Connect with us

LABARAI

Boko Haram Ta Kone Wani Gari Kurmus A Adamawa

Published

on


Daga Muhammad Shafi’u Saleh, Yola

Shugaban karamar hukumar Madagali Honarabul Muhammad Yusuf, ya tabbatar da cewa kungiyar Boko- haram ta kone garin Yumbuli kurmus dake cikin karamar hukumar ta Madagali a jihar Adamawa. Wannan lamarin ya faru ne a wani harin da kungiyar ta kai garin, inda ta kwashe tsawon awa uku tana aikin kone garin cikin dare, lamarin da ya jefa jama’ar garin cikin mummunar yanayi domin kuwa mafiyawa sun tsere ne da kayan jikinsu kadai.

Rahotannin da suke fito daga yankin sun tabbatar da cewa, ‘yan kungiyar ta Boko- haram sun kone garin kurmus komai a garin ya koma toka,wanda ko dabbobi basu tsira da rai ba a yayin.

Shugaban karamar hukumar ya ci gaba da cewa, abun da ya faru da garin abun bakinciki ne matuka.Yace ganin matakan tsaron dake yankin, bai kamata hakan ta faru ba, ace a kone gari gaba daya.

“Wannan abu da ya faru abun bakinciki da takaici ne da bai kamata ya faru ba, domin duk garin gaba daya ‘yan Boko- haram sun koneshi kurmus. “Sun kone gidagen mutane da abinci da duk dabbobinsu da duk abinda suka mallaka, babu wanda ya fita da komi a cikinsu in banda kayan da yake dashi ajikinsa”.

To sai dai shugaban karamar hukumar Yusuf Muhammad, yace ‘yan Boko- haram din basu kashe kowa a yayin harin ba.Yace, saboda jama’ar garin sun gudu zuwa kan Duwatsu.Wannan dai ba shi ne harin farko


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI