Connect with us

LABARAI

Karamar Hukumar Gumi Na Yunkurin Magance Ambaliyar Ruwa

Published

on


Daga Hussaini Ibrahim, Zamfara

Sabon shugaban Karamar hukumar Gumi a Jihar Zamfara Alhaji Sa’idu Daki-Takwas ya bayyana cewa, Majalisarsa na kokarin magance matsalar ambaliyar ruwa da ke addabar karamar hukumar, ya bayyana haka ne a lokacin ziyara da Kungiyar ‘yan Jarida ta jihar Zamfara keyi a fadin Kananan hukumomi don duba ayyukansu.

Alhaji Sa’idu Daki-Takwas ya bayyana cewa, ‘Majalisarsa ta dukufa wajen ganin an yashe hanyoyin ruwa da kwalbatoci don gudun faruwar ambaliyar ruwa a damunar bana, Haka kuma Majalisar ta dukufa wajen ayyukan more rayuwa musamman bangaren noma daLafiya da Ilimin da dai Sauran su.

Yanzu haka, akwai ayyukan da mukeyi, na hadaka tsakaninmu da gwamnatin jiha, musamman na tituna, inda muka Samar da titi mai tsawon kilomita 24,a fadin Karamar hukumar Gumi.  Haka kuma, Gwamna Abdul’aziz Yari ya gina mana makarantar kurame wadda Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbanjo ya bude kwanakin baya.

Shi ma anasa jawabin Shugaban tawagar‘yanjarida Alhaji Maharaji Sale Altine, ya jinjina wa Shugaban karamar hukumar wajen Samarwa da al’umma kayan more rayuwa.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI