Connect with us

RAHOTANNI

Mazan Zamanin Nan Ku Ji Tsoron Allah, Ku Rika Sauke Nauyin Iyalanku —Amira Rakiya

Published

on


  • Imam Kabir Ya Nemi Dabbaka Addini A Dukkan Mu’amala

Daga Abdulrazak Yahuza Jere, Abuja

Kungiyar Jama’atud Da’awa, bangaren mata ta yi kira ga mazan zamanin nan su ji tsoron Allah su rika sauke nauyin iyalansu da addini ya dora musu.

Amirar kungiyar, Hajiya Rakiya Shehu Bamalli ta yi kiran a yayin rufe Tafsirin Alkur’ani maigirma na watan Azumin Ramadan da ya gabata a babban dakin taro na harabar Masallacin Jumma’a na Fu’ad da ke Unguwar Wuse, Zone 3 a Abuja.

Hajiya Rakiya Bamalli ta yi tsokacin cewa akwai matukar ban takaici dangane da yadda maza ke barin matansu da yaransu a cikin wahalhalu wanda hakan ke matukar tagayyara rayuwarsu idan ba a yi sa’a ba abin ya kai ga mutuwa.

“A gaskiya a ‘yan kwanakin nan mun samu tururuwan mata masu matsaloli da yawa. Kar a ce na yi son kai, amma galibin matsalolin da matan suka shiga ciki daga mazajensu ne. Sun tafi har gidan iyayensu suka auro su, hakkinsu ne su basu wurin zama, su ciyar da su da sauran abubuwan da suka wajaba. Amma abin da muke gani a wannan zamanin shi ne da zaran an yi auren, duk nauyin sai ya koma kan matan har da dawainiyar yara. Kuma ba haka Allah ya ce a yi ba. Allah ya umurci mata su zauna ne a gida su kula da yara shi kuma miji ya fita waje ya nemo abubuwan da zai sauke nauyin iyalansa da su. Amma a wannan zamanin abin ya canja, mata da yawa sun kawo mana korafe-korafe game da halin da suke ciki.

“Maza suna barin hakkokin da suka rataya a wuyansu. Abubuwan sun yi yawa. Akwai wata mata da ta zo nan kamar za ta haihu mana. Sai da muka dauke ta zuwa asibiti, bayan ta haihu lafiya mun tambaye ta ina mijinta sai ta ce ai ya ki zuwa ne saboda bashi da kudi. Malamai su rika fadakar da Maza a kan hakkokin iyalansu, wallahi abubuwa suna mana yawa kuma ga yara da yawa”.

Da aka tambaye ta ko mene ne take ganin musabbabin wadannan matsalolin, Amirar ta bayyana cewa “rashin ilimin addini ne, sai dai kuma a wasu lokutan akan samu wadanda suke da ilimin amma kuma ba su kula da iyalansu. Amma tsakani da Allah idan har za mu koma mu yi koyi da Sunnar Annabi (SAW) duk wadannan matsalolin za su kau. Duk rashin bin Sunnah ne ya sa hatta yaranmu suka fada harkar shaye-shayen miyagun kwayoyi a kan tituna, saboda ba mu da lokacin da za mu tarbiyyanatar da su. Namiji ya fita neman kudi ita ma mata ta fita neman kudi. Su kuma matan ya zama masu lalura dole wasu sai sun fita sun nemo domin namijin ya kasa sauke nauyin da ke kansa. Ina kira ga mazajenmu su ji tsoron Allah su rika sauke nauyin da ke wuyansu domin mu samu iyalai masu albarka”.

A zantawarsa da LEADERSHIP Hausa jim kadan da kammala addu’o’in rufe Tafsirin, Babban Malamin da ya gabatar da Tafsirin wanda har ila yau shi ne Limamin Masallacin Jumma’a na Unguwar Wuye da ke Abuja, Imam Muhammad Kabir Othman ya ce Tafsirin na bana ya kunshi wa’azozi da nasihohi daban-daban a kan gyara zamantakewar al’ummar Musulmi.

“Mun tattauna abubuwa da dama dangane da zamantakewar al’ummarmu musamman abin da ya shafi ma’aurata, tarbiyyar yara, zama da makota Musulmi ko wadanda ba Musulmi ba sannan a yau da muka rufe karatun mun yi nasiha a kan ‘yan’uwantaka a Musulunci da ba da sadaka da kuma abin da ya shafi Sallar Idi da bukukuwan sallah”. Ya bayyana.

Malamin ya yi kira ga daukacin Musulmi sun rika yin rayuwa abin koyi a duk wurin da suka tsinci kansu ba sai a wasu kebantattun wuraren ibada ba.

“Musulmi ya yi rayuwa abar koyi tana da amfani gare shi da kuma wadanda ma ba Musulmi ba. Ba mu da bukatar dole sai mun kira wadanda ba Musulmi ba su Musulunta da baki. Matukar za mu rika dabbaka koyarwar Musulunci a aikace da kansu za su zo su Musulunta. Matsalar ita ce mu Musulmi mukan ajiye addini sai in mun zo Masallaci kawai wanda wannan babban kuskure ne, ya kamata mu rika aiki da koyarwar addininmu a cikin mu’amalarmu kuma a duk inda muka tsinci kanmu. A kasuwa ne, a ofis ne a duk inda mutum yake ya san cewa Allah yana ganin sa. Wannan zai sa wadanda ba Musulmin ba su san cewa Musulunci shi ne addinin gaskiya kuma su rungume shi”.

Imam Kabir ya kuma bayyana cewa bisa yadda wa’azozi da nasihohin da aka yi suka ratsa zukatan mahalarta Tafsirin, akwai yakinin cewa za a samu kyakkyawan sakamako.

“Daga irin tambayoyin da ke fitowa daga mahalartan za ka san cewa wa’azin ya ratsa su. Misali, daga wa’azin da muka yi a kan amana da irin tambayoyin da suka biyo baya akwai alamar cewa mutane sun san abin da suke yi kuma a shirye suke su sauya halayyarsu. Haka nan wa’azin da muka yi a kan hakkokin miji da mata, akwai mazajen da suka rika kira na suna godiya saboda canjin da suke gani daga matansu. Ka ga wannan kyakkyawan sakamako ne kuma mun gode wa Allah da hakan, don ba yin kanmu ne ba”.

Har ila yau, Limamin ya hori wadanda suke ayyukan ibada a cikin Ramadan kawai kuma da zaran watan ya fita su daina su ji tsoron Allah su san cewa Allah ake yi wa bauta ba watan Ramadan ba.

Ya kara da cewa “a kowane wata ana bautan Allah ba sai a Ramadan ba kawai. Ka zama Musulmi na kwarai a koyaushe don ba ka san yaushe mutuwa za ta zo ma ba. Masu wannan dabi’a su tuba su san cewa Allah da’iman yana nan ba sai a Ramadan ba kawai”.

Kamar yadda Amirar kungiyar ta yi bayani, ita dai Kungiyar Jama’atud Da’awa an kafa ta ce fiye da shekara 20 da suka gabata.

Duk da cewa kungiyar ta fi gudanar da hidindimu masu tarin yawa a cikin watan Azumin Ramadan, har ila yau tana da abubuwan da take gudanarwa masu yawa musamman ta fuskar taimakon al’umma a sauran watanni.

Amirar kungiyar, Hajiya Rakiya Shehu Bamalli ta yi karin haske, “Bisa taimakon matan da suke zuwa wannan Tafsirin mun aiwatar da ayyuka da dama duk da cewa ana cikin matsin tattalin arziki amma Alhamdulillah kamar ma ba a cikin matsin. An kawo mana gudunmawar kayan abinci, tufafi har ma da zakkah. Mun ziyarci wurare da dama har da Maiduguri da Yobe domin kai kayan agaji”.

An rufe Tafsirin na bana na kungiyar ne a ranar 27 ga watan Ramadan wanda ya yi daidai da 22 ga watan Yunin 2017.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI