Connect with us

FAHIMTA FUSKA

FAHIMTA FUSKA: Sheikh Ibrahim Khalil

Published

on

A aiko da tambaya ta wadannan imel: [email protected] ko [email protected] ko kuma sakon ‘tedt’ ta wannan lamba domin Malam ya amsa tambaya: .

Malam, tun ina firamari na ke son wani saurrayi nawa, to amma sai iyayena su ka yi mi ni auren dole da wani tsoho. To, bayan auren ne ni ba na gamsuwa da shi. Hakan ta sa na ke zuwa gurin wancan saurayin nawa a karshe muka samu ’ya’ya. Bayan wani lokaci sai wannan tsohon ya m utu na kuma auri wannan saurayin. Malam, ’ya’yana za su gaji wancan mijin na farko ko na biyun za su gada?

Abu na farko dai wajibi ne a gare ki ki roki Allah gafara da rahamarSa. Kuma ki yi ta rokawa tsohon mijinki gafara har tsahon rayuwarki. Kuma ki nace wajen yin sadaka da ayyukan alheri da sallar nafila, domin ki samu rahamar Allah.

Abu na biyu; wadannan ’ya’ya zasu gaji babansu, kuma su na da hakkin wannan gado, don babu wani dalili da zai tabbatar da cewa ’ya’yansa ne ko ba ’ya’yansa ba ne. Don ki na saduwa da wancan kuma ki na saduwa da mijinki ba dole ba ne ya zama wannan shi ne ya yi cikinsu. Zai iya zama mai gidanki ne, zai iya zama wancan. Ala’aiyi halin dole ne ’ya’yanki su na da gado.

Abu na uku da zan gaya miki shi ne, kada ki yarda ki sake wannan zance ga wani mahaluki a duniya. Abu na hudu da zan fada shi ne, wajibi ne a kan iyaye da su rika la’akari da ’ya’yansu, kada su rika tilasta su su auri wanda ba sa so. Kuma lallai ne da a rika la’akari da dabi’a ta dan adam, musamman ’ya mace har ma shi da namiji. Amma ita mace wajibi a rika la’akari da dabi’ar rauninta da cewa duk lokaci a ka ce ga wani saurayi ta na so, to a ba ta wannan saurayi sai fa idan an ga wata matsala muhimmiya wacce dole a yi ma ta bayani kuma a nuna ma ta illarta. Shi ya sa kullum mu ke kira ga iyaye su zama su na kokarin dasa soyayyarsu a cikin zuciyar ’ya’yansu tare da ganin girman iyayensu da kuma jin cewa iyayensu ne su ka fi kowa son su. Wannan zai zama duk lokacin da su ka bijirowa ’ya’yan da wani abu, to za su karbe shi ko da ba sa son sa cikin jin dadi saboda sun san cewa ba su da wanda ya ke son su kamar iyayensu. Sannan kuma mu na kira ga al’umma bakidaya cewar su taimaka wajen bawa mutane goyon baya na yin abinda ya ke shi ne daidai.

 

Malam, ni mace ce mai kishi, mijina ya na son zai auri wata kawata, sai na hau haukan karya. Sakamakon haka sai ya fasa auren ta. To, ashe su na can su na mu’amalarsu har a ka samu ciki. Malam Ina da laifi?

Wato na farko dai ita mace babu abinda ya ke bata ma ta rai ya tayar ma ta da hankali kamar mijinta ya ce zai auri kawarta. Duk mace ba ta son wannan. Don haka wajibi ne maza su yi la’akari da wannan cewar su daina kokarin su ga sun auri kawayen matansu. Halal ne a Shari’aH, amma ya na hana zaman lafiya tsakanin matar da a ka aura da wadda za a auro. Sannan kuma ya na sa kishi ya yi zafi har karshen rayuwarsu. Wani lokaci ko ya sa daya ta fita, musamman uwargidan, domin ita mace ta na ganin wulakanci ne da kuma cin mutunci a auri kawarta. Haka nan ta na ganin cewa ita kawar tata ta ci amanarta. Don haka wajibi ne maza su fahimci wannan.

Amma ke da ki ka yi haukan karya, wannan ba zai sa a kama ki da laifi na haukan karya da ki ka yi ba, domin ki na neman mafita ne. Amma su kuma da su ka koma su na kula junansu a boye sun sabawa Allah. Wajibi ne su roki Allah gafara da rahama. Ke kuma ba za a kama ki da zunubi ba, saidai ki cigaba da rokon Allah gafara da rahama domin ba a san mai zai je ya dawo a kanki gobe ba. Don haka ki yi ta rokon Allah gafara dangane da abinda ki ka yi na kokarin kare kanki, wanda ya zama sababin mijinki da wannan mata su ka aikata sabon Allah.

Malam, a gaskiya ni Ina da karamin zakari. To, yaya zan yi na rika biyawa iyalina bukata?

A’a, ba za a ce ka na da karamin zakari ba sai ka duba kanka; idan ya zamana idan zakarinka ya tashi ba ya wuce girman karamin dan yatsan hannunka na karshe, to wannan shi ne karamin zakari. Amma idan ya zamana idan zakarinka ya tashi ya na iya kaiwa tsawon daya daga cikin ’yan yatsunka na tsakiya guda uku, to ba karamin zakari ne da kai ba. Sai dai kawai ka nemi magani da zai kara ma ka karfin namiji… To, idan kuma ya zamana idan zakarinka ya tashi ba ya wuce karamin dan yatsan naka wanda cindo ya ke iya fito ma ka, to akwai magani da za ka iya nema wanda ya ke sa zakari ya karu.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: