Connect with us

SANA'A SA'A

SANA’A SA’A: Sirrin Citta Da Tambayoyin Masu Karatu

Published

on

Kamshin citta da dandanonta yana kara kamshi na  daban mussaman a cikin kayan marmari ko miyar ganye.

Citta na taimakawa a wajen bada kariya da yawa ta wajen iskar da ke shiga cikin hanji.

Sannan tana kare cututtuka kamar jiri, amai da kuma gumi.

Tana kare mace mai dauke da ciki daga yawaitar yin amai don an tabbatar da mata 19 daga cikin 27 kan kamu da amai yayin da suke da karamin ciki da bai gaza sati 20 ba, ba kamar sauran magunguna da ake baiwa masu ciki don tsayar musu da amai ba, wani lokacin akan samu yana da matsala yayin haihuwarsu amma citta

Ba ta da matsala kuma kadan ake bukata a sha.

Ga masu fama da ciwon gwiwa ko kafa don shekaru sunja sai a rinka hada citta a cikin abinci ko abin sha ana ba su zai taimaka musu sosai.

A wani bincike da aka yi an gano cewar maza 126 da mata 23 wadanda shekarunsu ke tsakanin 42 zuwa 85, na fama da matsanancin ciwon gwiwa wanda sanyi ke haifar da shi,  a halin yanzu suna samun sauki sakamakon amfani da ctta.

 

Amsoshin Tambayoyinku

Assalamu alaikum ‘yan uwana da fatan mun yini lafiya? Ya ya yara ya ya hidimomin yau da kullum? Allah Ta’ala Ya sa mu gama lafiya, amin ya rabbi.

To yau dai ina so na sauke nauyin da yake kaina, na yawan tambayoyin da mutane suke turomin. Za ku min hakuri na amsa masu. Sati mai zuwa sai mu i bayani kan wani abin.

 

Tambaya: Assalamu alaikum malama Jumai ina godiya da abubuwan da ki ke taimaka mana da su, amma na ka wo kukana gare ki da fatan zaki taimaka min. Matsalata ita ce, ba ni da sha’awa, kuma ba na gamsar da mijina don Allah malama Jummai ki taimaka min. Na bar ki lafiya. Daga Faiza daga Gombe.

 

Amsa: Mallama Faiza matsalarki ba wani abu bane mai wahala, kina da damuwa ko bacin rai ko kuma kina fama da kaikayin gaba, kila sune suke sanya mki rashin sha’awa, kuma duk in da babu sha’awa to babu maganar gamsarwa.

Idan har kina da ciwon kaikayin gaba to ga maganinsa. Ki samu zuma mai kyau da garin tafarnuwa, kistul hindi, garin zaitun, garin zogale, sai ki hada su waje guda, ki rika shan cokali 3 safe da yanma, har tsawon sati guda insha Allah za ki rabu da wannan cuta har abada, ki je Islamic Chemist duk akwai wadannan kayan hadin.

Idan kuma ba shi bane to ki samu kanumfari daidai kima ki tafasa,  idan kin sauke,  ki juye a kofi ruwan ki sha, sannan ki yi tsarki da shi, amma fa sai kin daure za ki iya sha. Idan ki ka daure yana saurin dawo da sha’awa. Allah ya bada sa’a.

 

Tambaya: Assalamu alaikum zuwa ga malama Jummai, don Allah ki taimaka min kamar yadda Allah ya taimake ki. Mijina ne ba damu da ni ba, kuma baya mu’amula da ni sai idan zai biya bukatarsa. Shi yasa nake neman taimakon ki. Daga mamman Amira Bauchi.

 

Amsa: Maman Amira ki yi hakuri, komai ya yi farko tabbas zai yi karshe. Ki yi ta addu’a ki na fadawa Allah. Shi kuma Allah ya shirye shi. Maza ku ji tsoron Allah, domin duk abin da ku ke yana kallon ku.

Tambaya: Auty Jummai  ni budurwace amma mamana haka kawai ya zube, kuma ina neman maganin tumbi da narkanwa don Allah.

Amsa: To malama ba ki sanya sunanki ba, kuma wannan larura taki ga dukkan alamu, yana yin halitan ki ne ya canza, shi ya sa suka zube, don ko kwanaki baya na bada magani akan masu shayarwa, amma ke ki yi hakuri, saboda ke budurwace, Allah ya baki miji na gari.

 

Tambaya: Assalamu Alaikum anty Jummai da fatar kina lafiya. Ni kuma matsala bana jin sha’awa, ko da kuwa muna saduwa da mijina, sai da na yi ta daurewa, na rasa wanda zan tunkara da batun. Cikin ikon Allah, ina karanta LEADERSHIP Hausa sai na ga filinki na sana’a sa’a. Ki ba ni shawarar. Ki ki huta lafiya.

 

Amsa: To malama ke ma ba ki sanya sunanki ba. Ki duba sama, akwai amsar dana baiwa Faiza, ki yi irin sa, In Sha Allah za’a dace. Allah ya bada sa’a.

 

Tambaya: Asslamu anty na Jumai an tashi lafiya anty na ni matar aure ce amman na kasance mai damuwa akan mijina wallahi bansan meye matsalataba sai mu hada wata babu wata alaka tsakaninmu. Sadiya KT.

 

Amsa: Malama Sadiya ki zaunar da shi kiji dan yana da wani damu wa ne ta haka zaki san hanyan da yakamata kubi don gyara.

 

Tambaya: Salam Malama Jummai ina so ki fada min abin da zan yi gabana da kuguna su fito, domin mai gidana yana so, ni kuma ba ni da su. Daga TMS KT.

 

Tambaya: Salam! Ya gida ya aiki anty ya zan gyara gabana duk lokacin da miji na zai sadu dani ya rika ji kamshi, kuma ni’imata ta wadatu? Ya zan y mamana su ciko su mike don sun fara faduwa. ga shi maigidana yana son ganinsu a mike, anty ni mace ce mai son gamsar da mininta, don kar ya wutakantani,  ko aure na ya mutu.

 

Amsa: TMS KT. Ba ki sanya suna ba, amma zan ba ku amsa daya ke da wadda take samanki. Idan mace tana so idan mijinta yana saduwa da ita kamshi ya rinka tashi, sai ki nemi; miski, ambar, ganyen magarya, rihatul hubbi, zamzam, ma’ul ma’i. sai ki hada su guri guda a kwano, sai ki dan tafasa su, ya yin da ya huce sai ki nemi buta mai kyau ki zuba, sai ki kara masa ruwa, duk lokaci da za ki tukarar maigida, sa ki yi tsark tare da shashafewa a cinyoyinki, wannan zai hana mijin ki ya gujeki, za ki ga yadda zai rika nuna dokinsa a kanki.

Ga kuma wani sirrin gyaran nono. Ku samu; aya, gyada, plantain, alkama da madara. Za ku surfa ayar ku wanke kamar za a yi kunun, aya sai ku sami gyadar ku hada ku kai a markada muku.

Sai ku tace, sai kuma ku samu plantain danye wanda bai gama nuna ba, shi kuma za ku yanka shi kanana ku sannan ku shanya har ya bushe, sai ku kai injin nikan gari ku nika ku tankade, sai alkama shi ma ku nika ta, iya hadawa da busashen plantain din sai ku tankade ku debo tacaccen ruwan ayar da gyada ku zuba madarar gari a ciki, sai ku debo garin plantain din da alkama ku zuba daidai kima kamar yadda za ku iya sha, sai ku juya ya kauri sai ku sha kamar sau biyu a rana.

In Sha Allah kirji zai cika ya yi kyau. Allah ya bada sa’a.

Tare da

Jummai Ibrahim
GSM: 08097160554 (tes kawai)
[email protected]
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: