matsuguni hakkinsa ne ya nemawa iyalinsa matsuguni mai aminci abin nufi wanda za su rayu ciki da aminci ba tare da tunanin za a iya cutar da su cikin sauki ba.

 

  • Bangaren Mace:

Na daya kula da gida, kula da yara, yi masa biyayya gwargwadon yadda ba za ta sabi Allah a ciki ba, wato duk abin da yake so, ta so shi, kuma duk abin da yake ki ta ki shi, matukar bai sabawa Ubangiji ba.

 

  • Bangaren Tarayyarsu: Kiyaye hakkin juna ta wajen ayyuka. Da yawa mu kan yi ayyukan da muka san abokin zama bai so amma muna ganin bai wani abu ba ne mu sani cewa ire-iren wadannan ayyukan duk kankantarsu kan jawo rikici, wanda ke sabbaba rashin natsuwa a rayuwar aure ba tare da mun ankara ba.

Misali maigida kan dauki al’adar zaman waje hirar dare wanda da yawa yakan taba zuciyar iyalinsa domin yawancin mata ba su cika son wannan ba. Hakika irin wannan kan haifar da rashin natsuwar mace tattare da mijinta wanda ke haifar da shaidan yai ta mata kulle-kulle sai ka ga kananan sauyi na bullowa a zamantakewa har ya jawo abin da ba a fata.

Haka bangaren mace da yawa za ka ga miji bai cika son ta fita ta kai dare ba, amma wata duk sanda ta fita sai ta kai, wanda hakan ma kan jawo kace nace har ka ga aure ya rasa hadafin da Allah ya halatta shi domin sa wato natsuwa.

Amma na biyu a bangaren tarayya shi ne: Hakkin lafazi, hakika mun manta da wannan a zamantakewar aure na yanzu. Za ka ga namiji da mace ta yi kuskure kadan ya kama fada tare da furta kalmar da duk ta zo bakinsa yayin da ita ma dan ta rama sai ta yi kokarin kwabo mara dadi wadda in ba a yi sa’a ba, ko da an gama fadan nan ma’ana an huce, shaidan zai yi ta tariyo masu maganganun juna sai ka ga an kullaci juna daga haka sai ka ga aure ya rasa natsuwa da kyakkyawan matsaya.

Hakkin kwanciya ko mu’amalar aure: Na taba jin wani shaihun malami yana bayani a kan haka ya ce ka so mafi yawa na aure na mutuwa ne sakamakon take hakkin juna wajen mu’amalar aure. Wanda shi ma dole ya zamo yana da kaso kamar haka: Hakkin juna wajen kula da yanayin lokacin mu’amalar musamman ga bangaren maza. Da yawa ba su lura da yanayin da matar ke ciki kan su kawo bukatarsu domin akwai lokutan da mace kan tsinci kanta cikin rashin lafiya ba jiki ko rashin kuzari ko bacin rai musamman yayin da take cikin satin da al’ada za ta zo mata wasu matan kan kasance cikin yanayi na fushi ko kasala. Wanda a irin haka in ba a yi sa’a ba, in namiji ya zo da bukatarsa, sai ta ki, a nan idan aka yi rashin sa’a sai ka ga an samu matsala, daga haka aure ya rasa kyawun yanayi.

Halin da za a kasance kafin mu’amalar ma’ana a nan kula da tsabta daga dukkansu su biyun dole su tabbatar da sun kauda duk wani abu da zai cutar da dayansu yayin mu’amalar. Misali kula da wanke baki hammata kyakkyawan tsarki da sanya turare mai sanyi ba mai karfi ba domin karya cutar da abokin mu’amala. Hakika rashin kula da wannan zai iya jawo a rika dardar wajen nuna bukata wanda kuma shi ma hakan wani wawakeken gibi ne a rayuwar aure wanda ke tarwatsa nutsuwar cikinsa.

Babban hakki na kula da gamsuwar juna. Bana tantama cewar zaa iya yarda da maganata in na ce a cikin kaso 100 na auren dake mutuwa sakamakon nakasu na mu’amalar aure, kaso 99 rashin sanin hakkin juna ne ta fannin gamsuwa. Duk da mata sun fi kokawa wajen rashin kula da hakkinsu na gamsuwa amma mazan ma na kokawa ta wannan fannin. Dole ne hakkine a kanka da kanki ku zauna ku fayyacewa juna nakasun da kuke fuskanta yayin mu’amalar aure. kai namiji karkace inka samu biyan bukata ka gama haka ma macen kar tace kunya take ji ba za ta fada masa ba ta samu biyan bukatarta ba. Domin in har za a tafi a haka, to tabbas wannan aure ba zai samu daidato ba bare natsuwa.

Amma bangare na uku a samun natsuwar aure shi ne tarbiyyar yara: Hakika duk gidan da yaran cikinsa suka zamo masu nakasu wajen tarbiyya to wannan gida natsuwarsa mai karanci ce. Dalili akan hakan shi ne da yawa gida in yaran gidan ba su samu kyawun tarbiyya ba za a rika zargin juna tsakanin iyayen shi uba ya rika ganin laifin uwa ne. Ita ma tana ganin nasa. Da sannu za ka ga kwanciyar hankali da natsuwa ta kaura daga wannan iyali.

Hakuri da jarabawar da aka tsinci kai a zaman aure daga namijin har mace. Tabbas wannan ma wani jijjige ne a samar da natsuwar aure. Allah zai iya jarabtar auratayyarku da samun matsaloli na karancin abun hannu ko rashin lafiya daga daya bangaren ko daga yaranku ko matsalar dangi ta kowane bangare walau na mijin kona matar. Hakika idan ya kasance ba a samu hakuri da tawakkali ba. Aure zai zama kawai zamane ake yi ba natsuwa tare da shi.

A kalami na gana sai ubangiji  (SWT) Ya ce: “..kuma muka sanya tsakanin kauna da tausayi…” To mun ga a nan ashe natsuwa ita ke jagortar kauna da tausayi har a samu zaman lafiya a aure.

Hakika ‘yan’uwa muna tafka kuskure wajen daukan wasu abubuwa a aure a kan suke samar da zaman lafiya. Mu sani a cewa ba wani zamananci ko al’ada da zai wanzar maka da zaman lafiya a auratayya face an gina shi a kan tsarin da za a samu natsuwa a cikinsa. Natsuwar kuwa dole ta kasance daga kowane bangare ma’ana duka bangaren biyu sun hada kai don samar da ita.

Inda za mu koma mu kalli zaman magabatanmu za mu fuskanci ba komai muke ba a zaman aure face dambarwa. A yau ‘yan bana-bakwai sun dage a kan cewa aurensu shi ne auren ‘yanci ka-ganni-kana-so, na-ganka-ina so!

An yi aure irin na soyayya kaman a lashe juna to amma sai ka ji ko shekara ba a rufa ba, an fara gajiyawa da juna kowanne ka zaunar da shi sai ya rubuta maka littafi guda na laifin dan’uwansa. Mace-macen aure sun yawaita har ya kasance duk wanda ka raba, sai ya ce ma yana tsoron aure. Shin ina yancin? Amsa ita ce an manta tsari da hujjar auren ne an tafi ga abu daya wato jin dadi. Kowanne bangare na ganin dole dan’uwansa ya kyautata masa ba tare da tunanin shi ma hakki ne a kansa ya kyautata din ba.

Fatana Ubangiji (SWT) Ya ba mu zaman lafiya, Ya kuma ba mu ikon kiyaye hakkin juna a wannan Sunna mai karfi. Ya kuma ba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikinta domin mu samu lagwadar samun natsuwa da junanmu.

Mu hadu a mako mai zuwa da yardar Allah. Bissalam.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI