Connect with us

RAHOTANNI

Dan Majalisar Tarayya Ya Raba Kwamfutoci A Sakkwato

Published

on


Daga Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Kebbe/ Tambuwal a Majalisar Wakilai, Honarabul Abdussamad Dasuki, ya raba komfutoci da na’urorin gurza takardu ga makarantun sakandire a Kebbe da Tambuwal domin bunkasa sha’anin ilimi.

A yayin da yake hannunta komfutocin samfurin tafi-da gidanka (Laptop) guda 48 ga wadanda za su amfana a Karamar Hukumar Tambuwal a makon jiya, Dasuki ya bayyana cewa, tallafin gudunmuwa ce domin inganta sha’anin ilimi a mazabarsa.

Dasuki wanda shine Shugaban Kwamitin Sojojin Ruwa a Majalisar Wakilai ya bayyana cewa, samar da komfutocin na da manufar marawa kokarin Gwamnatin Jiha baya kan shirinta na agajin gaggawa a fannin ilimi tare kuma da karfafawa daliban yankin domin su samu ilimin Kimiyar Sadarwar Zamani domin ci-gaban kansu da na al’ummarsu.”Kamar yadda ku ka sani, a watan da ya gabata na bayar da kyautar komfutoci 50 ga daliban wannan mazabar da ke karatu a manyan makarantu da suka hada da Jami’ar Jihar Sakkwato, Kwalejin Kimiya da Fasaha da Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, don haka muna yin abin da ya wajaba domin ganin dalibanmu da ke sakandire sun samu ingantaccen ilimin Fasahar Sadarwar Zamani a yayin da suka kammala karatun sakandire.” Inji shi.

Ya kara da cewa: “Wannan daya ne daga cikin ire-iren gudunmuwar da muke bayarwa domin inganta sha’anin karatu a wannan yankin. Fasahar Sadarwar Zamani a yau ta riga ta mamaye duniya don haka ba za mu bari a bar mu a baya ba.”

Dan Majalisar ya ce wannan gudunmuwar kari ce ga ayyukan raya mazaba da yake yi wadanda suka hada har da samar da rijiyoyin bohol guda 11 a mazabarsa.

Haka kuma Mai Shata Dokokin ya bayyana shirinsa na karfafawa al’ummar yankin domin su tsunduma a sha’anin noman kasuwanci. “A shirye nake domin bayar da tallafin kudi ga matasanmu domin su fara noma domin samun riba. Wannan ya zama wajibi domin noma shine babbar hanyar samun kudin shiga ga al’ummar mu.”

Honarabul Dasuki ya kuma jinjinawa Gwamna Tambuwal kan kokarin da yake yi na kyautatawa al’umma ta yadda a nasa bangaren ya ce zai ci gaba da gudanar da wakilci nagari.

A jawabinsa Shugaban Karamar Hukumar Tambuwal, Honarabul Abubakar Zaki Bashire, ya godewa dan majalisar kan gudunmuwar tare da kira gare shi da ya ci-gaba da rungumar al’ummarsa a ayyukan raya mazaba da ci-gaban al’umma. Haka ma Bashire wanda shine Sakataren Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi ya yi kira ga sauran Masu Shata Dokoki da su yi koyi da irin wakilcin Dasuki.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI