Connect with us

LABARAI

Sama Da Mutum 200 Sun Kamu Da Cutar Kwalara A Borno

Published

on


Daga Muhammad Maitela, Maiduguri

Bayanan da kungiyar (MedicineSanFrontières) dake aiki a sansanonin ’yan gudun hijira a jihar Borno ta bayar, sun tabbatar da cewa, sakamakon bullar annobar kwalara a jihar ya yi sanadin mutuwar mutum bakwai, sannan da karin mutune kimanin 200 wadanda ke dauke da cutar, a cikin birnin Maiduguri.

Shugabar kungiyar likitocin wato, Madam Anna Cillers ce ta bayar da wannan adadin a lokacin da take yiwa manema labarai bayanin a babban birnin jihar, Maiduguri. Inda ta shaidar da cewa zancen da ake ciki yanzu haka (lokacin hada wannan labarin) cibiyar kungiyar likitocin mai kula da masu cutar kwalara dake Dala tana kula da majinyatan da suka kamu da wannan matsala samada 50.

Dukta Cillers ta sake jaddada cewa: “Adadin mutanen da suka harbu da wannan cutar kuma wadanda aka kwantar a cibiyoyin kula da majinyata daban- daban tun farkon faruwar annobar zuwa yanzu sun zarta mutum 200 yayin da aka sallami mutum 100, inda mutane 7 suka rigamu gidan gaskiya”.

Kungiyar ta likitocin agajin kasa da kasa ta bayyana daukar matakan kan-da-garki na bai daya ita da ma’aikatar kiwon lafiya dake jihar Borno hadi da kungiyoyi wajen dakile yaduwar annobar domin takaitah asarar rayuka a birnin na Maiduguri.

Inda kungiyar ta samar da cibiyar kula da cutar mai gadaje 40 a Dala.

Haka zalika kuma, kungiyar likitocin ta ta samar da magungunan ko-ta-kwana a sansanin ’yan gudun hijira na Muna (Oral Rehydration Point ) da kafa Wani kwamitin kwararrun ma’aikatan lafiya na mutum 14 (Community Health Workers) wadanda zasu taimaki kungiyar da bayanai dangane da bullar annobar a ko ta dalilin wadanda suka yi mu’amala da wadanda suka kamu da ita. Musamman yadda bayanai suka bayyana cewa cutar ta fi kamari a sansanin ’yan gudun hijira na Muna Garage.“Muna kokarin shawo kan matsalar ta hanyar baiwa majinyatan ingantattun magungunan cutar kwalarar a cibiyar da muke da ita a Dala mai dauke da gadaje 50, kuma muna kokarin bude karin wata cibiyar kusa da inda jama’a ke dauke da ita. Mun damu matuka dangane da yadda majinyatan suke yawa fiye da tanadinmu”. Ta bakin Anna Cillers. “Saboda haka muna shawartar mutane, idan mutum ya gano cewa yana dauke da alamun wannan cuta ta kwalara to ya nemi hadin gambizar OralRehydrationSolution ko ya garzaya cibiyoyin kula da cutar da gaggawa domin a duba shi. Har wala yau kuma, hanya kwara daya da za a bi wajen takawa wannan matsala birki shi ne doke duk masu ruwa da tsaki a sha’anin kiwon lafiya a nan Maiduguri su hada hannu wuri guda a yaki cutar”. Inji ta.

 


Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

LABARAI