Connect with us

LABARAI

Alhazan Kaduna Uku Suka Rasu A Hajjin Bana

Published

on


Daga Abubakar Abba, Kaduna

Mai lura da Hukumar alhazai reshen Jihar Kaduna Imam Hussaini Sulaiman Tsoho, ya tabbatar da rasuwar mahjjata uku da suka fito daga jihar yayin aikin Hajjin da ya gabata a kasa mai tsarki.

Jami’in ya ce, alhazai biyu sun rasu ne kafi hawan Arfa, yayin da dayan kuwa ya kamu da rashin lafiya a ranar Arf wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwarsa bayan kwana biyu a wata asibitin Makka.

Kazalika ya bayyana cewa, an samu wasu alhazai biyu da suka yi targade aka kai su asibiti bayan sun samu sauki aka sallame su.

A cewarsa, an samu dimbin nasarori a aikin Hajjin na Bana, musamman ganin ba a samu wasu manyan matsaloli da suka auku ba duk da cewar Jihar Kaduna ita ce ta fi yawan alhazai a duk fadin kasar nan a aikin na Bana.

A karshe, jami’in ya ce, kimanin alhazai dari bakwai ne  daga jihar suka sauke faralinsu a Bana, inda adadin ya wuce yawan kujerun da Hukumar Alhazai ta Kasa ta ware wa jihar.


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI