Connect with us

LABARAI

(Sickbay) Na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya Ya Zama Cikakken Asibiti

Published

on


Daga Idris Umar, Zariya.

A kwanakin baya ne shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Ibrahim Garba ya jagoranci bikin bude sabuwar cibiyar kula da lafiyar dalubai da ma’aikata wanda ke a cikin harabar jami’ar.

A yayin da ya ke jawabi a wajen taron ya ce, “Cibiyar an samar da ita ne a sakamakon bukatar da jami’ar ke da ita na samar da ingantaccen wajen kula da lafiya.” Farfesa ya kara da cewa, “Cibiyar lafiyar ita ta maye gurbin wajen kula da lafiyar jami’ar na da wanda aka fi sani da suna (Sick bay), wanda a baya ba komai da ake bukata ya ke da shi ba, amma yanzun kuwa ya zama sabuwar cibiyar mai dauke da duk wani abu na kula da lafiya da ake bukata a manyan asibitocin da ke fadin kasar nan.”

Har wa yau shugaban jami’ar ya bayyana cewa cibiyar wata dama ce ga sababbin likitocin da aka turo cibiyar kula da lafiyar domin koyon aikin likitanci, don haka sai ya bukaci hukumar kula da cibiyar da su dage wajen ganin an cimma manufar kaukaka wajen.

Ita ma a nata bangaren, daraktar cibiyar kula da lafiyar, Dakta Nana Madugu, ta ce, “A halin yanzu, wannan cibiyar tanada wajen kula da marasa lafiya (Patients’ Wards) dakunan aikin tiyata (Theatre/Operation Room) da kuma cikakkun kayan aiki domin kula da daukacin jami’ar da sauran wurare.”

Daraktar ta kara da cewa cibiyar tana samar da duk wasu manyan harkokin kula da lafiya kuma ta samu shaida daga hukumar NIHS, don haka ne tayi kira ga mazauna kusa da asibitin da su nuna kauna ga asibitin wanda hakan zai sanya shi asibitin ya samu cigaba mai dorewa, kuma tayi kira da bubban murya da cewa duk wanda yake son bayar da wata gudummawa ta kowani sashi to cibiyar a shirye take ta karbi gudummawar, a karshe ne tayi yabo ga shugaban jami’ar Farfesa Ibrahim Garba bisa ga irin gudummawar da yake bayarwa a fannoni daban-daban wanda hakan ke sa lamarin kiwon lafiya ke bunkasa a  jami’ar.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI