Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Bauchi Za Ta Hukunta Manyan Ma’aikata A Kan Rashin Zuwa Aiki

Published

on


Daga  Khalid Idris Doya, Bauchi

Gwamnatin jihar Bauchi ta bayyana cewar za ta sanya kafar wando daya da dukkanin wani ma’aikacin da baya zuwa wajen aiki kan ka’ida duk da dumbin kokari da gwamnatin ta ke yi wajen biyan su hakkokinsu na albashi. Gwamanatin ta nuna takaicinta a bisa yanda manyan ma’aikatu ke sake neman kashi da aikinsu a ma’aikatun nasu. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban ma’aikata jihar Alhaji Liman Bello a wata ziyarar bazata da ya kai ma’aikatun domin ganin yanayin zuwan ma’aikatan bakin aikinsu.

Shugaban ma’aikatan, ya ziyarci ma’aikatun bayan dawowa hutun sallah inda ya tarar da manyan sakatarori da manyan daraktoci da sauran ma’aikatan gwamnatin sun ki dawo wa bakin aikin nasu, inda nan take ya bada umurnin su gurfana a gabansa domin bayyana dalilinsu na rashin zuwa bakin aiki.

Shugaban ma’aikatan ya ce “yawancin ma’aikatu da na ziyara ma’aikata basu zo bakin aikin nasu ba. kusan zan iya cewa manyan Sakatarori ma su ma da kansu basu fito bakin aiki ba. haka ma Daraktocinsu. “Wannan ba dabi’a ce mai kyau ba”. in ji shi.

Alhaji Liman Bello ya nuna damuwarsa a kan yadda ya yi ta jawo hankulan ma’aikan kan kula da aikinsu, inda ya ce irin wannan ziyarar bazatan shi ne karo na biyu amma bai samu canji daga ma’aikatan ba “Na dauka ma’aikatanmu za su yi aiki da hankali domin a baya can na ziyarci ma’aikatu da dama na dauka hakan zai sanya su shiga taitaiyinsu amma abun takaici ba su zo aiki ba wajen karfe tara har ta wuce  manyan ma’aikata ba su zo ofishinsu ba, akwai ma’aikatar da muka shiga mutum daya muka tarar mai mataki aiki na sha 14, hatta masinjojin ma’aikatun ma babu su zo aikinsu ba, ga kuma ofishoshi a bude da fayel-fayel a kan kujeru amma babu masu kula da su wannan abun takaici ne”. in ji Liman Bello

Shugaban ma’aikatan jihar Bauchi ya bada umurnin kowani sakatare ya kurfana a gabansa a kan wannan laifin “Na bada umurnin manyan sakatarori da daraktocinsu su zo mu tattauna mu kuma fada musu gaskiyar magana da kuma yanda gwamna ta dosa, don ya zama dole mu dauki mataki kan wannan rashin zuwa aikin”. In ji shi

                             


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI