Connect with us

DAGA TEBURIN EDITA

Kafin Na Zama Edita…

Published

on


Sulaiman Bala Idris  07036666850

Alhamdu lillah! Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki, wanda ya nufe mu da rayuwa, sannan ya albarkace mu da ni’imar lafiyar kwakwalwa da ta jiki. Allah mun gode da dukkanin ni’imomi a garemu.

A lokacin da na fara rubutu a jarida, ban yi tsammanin cewa alkalamina zai motsa daga bigiren da na dora shi zuwa wani bigiren a gajeren lokaci ba. Duk a tsammanina, na yi rubutu ne a kwabe, cikin salo na rashin kwarewa, yarinta da rashin iyawa.

Bayan rubutun ya fita, an wallafa a jarida, na yi ta samun sakonnin karfafa gwiwa daga al’umma, wadanda ke bayyana min irin shaukin da rubutun nawa ya sanya su. Wanda ya fi min tasiri, shi ne shawarar da mahaifina ya bani. Ya shawarce ni da in mayar da hankali; “Rubutu baiwa ne, wanda kuma ke tattare da natijoji masu tarin yawa”.

A zuciyata na amshi wannan shawara, kuma na gamsu, amma kwakwalwata a daidai wancan lokaci, ba ta amshi sakon cewa rubutu zai iya haifar min da wata natija ba, ni dai kawai na bar wa raina cewa zan ci gaba da yin rubutu.

A haka na ci gaba, duk lokacin da na yi rubutu, sakonnin masu karatu ke kara min kawarin gwiwa, saboda yadda suke nuna min shaukinsu. Har aka zo lokacin da Editan jaridar Leadership Hausa na  wancan lokacin Ashafa Murnai Barkai, ya janyo ni a jiki, ya fara sanya in yi masa rubuce-rubuce, fassara daga turanci zuwa Hausa. Tabbas, tarihin wannan tafiya ba zai cika ba, sai an ambaci sunan Malam Ashafa Murnai.

A sanadiyyar wadannan rubuce-rubuce da fassara a jaridar Leadership Hausa ne, sai shugaban kamfanin ‘Matasa Media Links’, Malam Danjuma Katsina ya kira ni akan na yi aiki da sabuwar mujallarsa mai suna ‘MATASA’. Lokacin da ya fara kirana ta wayar hannu, ya shaida min cewa, ya lalubo ni ne sakamakon rubuce-rubuce da fassarar da nake yi a Leadership Hausa. Daga wannan wayar ne, na shirya na tafi Katsina, inda muka hau kan aiki ba kama hannun yaro. Kwanaki bakwai na yi a garin Katsina, muka shirya komi, tun daga dan ban shafin farko har zuwa na karshe.

Bayan mun gama tsara yadda mujallar Matasa za ta kasance, lokacin da zan tafi Kaduna, wurin da za a buga ta, sai Malam Danjuma ya ce, ni aka ba Editan riko na mujallar. Tabbas wannan lokaci da na dauka ina aiki karkashin Malam Danjuma Katsina, na samu karin haske, kwarewa da sanin makamar aikin jarida. Wani abu da Malam Danjuma yayi min, wanda yana daga cikin abubuwan da suka taimaka min matuka, shi ne yadda ya sakar min mara, ya bani wuka da nama. Idan na tsara abu, ko na shirya wani abin, sai dai ya duba ya yi gyara a wuraren da suke bukatan gyara. Lokacin da hannu ya fada sosai da aikin, sai Malam Danjuma Katsina ya tabbatar da ni a matsayin Editan mujallar, wanda muka kwashe shekara daya da wata daya muna fitowa.

Sanadiyyar Malam Danjuma zai shiga siyasar cibiyar ‘yan jarida ta kasa, reshen jihar Katsina ne muka dakata da aikin mujallar Matasa, saboda a ka’idar cibiyar akwai sharadin cewa dan takara ba zai yiwu ya zama mawallafi ba. Shi kuma Malam Danjuma na neman kujerar mataimakin shugaban ‘NUJ’ reshen jihar Katsina. A dai-dai lokacin da nake Editan mujallar Matasa, na fara karatu a makarantar koyon aikin jarida ‘International Institute of Journalism’. Inda na yi karatun difloma a fannin koyon aikin jarida.

Mujallar Matasa na daina fitowa, sai na sake komawa da rubuce-rubuce da fassara a jaridar Leadership Hausa, a karkashin Malam Ashafa Murnai. Sai dai a wannan karon, ban jima ba, sai Malam Ashafa ya zo min da wata babbar Magana. Ya ce, min yana shirin barin Leadership Hausa, zasu soma wata jaridar hausa shi da tsohon ministan babban birnin tarayya, Dakta Aliyu Modibbo. Sunan jaridar ‘RARIYA’. Malam Ashafa Murnai, ya ce min ya na so mu yi aiki tare da sabuwar jaridar Rariya, a wannan lokacin kuma na fara karatun Difloma a jami’ar Bayero da ke Kano. Ban yiwa Malam Ashafa gardama ba, na aminta akan zan yi aiki da sabuwar jaridarsu ta Rariya; ina cikin mutanen farko da suka fara jaridar Rariya. Na gabatar da wani shafi mai suna ‘Malam Mai Barota’, haka kuma na yi wani shafi na hikaya, wanda Dakta Modibbo ke matukar kauna.

Da tafiya tayi tafiya, bayan Malam Al’amin Ciroma ya zama Editan jaridar Leadership Hausa. A wuraren shekarar 2011, sai na tuntube shi akan ina son komawa shekar da na fito. Ciroma ya grime ni a shekaru, nesa ba kusa ba, a takaice ma dai, ni kanin-kaninsa ne. Amma duk da haka yana ganin girma na matuka. Ko da na ce mishi, ina son dawowa Leadership Hausa, sai ya ce min shi a bangarenshi zai so haka, sai dai bana ganin hakan zai iya haifar da matsala tsakaninsu da Rariya? Sai na ce mishi, ai ina ga babu wata matsala, saboda wannan zabina ne, kuma na yanke hukunci, na gama shawara har can cikin raina.

Ba tare da bata lokaci ba, Malam Ciroma ya aminta da tayin da nayi na komawa Leadership Hausa. Yayi alkawarin gabatar da sunana ga hukumar kamfanin don su bani takardar shaidar aiki. A makon da muka yi wannan zance da shi, nine na rubuta babban labarin jaridar Leadership Hausa, wanda aka yi akan hadarin jirgin saman ‘DANA AIR’.

Babu makawa Malam Ciroma ya sha dawainiya da gwagwarmaya wurin ganin takardar aikina ta fito da jaridar Leadership, duk kuwa da kasantuwar na fara karatun digiri a jami’ar Bayero. Ina makaranta a Kano, daga can nake rubuce-rubuce na, labarai, rahotonnin musamman, da sauransu. Sai a watan Yunin shekarar 2012 ne aka samu takardar aikina ta fito, a matsayin wakilin jaridar Leadership Hausa. Bayan fitowan takardar ne kuma, Malam Ciroma ya kara bani wata dama, inda na fara yin rubutu duk mako, a shafina na ‘Manufar Rayuwa’.

Wata magana da Malam Ciroma yake yawan fada min, ita ce, ‘Da sannu watarana za ka iya zama editan jaridar nan’.  A lokacin dai kawai na kan ji shi ne, amma ba wai ina daukan maganar da girma ba. Ban kuma yi tsammanin cewa ‘wata ranar’ nan kusa take ba.       Tafiya ce me nisa, shi ya sa ma na kirata da ‘Kafin na zama Edita’, na hadu da abubuwa masu yawan gaske a hanya, na yi gane – gane, sannan na dauki darussa masu yawa. Editan day a gaji Malam Ciroma shi ne, Malam Musa Muhammad. Bayan na kammala karatu a jami’ar Bayero, na dawo gida, sai muka shirya akan zan rika bin Edita Malam Musa zuwa Abuja don yin aiki tare dasu a ofis. A haka muka rika zuwa Abuja, lokuta da daman gaske daga aljihunshi ake komi, tun daga kudin mota har zuwa na abinci.

A takaicen takaitawa dai, wannan jaridar ta Leadership A Yau – jaridar hausa ta farko da ta fara fita kullum a tarihin Nijeriya, ni ne Editanta. Na kawo wannan matsayin ne, ba don ina da wayo ba, ba don na fi kowa iyawa ba, ba don na fi kowa kwarewa ba, sai kawai domin nufin Allah, ikonSa da karfin kudurarSa. Dalilin haka ne nake rokon Allah, kamar yadda ya lamunce mana a wuraren da muka gaza, a wuraren da bamu da karfi, Allah ya sa yadda muka gangaro wannan tafiya a sa’a, mu karasa ta cikin nasara.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI