Connect with us

MANYAN LABARAI

BABBAN LABARI Nijeriya Ta Yi Babban Rashi


A ranar Litinin din makon nan, 3 ga watan Yuli 2017, al’ummar Nijeriya suka yi gari da labarin rasuwar tsohon dan takarar Shugaban Kasa karkashin tutar jam’iyyar NPN, Alhaji Yusuf Maitama Sule


Published

on


  • Ina Da Masaniya Game Da Rashin Lafiyarsa – Buhari •Nijeriya Ta Yi Babbar Asara – Osinbajo
  • Ya Kamata A Samar Da Dandalin Tunawa Da Shi – Saraki •Rashi Ne Ga Afrika Baki Daya – Yakubu Dogara
  • Kullum Burinsa Hadin Kan Nijeriya – Tambuwal •Mun Yi Rashin Uba Nagari A Siyasa – el-Rufai
  • Masari, Kaita Da Danmusa Sun Jajanta Wa Al’ummar Kano •Abubuwan Da Ba A Sani Ba Game Da Shi

Daga  Mubarak Umar da Umar Faruk Abdullahi da Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

 

A ranar Litinin din makon nan, 3 ga watan Yuli 2017, al’ummar Nijeriya suka yi gari da labarin rasuwar tsohon dan takarar Shugaban Kasa karkashin tutar jam’iyyar NPN, Alhaji Yusuf Maitama Sule, wanda ake yi lakabi da Dan Masanin Kano, lamarin da ya jefa jama’a cikin dimuwa da damuwa sakamakon wannan babban rashi.

Maitama  Sule ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Cairo na kasar Egypt bayan ya yi fama da gajeriyar rashin lafiya, kamar yadda dansa Mukhtar Yusuf ya shaida wa manema labarai cewar, an fara kai shi Asibitin Nasarawa da ke Kano sakamakon tsananin ciwo da kirjinsa yake yi, kafin daga bisani likitoci su bada umarni ficewa da shi kasar waje.

Babban Mataimaki na musamman ga marigayin, Alhaji Sharu, ya shaida wa wakilinmu tsohon ministan ya rasu a lokacin da yake kokarin fitar da matsayarsa kan rikicin ballewa daga Nijeriya da kabilar Ibo ke yi da kuma hanyoyin da za a bi wajen magancewa.

Wakilinmu ya samu ganawa da Danmasani kwana daya kafin rashin lafiyar ta tsananta, inda suka so tattaunawa washegari (Asabar) kan batun raba Nijeriya, sai dai a daren ranar da misalin karfe biyu na dare aka garzaya da Maitama Sule Asibitin Nasara kafin daga bisani su wuce Egypt, inda Allah ya dauki ransa a can.

Daya daga cikin ‘ya’yansa Abdulkadir wanda yake jinyarsa a asibiti shi ne ya bugo da safiyar Litinin ya sanar da sauran ‘yan uwansu labarin rasuwar mahaifin nasu ta wayar tarho.

A wata tattaunawa da manema labarai suka yi da Mukhtar Maitama Sule, daya daga cikin ‘ya’yan marigayin. Ya shaida cewar: “Da safe, kanina da yake tare da shi a al-Kahira ya bugo min waya ya sanar da ni.”

Da yake magana kan irin gibin da aka samu, Mukhtar ya ce: “Hakikanin gaskiya ba zai misaltu ba, saboda ni abokina ne shi. Abokantaka muke yi da shi. Babu irin maganar da bama yi da shi. Ya bani dama na mu’amulla kwarai da gaske. Domin tun lokacin da ya sami larurar ido ya ce da ni, na dauke kamar abokinka, ba shi da mutum kamar ni, inda ya nuna min cewar lallai in rika kasancewa da shi a koda yaushe.”

Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagoranci Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta ayyana Talatar da ta gabata a matsayin ranar hutu domin girmamawa ga marigayi, wanda aka yi masa sutura bisa tsarin da addini Musulunci ya shimfida da misalin karfe 5:25 na yammacin Talata, 4 ga watan Yuli, 2017.

Wannan Hutu ya samu ne domin alhinin mutuwar Danmasanin Kano da  jimamin rasuwar tsohon ministan mai, Alhaji Maitama Sule. Kamar yadda Mataimakin na musamman ga sha’anin yada labarai na gwamnatin Kano, Salihu Tanko Yakasai ya bayyana.

Gawar Dan masanin Kano ta iso filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu dake Kano da misalin karfe 4:20 na yammacin ranar Talata. Daga nan ne kuma aka dunguma da gawar zuwa gidan marigayi dake Dawaki Road a unguwar masu hannu da shuni dake Nasarawa domin yin bankwana da iyalansa. Bayan an fito dashi ne aka wuce zuwa fadar sarkin Kano, Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II shi ne ya jagoranci ya sallatar gawar Dan masanin Kano. Bayan idar da sallar ne aka dauki gawar zuwa makabarta Wali mai geza dake kusa da babbar mayankar Kano kan titin Gwammaja kusa da kofar Mazugal inda aka yi masu sutura kamar yadda kafin mutuwarsa ya yi wasiya.

A cikin wadanda suka shaida Jana’izar Dan Masanin Kano akwai Tawagar Gwamnatin Tarrayya wadda Abba Kyari ya jagoranta, sai kuma Shugaban Dattawa, Dakta Abubakar Bukola Saraki, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, Alasan Ado Doguwa, Ministan Harkokin cikin Gida Abdurrahaman Bello Dambazau, Ministan tsaro Mannir Dan Ali da kuma Abdurrahama Kawu Sumaila, haka kuma akwai Gwamnoni dasu akayi dakon isowar Gawar Dan masanin na Kano dasu, akwai Gwamna Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Aminu Waziri Tambuwal Gwamnan Sokoto, Kashim Shettima na Borno da kuma Alhaji Badaru Abubakar na Jigawa, sai Kuma Sardaunan Katsina Alhaji Ibrahim Kumasi da shararren dan Kasuwar nan Alhaji Aminu Dantata shima ya halarci jana’izaar Dan Masanin Kano.

A bangaren Sarakuna kuma akwai sarkin Dutse, Sarkin Gumel, Sarkin Kazaure da kuma sarkin Hadeja duk daga Jihar Jigawa. Haka suma tsofaffin ambasadoji da yawa suka halarcin jana’izar Dan Masanin Kano.

 

  • Ina Da Masaniya Game Da Rashin Lafiyarsa — Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu da yake jinya a birnin Landan na kasar Ingila, ya aike wa da Gwamnatin Jihar Kano sakon ta’aziyya ta bakin mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu inda ya bayyana rasuwar Danmasani a masayin babban rashi, ga iyalansa kadai ba, baki dayan al’ummar Nijeriya za su yi jimamin rashin wannan bawan Allah dan kishin kasa.

Har ila yau, Shugaba Buhari ya ce duk da yana da labarin rashin lafiyar Maitama Sule a kai a kai, amma rasuwarsa ta zo masa cikin bazata.

Shugaban Kasa, Muhammad Buhari ya tabbatar da cewa yana da masaniya game da halin rashin lafiya da Marigayi Maitama Sule ke ciki kafin Allah ya karbi ransa inda ya nuna cewa a kodayaushe ya sadu da marigayin yana matukar karuwa da shawarwarinsa.

Shugaba Buhari ya ce marigayin na daga cikin Dattawan da ke kishin ganin Nijeriya ta ci gaba a maimakon fifita bukatun kansa. A karshe Shugaba Buhari ya jajantawa iyalan marigayin da kuma gwamnatin Kano a kan wannan Babban rashi.

“Na samu labarin rasuwar dan kishin kasa Dakta Yusuf Maitama Sule Danmasanin Kano, ina da masaniya yana fama da rashin lafiya, amma rasuwarsa ta zo min cikin bazata. Tabbar Nijeriya ta yi babban rashi.

“Lokacin da yake Minista a Jamhuriyya ta farko, ya taimakawa iyayen kasa irin su Dakta Nnamdi Azikiwe, Cif Obafemi Awolowo, Alhaji Ahmadu Bello da Alhaji Abubakar Tafawa Balewa wajen gina kasar nan kan tafarki da za mu amfana.

“Allah Ya albarkaci Maitam Sule da zazzakar murya mai fitar da sako cikin hikima da basira. Ya hidimtawa kasar iyakacin iyawarsa lokacin da ya zama ministan tama da da karafa, amma ba a taba zarginsa da laifi guda daya bat un daga lokacin da ya fara gwagwarma.” A cewar Shugaba Buhari.

Har ila yau, Muhammadu Buhari ya ce: “Zan yi amfani da wannan dama in taya Gwamnatin Kano, iyalai, ‘yan uwa, abokan arziki, al’ummar Kano da ma Nijeriya baki daya bisa wannan babban rashi da muka yi.”

 

  • Nijeriya Ta Yi Babbar Asara — Osinbajo

Mukaddashin Shugaban, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana rasuwar Yusuf Maitama Sule Danmasanin Kano a matsayin babban gibi wanda zai yi wahalar cikewa nan kusa.

A wata takarda da ya fiyar ta hannun mai magana da yawunsa, Laolu Akande, Farfesa Yemi Osinbajo ya dangantaka Maitama Sule da kogin ilmi wanda Nijeriya take kwankwada daga gare shi, saboda haka rashinsa a daidai wannan lokaci ba karanar asara ba ce.

“Na kidime matuka da na samu labarin rasuwar Danmasanin Kano, wanda a baki dayan rayuwarsa ya sadaukar da komai nasa domin ci gaban Nijeriya. Hakika duniya ba za ta manta da irin gudunmawar ya bawa kasarsa a lokacin da yake wakili a Majalisar Dinkin Duniya.”

Ya ce Danmasani ba ya yin nawa wajen ganin ya furta kalmar da za ta ilmantar da mutane musamman kan sha’anin da ya shafi hadin kan kasa da ci gabanta. Har ila yau, yana tsayawa tsayin daka wajen bada shawarwarin da za su amfani Nijeriya da al’umar cikinta.

A karshe ya roki iyalai, ‘yan uwa da abokan arziki da su yi hakurin wannan rashi, domin abubuwan da Maitama Sule ya yi lokacin da yake raye, al’ummar Nijeriya ba za su taba mantawa da shi ba.

 

  • Ya Kamata A Samar Da Dandalin Tunawa Da Shi — Saraki

Shugaban Majalisar Dattawa, Alhaji Abubakar Bukola Saraki, ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kano da su samar da wani bigerwa na musamman domin tunawa da Alhaji Yusuf Maitama Sule, Danmasanin Kano.

Saraki ya fadi hakan ne ta bakin mai magana da yawunsa, yusuph Olaniyonu, inda ya ce hakika Nijeriya ta yi babban rashin wanda ya haifar da gibi mai wuyar cikewa, saboda haka ya dace Gwamnati ta samar da abubuwa wadanda za a rika tunawa da shi.

“Labarin rasuwar Danmasanin Kanio ya girgiza ni sosai. Hakika mun yi rashin uba a siyasa, wanda ya bada lokacinsa don gina kasar nan bisa tafarki nagari, ya zama Minista tun lokacin yana da kuruciyar, amma hakan bai hana shi bada gudunmawa ga ci gaban Nijeriya ba.”

Bukola Saraki ya jadaddawa cewar Maitama Sule mutum ne mai kima da daraja a tarihin Nijeriya, dan kishin kasa wanda ba shi da tsaro wajen tsage gaskiya komai dacinta, ya yi amfani da muryarsa mai tattare da hikima don ganin ya furta kalamai wadanda za su hada kan Nijeriya. Saboda haka ya bukaci al’ummar da suke raye yanzu da su yi koyi da kyawawan halayen irin na Danmasanin Kano.

 

  • Babban Rashi Ne Ga Afrika — Yakubu Dogara

Kakakin Majalisar Tarayya Yakubu Dogara, ya bayyana mutuwar dattijon Maitama Sule a matsayin babban rashi ga ilahirin nahiyar Afirka.

Mai magana da yawun Dogara, Tukur Hassan ne ya bayyana haka a wata takarda da ya rabawa manema labarai, inda ya ce duk Danmasani ya tsufa kuma yana fama da rashin lafiya, hakika rashin a Njeriya ba karamin tashin hankali ba ne.

Ya ce: “Danmasanin Kano hazikin mutum ne kuma Gwarzo, uba ga kowa kuma dattijo arziki, mai mutunci wanda ya sa sunan sa ya yi fice a idon duniya kan halin dattaku, kuma ya bar tarihi a Nijeriya.”

“Yana cikin mutane da suka yi gwagwarmayar samarwa da kasar nan ‘yancin kai, ya samu nasara a matsayinsa na wakilin al’ummar a Majalisar Tarayya a wancan lokaci. Ya rike mukamin Kwamishin Hukumar Sauraron Korafin Jama’a, amma ba a taba jin sa da mummunan hali ba, hakika akwai bukatar mu yi koyi da halayansa.

 

Mun Yi Rashin Uba Nagari A Siyasa — el-Rufai

Gwamnan Jihar Kaduna, Malan Nasir el-Rufai ya ce Nijeriya ta rasa mai bada nagartattun shawarwari, watau marigayi Maitama Sule.

Nasir el-Rufai ya yi addu’a Allah Ya gafarta wa Maitama Sule da rahamarSa, wanda mutuwarsa ta taba manya da kanana a kasar nan. Ya kara da cewa marigayin ya rike mutuncinsa, domin ya zauna da kowa lafiya.

A cikin sakon nasa, el-Rufai bayyana marigayin a matsayin dattijo wanda yana cikin wadanda suka yi gwagwarmay kwato ‘yancin Nijeriya.

“Lokacin da yake Minista a jamhuriya ta daya kuma matashi a cikin ministoci wanda su taka rawar gani ga rayuwar al’umma a kasar nan. Maitama Sule ya yi wa al’umma aiki wanda tarihi ba zai manta da shi ba.” In ji el-Rufai.

Gwamnan ya kara da cewa ya amfana matuka daga ilimunmukan da Allah ya horewa marigayin da kuma shawarwari da yake ba shi ka sha’anin gudanar da mulkin jama’a.

 

Kullum Burinsa Hadin Kan Nijeriya — Tambuwal

Da yake nasa jimamin, Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana rasuwar Maimata Sule a matsayin abin tausayi ga Nijeriya, domin rashin babban gwarzo irin wannan gibi ta fuskar ci gaban kasa.

Ya kara da cewa marigayi: “Dan Masanin Kano ya hidimtawa kasar nan da kuma al’ummar da ke cikinta har zuwa lokacin da Allah ya dauki ransa. Maitama Sule ya kasan ci mai son al’umma wanda kuma ya sadaukar da rayuwar sa ga hadin kan ‘yan kasa da kuma kasa shen afirka baki daya.

Bisa ga bayanan da ya fitar a makon da ya gabata a wurin taron ta’aziyar marigayin ta hannun jami’in Gwamnan kan sha’anin watsa labarai, Malan Imam Imam ya ce Gwamna Tambuwal bayyana marigayin a matsayin haziki mutun wanda ya sadaukar da rayuwar sa kan bauta wa kasa da kuma ‘yan kasar sa da ma afrika baki daya.

Har ila yau ya ce, “A madadin Gwamnatin Jihar Sakkwato, ina yi wa gwamnatin Kano da al’ummarta jaje da ta’aziyyar rasuwa dan kishin kasa, Alhaji Yusuf Maitama Sule Dan Masanin Kano, muna addu’ar Allah Ya ji kansa da rahama.

 

  • Masari, Kaita Da Danmusa Sun Jajanta Wa Al’ummar Kano

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari, shi ma mika ta’aziyarsa ga iyalan gidan marigayi Maitama Sule, Gwamnatin Jihar Kano da kuma Masarautar Kano bisa rasuwar dattijon arziki.

A cikin jawabinsa, mai magana da yawun Gwamnan Katsina kan yada labarai Abdu Labaran, ya ce Gwamnan ya jajanta kan rasuwar dan kishin Afirka, wanda a kullum burinsa ci gaban Nijeriya.

Ya ce: “Rasuwarsa ta zo lokacin da kasarmu ke neman ire-iren su domin gyara al’amura. Dan Masanin ya bar tarihi a kasar nan da duniya baki daya, hakika ya bada gudunmawa wadda ba za a manta da it aba.

A nasa bangaren, Tsohon Gwamnan Kaduna, Alhaji Lawal Kaita ya shaida wa jaridar LEADERSHIP cewa duk wanda ya san Dan Masani hakika zai bada kyakkyawar shaidar tarihi game da shi, saboda mutun ne haziki kuma gwarzo, wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga ‘yan kasa da kuma ci gababan Afirka baki daya.

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Mamman Danmusa, ya bayyyana Dan Masanin Kano a matsayin mutum mai kishin nahiyar Afirka da kasasar Nijeriya, kamilallen dattijo wanda ya sadaukar da komai nasa wurin hidinmtawa kasarsa. A ko da yaushe a shirye ya ke don taimakawa kasarsa.

 

Gwamna Umahi, Sanata Ogba Sun Jajanta

Gwamnan jihar Ebonyi Cif Dabid Umahi da Sanata mai wakiltar Ebonyi ta tsakiya a majalisar Dattawa sun bayyana rasuwar Dan Masanin Kano a matsayin wata masifa ga kasa.

Yayin da su ke mika gaisuwar ta’aziyar su ga iyalan marigayin, Gwamnatin Jihar Kano, Masarautar Kano da ilahirin al’ummar Nijeriya na rashin wannan gwarzo dan kishin kasa.

Haka zalika Gwamnan ya kara da cewa marigayin ya taka muhimmiyar rawa kan harakokin siyasar kasar nan. Daga nan ya roki Allah da ya yafe wa marigayin kurakuransa.

 

  • Ina Cikin Mutanen Da Yake Fatan Ganin Sun Gaje Shi – Kanal Isa Kachako (RTD)

Da yake yiwa wakilinmu karin haske kan irn abubuwa alhairi na Dan Masanin Kano Kanal Isa Kachako mai murabus ya bayyana cewar Dan Masani ya koyar da shi a makarantar horar da malamai ta Kano, saboda haka ya san kyawawan halayensa, har ma a lokuta da dama bayan ya yi ritaya daga aikin soja ya tsunduma harkokin siyasa, ya zabi ci gaba da bayayana muradunsa a kafafen yada labarai, wanda hakan tasa da kansa Dan Masani ke cewa ko babu shi akwai mutane irinsu Isa Kachoko, za su ci gaba da wayar da kan al’umma.

Kanal Isa Kachako ya yi amfani da damar da ke akwai wajen taya iyalai, ‘yan uwa da abokan arziki jajen rasuwa wannan bawan Allah da bada gudunmawa ga ci gaban Nijeriya.

 

Ba Iyalansa Kadai Suka Yi Rashi Ba — Farfesa Dandatti

Farfesa Dan Datti Abdulkadir ya bayyyanawa cewar wannan rashi ba iyalan Dan Masanin kadai suka yi shi ba, har da al’ummar kasa baki daya. Ya ce abin alfahari ne yadda Dan Masani idan ka cire iyalansa ba abinda ke gaban sa da ya wuce kasa da kishin al’ummarta.

Saboda haka farfesan ya yi addu’ar Allah ya kyautata makwancin maragiya=in ya Ya kuma sanya Aljannah ta zamo makomarsa.

 

Gwani Hassan Musa Minna

Shi ma da yake yiwa jaridar LEADERSHIP Hausa bayani a lokacin jana’izar Dan Masanin Kano, Shugaban Majalisar Mahaddatta Alkur’ani na Kasa, Gwani Hassan Musa Minna ya ce wannan rashi kamar alarammomi kadai aka yiwa, kasancewar Maitama Sule masoyin Alkur’ani ne da ahlinsa. Saboda haka ya gabatar da ta’aziyyar wannan babban rashi da al’umma Kano da kasa baki daya.

Yace Dan Masanin Kano ya tafiyar da mafi yawancin rayuwar sa kan hidimtawa al’umma.

A karshe Gwani Hassan Musa ya bada umarni ga daukacin tsangayun da ke karkashin wannan Majalisa da su gudanar da saukokin alkur’ani domin Allah ya yalwata kabarin Dan Masanin Kano da haske Alkur’ani.

 

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI