Connect with us

BURIN ZUCIYA

Wace Nasiha Za Ki Yi Wa Diyarki Ranar Aurenta?

Published

on


Daga Abban Umma

Bisa nazarin yadda ake samun yawaitar mace-macen aure musamman a gidajen Hausa/Fulani, yana da kyau a rika neman hanyoyin magance su. So tari, idan har hakan ta faru, a kan tankwashe kafa a fara lissafin laifukan juna, alhali tun farkon farawa an manta da bin hanya madaidaiciya, yadda Manzon Rahama (SAW) ya koyar.

A nazarin da aka gudanar, zawarawa masu karancin shekaru sun yawaita a mafi yawan manyan jihohinmu na Arewa a yau. Zawarawa nawa ka sani a unguwarku? Maza nawa ka sani, wadanda suka saki matansu jim kadan bayan aure? Wai shin me aka dauki aure? Mene ne matsayin matarka a gare ka? Me ya sa ake saurin dirka wa mace saki bisa laifin da bai taka-kara ya karya ba?

Wace irin huduba iyaye mata ke yi wa ‘ya’yansu ranar aure? Shin kwalliya na biyan kudin sabulu ga iyaye masu cewa ‘ya’yansu ‘Namiji ba dan goyo ba’?

Wata uwa tagari, wadda ta san halin zamantakewa ta yi wa diyarta hudubar ABUBUWA 12, wadanda duk diyar da ta rike za ta samu alheri a rayuwarta na aure, kamar haka:

1 – Ki zama kamar baiwa ga mijinki, sai shi ma ya zama kamar bawa a gare ki.

2 – Kada ki nisance shi, sai ya manta dake.

3 – Ki kiyaye masa hancinsa, jinsa, da ganinsa; kada ya shaki wani abu daga gare ki sai mai kamshi, kada ya ji wani abu daga bakinki sai mai dadi, kada ya ga wani abu daga gare ki sai mai kyau.

4 – Ki kiyaye masa lokacin abincinsa da lokacin baccinsa, domin yunwa tana hassala mutum, kuma gurbata masa bacci na fusata shi.

5 – Ki kiyaye masa dukiyarsa, danginsa da gidansa, domin suna da matukar muhimmanci a gare shi.

6 – Ki guji yin farin ciki yayin da yake cikin bacin rai, kuma ki kiyayi yin bakin ciki, yayin da yake farin ciki.

7 – Ki girmama shi matuka shi ma zai girmamaki matuka, fiye da yadda kowa zai girmamaki.

8 – Ki sani cewa gwargwadon yadda kike amincewa da ra’ayinsa gwargwadon tausayawar da zai miki.

9 – Kada ki juya masa baya yayin da ya kusanto gare ki.

10 – Ki sani baza ki sami yadda kike so ba, har sai

kin zabi yardarsa a kan yardarki, kin fifita son ransa a kan son ranki.

11 – Kada ki fiya naci ko fushi a lokacin da kike neman wani abu a gare shi, sai ya kosa dake.

12 – Daga karshe don girman, Allah ki yi hakuri, ki zamo shimfida ga mijinki zai zamo rumfa a gare ki….

Ya ku masu karatu musamman iyaye mata, wace hudubar ku ke yi wa ‘ya’yanku ranar aure? Sai na ji daga gare ku.

Daga Abban Umma (B/014/Z/KAD). 08033225331

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI