Connect with us

MANYAN LABARAI

RAHOTO: ‘Ya Kamata Hukumar Hajji Ta Rage Kudin Kujera’

Published

on


Daga Ibrahim Ibrahim, Kaduna

An bayyana cewa zaman lafiya shi ne babban burin kowace al’umma a duk fadin duniya kasancewar babu abin da ya kai shi dadi a zamantakewa.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Garguwan Matasan Arewa, kuma Shugaban Rikunonin Kamfanin Jili and Son’s, Alhaji Usman Aliyu Jili, a yayin da yake zantawa da manema labaru a Kaduna.

Garkuwan na Matasan Arewa ya bayyana irin takaddamar da ta kunno kai tsakanin Matasan Arewa da na Kudancin Kasar nan a matsayin abin da ba zai haifar ma Kasar nan Da mai ido ba. Domin a cewar sa, Nijeriya Kasa ce dunkulalliya, mai dimbin arzikin albarkatun kasa, mai dauke da jin sin Al’umma kala kala.

Alhaji Usman Jili, ya kalubanci Matasan yankin Arewa da kuma na Kudancin kasar nan da cewa, lokaci ya yi da kowannen su zai kwance damarar da ya daura, domin ganin an zauna a teburin sulhu domin samun maslha.

“Ina mai tabbatar maka da cewa, duk mutumin da yake kokarin tayar da fitina Allah na yin fushi da shi. Saboda a kullum ita fitina a kwance take, amma wasu ne ke tayar da ita. Shiyasa Allah da kansa ya ce ya la’ancin mai tayar da fitina.”

“Duk kasar da babu zaman lafiya, wannan kasar na cike da raunin tattalin arziki, sannan Allah na yaye albarkarsa kacokan daga cikin wannan kasa.  Sannan tattalin arzikin wannan kasar ragagge ne.”

Garkuwan na Matasan Arewa ya yi kira da babbar murya ga shugabannin yankin da abin ya shafa da su gaggauta shawo kan wannan lamari tun kamin abin ya kazanta.

Garkuwan na Matasan Arewa, ya bi sauran takwarorin al’ummar kasar nan wajen yin kira ga Hukumar Aikin Hajji ta Kasar nan da cewa, su dubi girman Allah su rage Kudaden da suka ayyana na kudin aikin hajji, domin a cewar sa, mutane da damar gaske na son zuwa don sauke farali, amma saboda karin kudin kujerar akin hajji, dole ta sanya su su hakura saboda halin matsayin tattalin arziki da kasar ke fuskanta.

“Ina kira ga Hukumar aikin hajji da Gwamnatin Tarayya, akan su duba lamarin kudin kujerar aikin hajji, domin tsakani da Allah kudin ya yi  matukar yawa sosai duk da suna danganta hakan da tashin farashin dala a Kasar nan. Amma koma da menene, rage farashin kudin kujerar aikin hajjin shi ne hanya mafi inganci wajen tausayawa masu karamin karfi.”

Da kuma ya juya ga cikan gwamnatin APC shekara biyu a bisa kujerar mulki. Alhaji Usman Jili, ya bayyana irin dimbin nasarorin da gwamnatin Shugaban Kasa Buhari ta samu a cikin shekara biyu kacal, a matsayin abin a yaba mata.

“Gaskiya a cikin shekara biyu kacal na gwamnatin mai girma Shugaba Buhari, ya sami dimbin nasarori da ba za su musaltu ba, musamman idan akayi la’akari da yadda ya sami Kasar nan cikin mawuyancin hali, tattalin arziki ya durkushe, matsalar tsaro ya kazanta, ga  babu ingantaccen tattalin arziki.”

“Amma cikin ikon Allah bai wuce shekara daya a bisa mulki ba, har kar tsaro ya inganta, tattalin arzikinmu ya farfado fiye da shekarun baya, sannan uwa uba, shi ne yadda ya jajirce wajen yaki da kawar da cin hanci da rashawa a fadin Kasar nan. Gaskiya ko haka nan aka tsaya Shugaba Buhari ya ciri tuta.”

Daga karshe Garkuwan na Matasan Arewa ya yi kira ga ‘Yan Nijeriya da su kara dukufa wajen yima Shugaban Kasa Buhari addu’ar samun cikakken koshin lafiya domin samun ikon tafiyar da ragamar shugabancin kasar nan cikin kwanciyar hankali.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI